Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Paul: Persecutes the Christians; present at, and gives consent to, the stoning of Stephen

5 ayoyi · 103 fannoni

Ayoyi game da Persecutes the Christians; present at, and gives consent to, the stoning of Stephen

  1. Suka ja shi zuwa bayan birnin suka kuma yi ta jifansa da duwatsu. Ana cikin haka, shaidun suka ajiye tufafinsu a wurin wani saurayi mai suna Shawulu.

  2. Shawulu kuwa yana can, yana tabbatar da mutuwarsa. A wannan rana wani babban tsanani ya auka wa ikkilisiyar da take a Urushalima, sai duka suka warwatsu ko’ina a Yahudiya da Samariya, manzanni kaɗai ne suka rage.

  3. Amma Shawulu ya fara hallaka ikkilisiya. Yana shiga gida-gida, yana jan maza da mata yana jefa su cikin kurkuku.

  4. Ana cikin haka, Shawulu ya ɗage yana barazana yin kisa da tsananta wa almajiran Ubangiji. Sai ya je wurin babban firist

  5. Na tsananta wa masu bin wannan Hanyar har ga mutuwarsu, ina kama maza da mata ina kuma jefa su cikin kurkuku,