Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Paul: Is delayed in Melita three months; proceeds on the voyage; delays at Syracuse; sails by Rhegium and Puteoli; meets brethren who accompany him to Rome from Appii forum; arrives at Rome; is delivered to the captain of the guard; is permitted to dwell by him
Ayoyi game da Is delayed in Melita three months; proceeds on the voyage; delays at Syracuse; sails by Rhegium and Puteoli; meets brethren who accompany him to Rome from Appii forum; arrives at Rome; is delivered to the captain of the guard; is permitted to dwell by him
Bayan wata uku sai muka tashi a wani jirgin ruwan da ya ci damina a tsibirin. Jirgin ruwa kuwa na Alekzandariya ne yana da siffar tagwayen allolin Kasto da Follus.
Muka isa Sirakus a can muka yi kwana uku.
Daga can muka tashi muka isa Regiyum. Kashegari iskar kudu ta taso, kashegari kuma muka kai Futeyoli.
A can muka tarar da waɗansu ’yan’uwa waɗanda suka gayyaci mu mu yi mako ɗaya da su. Da haka dai muka kai Roma.
’Yan’uwan da suke can sun sami labari cewa muna zuwa, sai suka tashi tun daga Kasuwar Affiyus da Masauƙi Uku don su tarye mu. Da ganin mutanen nan sai Bulus ya gode wa Allah ya kuma sami ƙarfafawa.
Da muka isa Roma, sai aka yarda wa Bulus yă zauna shi kaɗai, tare da sojan da zai yi gadinsa.