Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Paul: Predicts misfortune to the ship; his counsel not heeded, and the voyage resumed

5 ayoyi · 103 fannoni

Ayoyi game da Predicts misfortune to the ship; his counsel not heeded, and the voyage resumed

  1. An riga an ɓata lokaci da yawa, tafiya kuwa ta riga ta zama da hatsari domin a lokacin Azumi ya riga ta wuce. Saboda haka Bulus ya gargaɗe su,

  2. ya ce, “Mutane, ina gani tafiyarmu za tă zama da masifa ta kuma kawo babbar hasara ga jirgin ruwan da kaya, da kuma ga rayukanmu ma.”

  3. Amma jarumin, a maimakon ya saurari abin da Bulus ya ce, sai ya bi shawarar matuƙi da kuma mai jirgin ruwan.

  4. Da yake tashar jirgin ruwan ba tă dace a ci damina a can ba, yawanci suka ba yanke shawara cewa mu ci gaba da tafiya, da bege za mu kai Funis mu ci damina a can. Wannan tashar jirgin ruwa ne a Kirit, tana fuskantar kudu maso yamma da kuma arewa maso yamma.

  5. Da iska ta fara busowa daga kudu a hankali, sai suka yi tsammani sun sami abin da suke nema; saboda haka suka janye ƙugiyar jirgin ruwa suka bi ta gefen tsibirin Kirit.