Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Paul

619 ayoyi · 103 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Gama waɗansu suna cewa, “Wasiƙunsa suna da nauyi da kuma ƙarfi, amma kuwa in ka gan shi, ba shi da wani kwarjini, maganarsa kuma ba kome ba ce.”

  2. Mai yiwuwa ni ba horarre ba ne a magana, amma ina da sani. Mun kuwa bayyana muku wannan a sarari, ta kowace hanya.

  3. In su Ibraniyawa ne, ni ma haka. In su Isra’ilawa ne, ni ma haka. In su zuriyar Ibrahim ne, ni ma haka.

  4. In su bayin Kiristi ne, ni na fi su ma, ina magana kamar ruɗaɗɗe ne fa! Ai, na fi su shan fama ƙwarai da gaske, da shan dauri, na sha dūka marar iyaka, na sha hatsarin mutuwa iri-iri.

  5. Sau biyar Yahudawa suka yi mini bulala arba’in ɗaya babu.

  6. Sau uku aka bulale ni da bulalar ƙarfe, sau ɗaya aka jajjefe ni da duwatsu, sau uku jirgin ruwa ya ragargaje ina ciki, na kwana na kuma yini ruwan teku yana tafiya da ni.

  7. Na yi tafiye-tafiye da yawa, na sha hatsari a koguna, na sha hatsarin ’yan fashi, na sha hatsari a hannun kabilarmu, na sha hatsari a hannun al’ummai, na sha hatsari a birane, na sha hatsari a jeji, na sha hatsari a teku, na kuma sha hatsarin ’yan’uwa na ƙarya.

  8. Na yi fama, na shan wuya, ga kuma rashin barci sau da yawa. Na san abin da ake nufin da jin yunwa da ƙishirwa, sau da yawa kuwa na kasance da rashin abinci, na sha sanyi da zaman tsirara.

  9. A Damaskus, gwamnan da yake ƙarƙashin Sarki Aretas, ya sa tsare ƙofofin birnin Damaskus, don yă kama ni.

  10. Amma aka saukar da ni cikin kwando ta tagar katanga, na kuɓuce masa.

  11. Dole in ci gaba da yin taƙama. Ko da yake ba za tă amfane ni ba, zan yi magana a kan ru’uyoyi da wahayoyi waɗanda na karɓa daga Ubangiji.

  12. Na san wani a cikin Kiristi wanda shekaru goma sha huɗu da suka wuce an ɗauke zuwa sama ta uku. Ko a cikin jiki ne, ko kuwa ba a cikin jiki ba, ni dai ban sani ba, Allah ne ya sani.

  13. Na kuma san cewa wannan mutum, ko a cikin jiki ne, ko kuma ba a cikin jiki ba, ni dai ban sani ba, amma Allah ne ya sani,

  14. an ɗauke shi ne zuwa aljanna. Ya ji waɗansu abubuwa waɗanda ba zai iya faɗarsu da kalmomi ba, abubuwan da ba a ba wa mutum damar faɗi.

  15. Don kada in cika da girman kai saboda waɗannan mafifitan manyan wahayoyi, sai aka sa mini wata ƙaya a jikina wadda ta zama ɗan saƙon Shaiɗan, don ta wahalshe ni.

  16. Sau uku na roƙi Ubangiji yă raba ni da wannan abu.

  17. Amma ya ce mini, “Alherina ya ishe ka, domin a cikin rashin ƙarfi ne ake ganin cikar ikona.” Saboda haka, zan ƙara yin taƙama da farin ciki game da rashin ƙarfina, domin ikon Yesu Kiristi yă zauna tare da ni.

  18. Shi ya sa nake murna cikin rashin ƙarfi, da zagi, da shan wahaloli, da tsanantawa, da matsaloli, saboda Kiristi. Don a sa’ad da nake marar ƙarfi a nan ne nake da ƙarfi.

  19. Bulus manzo, aikakke ba daga wurin mutum ba, ba kuma ta wurin mutane ba, amma ta wurin Yesu Kiristi da kuma Allah Uba, wanda ya tā da Yesu daga matattu.

  20. Kun dai ji labarin rayuwata ta dā a cikin Yahudanci, yadda na tsananta wa ikkilisiyar Allah ƙwarai, na kuma yi ƙoƙarin hallaka ta.

  21. Na ci gaba a cikin Yahudanci fiye da yawancin Yahudawan da suke tsarana, na kuma yi ƙwazo ƙwarai ga bin al’adun kakannina.

  22. Amma sa’ad da Allah, wanda ya keɓe ni daga mahaifa ya kira ni ta wurin alherinsa, ya kuma gamshe shi

  23. yă bayyana Ɗansa a cikina, domin in yi wa’azinsa cikin Al’ummai. Ban nemi shawarar wani mutum ba.

  24. Ban kuma tafi Urushalima domin in ga waɗanda suka riga ni zaman manzanni ba, sai dai na hanzarta na tafi ƙasar Arabiya, daga baya sai na koma Damaskus.

  25. Bayan shekara uku, sai na haura zuwa Urushalima domin in sadu da Bitrus, na kuwa zauna tare da shi kwana goma sha biyar.