Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Reviling and Reproaching

55 ayoyi · 35 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Suka ce wa juna, “Ga mai mafarkin nan can zuwa!

  2. “Kada ku yi maganar saɓo ga Allah, ko ku la’anta mai mulkin mutanenku.

  3. Ya ce masa, “Kana tsammani ni kare ne da za ka zo mini da sanda?” Sai ya la’anci Dawuda da sunayen allolin Filistiyawa.

  4. Da Dawuda ya koma gida don yă sa wa gidansa albarka, sai Mikal ’yar Shawulu ta fito don tă tarye shi, sai ta ce, “Tabbas sarkin Isra’ila ya fiffita kansa yau, ya tuɓe a gaban bayinsa ’yan mata, kamar yadda duk marar kunya yakan yi!”

  5. Yayinda yake la’antar, Shimeyi ya ce, “Tafi daga nan, tafi daga nan, mai kisankai, mutumin banza kawai!

  6. Ubangiji ya kama ka saboda alhakin jinin gidan Shawulu, wanda kake sarauta a maimakonsa. Ubangiji ya ba da masarautar ga ɗanka Absalom. Hallaka ta zo maka domin kai mai kisankai ne!”

  7. Mai yiwuwa Ubangiji Allahnka ya ji dukan maganganun sarkin yaƙi, wanda maigidansa, sarkin Assuriya, ya aiko don yă rena Allah mai rai. Bari Ubangiji Allahnka yă tsawata masa saboda maganar da ya ji. Saboda haka ka yi addu’a domin raguwar da har yanzu suke a raye.”

  8. Ka kasa kunne, ya Ubangiji, ka ji; ka buɗe idanunka ya Ubangiji ka gani; ka saurari kalmomin da Sennakerib ya aiko don yă yi wa Allah mai rai ba’a.

  9. Ƙasusuwana suna jin jiki da wahala yayinda maƙiyana suna mini ba’a, suna ce mini dukan yini, “Ina Allahnka ɗin?”

  10. Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina? Me ya sa ka damu a cikina? Ka dogara ga Allah, gama zai sāke yabe shi, Mai Cetona da kuma Allahna.

  11. saboda ba’ar waɗanda suke zagi suke kuma ƙina, saboda abokan gābana, waɗanda suka sha alwashi sai sun yi ramuwa.

  12. Ya aika daga sama ya kuwa cece ni, yana tsawata wa waɗanda suke fafarata da zafi; Sela Allah yakan aika da ƙaunarsa da amincinsa.

  13. Gama na jimre da ba’a saboda kai, kunya kuma ta rufe fuskata.

  14. gama himma da nake yi wa gidanka yana ƙunata, kuma zagi na masu zaginka yana fāɗuwa a kaina.

  15. Ba’a ta sa zuciyata ta karai ta bar ni ba mataimaki; Na nemi a ji tausayina, amma ban sami ko ɗaya ba, na nemi masu ta’aziyya, amma ban sami ko ɗaya ba.

  16. Ka tashi, ya Allah, ka kāre muradinka; ka tuna yadda wawaye suka yi maka ba’a dukan yini.

  17. Ka sāka a cinyoyin maƙwabtanmu sau bakwai zage-zagen da suka yi ta yi maka, ya Ubangiji.

  18. Ka tuna, Ubangiji, yadda aka yi wa bawanka ba’a, yadda na jimre a zuciyata da zage-zagen dukan al’ummai,

  19. zage-zagen da abokan gābanka suka yi mini, ya Ubangiji, da suka yi wa kowane matakin da shafaffenka ya ɗauka.

  20. Dukan yini abokan gābana suna tsokanata; waɗanda suke mini ba’a suna amfani da sunana yă zama abin la’ana.

  21. sa’an nan zan amsa wa masu cin mutuncina, gama na dogara ga maganarka.

  22. Duk wanda ya zalunci matalauci ya zagi Mahaliccinsu ke nan, amma duk wanda ya yi alheri ga mabukata yana girmama Allah ne.

  23. Ka kasa kunne, ya Ubangiji, ka kuma ji; ka buɗe idanunka, ya Ubangiji, ka kuma gani; ka saurara ga dukan maganganun da Sennakerib ya aika don yă zagi Allah mai rai.

  24. Wane ne ka zargi ka kuma yi wa saɓo? A kan wa ka tā da muryarka ka kuma daga idanu cikin fariya? A kan Mai Tsarkin nan na Isra’ila!

  25. Ta wurin jakadunka ka jibge zage-zage a kan Ubangiji. Ka kuma ce, ‘Da kekunan yaƙina masu yawa na hau ƙwanƙolin duwatsu, ƙwanƙolin mafi tsayi na Lebanon. Na sassare al’ul mafi tsayi fir mafi kyau. Na kai can wuri mafi nisa na kurminsa.