Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Paul: Called to be an apostle

27 ayoyi · 103 fannoni

Ayoyi game da Called to be an apostle

Tace bisa littafi
  1. “Sa’an nan ya ce, ‘Allah na kakanninmu ya zaɓe ka ka san nufinsa ka kuma ga Mai Adalcin nan ka kuma ji kalmomi daga bakinsa.

  2. Za ka zama mai shaidarsa ga dukan mutane game da abin da ka gani ka kuma ji.

  3. Yanzu me kake jira? Ka tashi, a yi maka baftisma, a wanke zunubanka, ta wurin kira bisa ga sunansa.’

  4. “Sa’ad da na dawo Urushalima ina cikin addu’a a haikali, sai na ga wahayi

  5. na ga Ubangiji yana magana. Ya ce mini, ‘Maza! Ka bar Urushalima, gama ba za su yarda da shaidarka game da ni ba.’

  6. “Na amsa na ce, ‘Ubangiji, waɗannan mutane sun san cewa na bi majami’a-majami’a na jefa waɗanda suka gaskata da kai a cikin kurkuku, in kuma yin musu dūka.

  7. Sa’ad da kuma aka zub da jinin Istifanus mashaidinka, na tsaya can ina ba da goyon bayana ina kuma tsaron tufafin masu kisansa.’

  8. “Sa’an nan Ubangiji ya ce mini, ‘Je ka; zan aike ka can nesa a wurin Al’ummai.’ ”

  9. Yanzu ka tashi, ka tsaya da ƙafafunka. Na bayyana a gare ka don in naɗa ka bawa da kuma mai shaidar abin da ka gani game da ni da kuma abin da zan nuna maka.

  10. Zan tsirar da kai daga mutanenka da kuma daga Al’ummai. Ina aikan ka zuwa gare su domin

  11. ka buɗe idanunsu su kuwa juyo daga duhu zuwa haske, daga mulkin Shaiɗan kuma zuwa wurin Allah, domin su sami gafarar zunubai da kuma matsayi a cikin waɗanda aka tsarkake ta wurin bangaskiya a cikina.’

  12. Bulus, bawan Kiristi Yesu, kirayaye don yă zama manzo, keɓaɓɓe kuma domin bisharar Allah.

  13. Bulus, wanda aka kira domin yă zama manzon Kiristi Yesu, bisa ga nufin Allah, da kuma ɗan’uwanmu Sostenes,

  14. Ba ni da ’yanci ne? Ni ba manzo ba ne? Ni ban gan Yesu Ubangijinmu ba ne? Ba ku ne sakamakon aikina cikin Ubangiji ba?

  15. Ko da waɗansu ba su ɗauke ni a matsayin manzo ba, tabbatacce, ni manzo ne a gare ku! Gama ku ne hatimin manzancina a gaban Ubangiji.

  16. Gama ni ne mafi ƙanƙanta a cikin manzanni, ban kuma isa a kira ni manzo ba, domin na tsananta wa ikkilisiyar Allah.

  17. Bulus manzo, aikakke ba daga wurin mutum ba, ba kuma ta wurin mutane ba, amma ta wurin Yesu Kiristi da kuma Allah Uba, wanda ya tā da Yesu daga matattu.

  18. Amma sa’ad da Allah, wanda ya keɓe ni daga mahaifa ya kira ni ta wurin alherinsa, ya kuma gamshe shi

  19. yă bayyana Ɗansa a cikina, domin in yi wa’azinsa cikin Al’ummai. Ban nemi shawarar wani mutum ba.

  20. Bulus, wanda Allah ya zaɓa don yă zama manzon Kiristi Yesu, Zuwa ga tsarkaka da suke a Afisa, da kuma suke amintattu cikin Kiristi Yesu.

  21. Bulus, wanda Allah ya zaɓa don yă zama manzon Kiristi Yesu, da kuma daga Timoti ɗan’uwanmu,

  22. Bulus, manzon Kiristi Yesu ta wurin umarnin Allah Mai Cetonmu da kuma na Yesu Kiristi begenmu,

  23. Don haka ne aka sa ni mai wa’azi, da manzo kuma, gaskiya nake faɗa, ba ƙarya ba, na kuma zama malami mai koya wa al’ummai al’amarin bangaskiya da kuma na gaskiya.

  24. Bulus, manzon Kiristi Yesu ta wurin nufin Allah, bisa ga alkawarin rai wanda yake cikin Kiristi Yesu,

  25. A wannan bishara ce, aka naɗa ni mai shela da manzo da kuma malami.