Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Paul: Visits Assos, Mitylene, Chios, Samos, Trogyllium, and Miletus, hastening to Jerusalem, to be there at Pentecost

4 ayoyi · 103 fannoni

Ayoyi game da Visits Assos, Mitylene, Chios, Samos, Trogyllium, and Miletus, hastening to Jerusalem, to be there at Pentecost

  1. Mu kuwa muka ci gaba zuwa jirgin ruwan muka tashi muka nufi Assos inda za mu ɗauki Bulus. Ya yi wannan shirin don zai tafi can da ƙafa.

  2. Da ya same mu a Assos, sai muka ɗauke shi a jirgin ruwan muka zo Mitilen.

  3. Kashegari muka tashi cikin jirgin ruwa daga can muka zo gefen Kiyos. Kwana ɗaya bayan wannan, sai muka ƙetare zuwa Samos, kashegari kuma muka iso Miletus.

  4. Bulus ya yanke shawara yă wuce Afisa a jirgin ruwa don kada yă ɓata lokaci a lardin Asiya, gama yana sauri yă kai Urushalima, in ya yiwu ma, a ranar Fentekos.