Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Reviling and Reproaching

55 ayoyi · 35 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. In an zage ku saboda sunan Kiristi, ku masu albarka ne, gama Ruhun ɗaukaka da kuma na Allah yana bisanku.

  2. Wannan gaskiya ce musamman ga waɗanda suke bin sha’awace-sha’awacen lalaci na mutuntaka, suna kuma rena masu mulki. Da ƙarfin hali da kuma girman kai, waɗannan mutane ba sa tsoro kawo zargin ɓata sunan talikan sama;

  3. duk da haka ko mala’iku ma da suka fi su ƙarfi suka kuma fi su iko, ba sa kawo irin wannan zargi na ɓata suna game da waɗannan talikai a gaban Ubangiji.

  4. Haka yake da masu mafarke-mafarken nan, gama sun ƙazantar da jikunansu, suka ƙi bin masu mulki, suna ɓata sunan talikan sararin sama.

  5. Kai, ko Mika’ilu babban shugaban mala’iku ma, sa’ad da yake mūsu da Iblis game da gawar Musa, bai yi garajen ɗora masa laifi da baƙar magana ba, sai dai ya ce, “Ubangiji yă tsawata maka!”