Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Paul: Persecutions endured by

77 ayoyi · 103 fannoni

Ayoyi game da Persecutions endured by

Tace bisa littafi
  1. Amma Allah ya tashe shi daga matattu, ya ’yantar da shi daga azabar mutuwa, don ba ya yiwuwa mutuwa ta riƙe shi.

  2. Zan nuna masa wahalar da dole zai sha saboda sunana.”

  3. Bayan kwanaki masu yawa, sai Yahudawa suka haɗa baki su kashe shi,

  4. amma Shawulu ya sami labarin shirinsu. Dare da rana suka yi fakonsa a ƙofofin birnin don su kashe shi.

  5. Amma almajiransa suka ɗauke shi da dare suka saukar da shi a cikin kwando ta taga a katanga.

  6. Ya yi magana ya kuma yi muhawwara da Yahudawa masu jin Hellenanci, amma suka yi ƙoƙarin kashe shi.

  7. Da iyayengijin baranyar suka ga hanyar samun kuɗinsu ta toshe, sai suka kama Bulus da Sila suka ja su zuwa cikin kasuwa don su fuskanci hukuma.

  8. Sai suka kawo su a gaban alƙalai suka ce, “Waɗannan Yahudawa ne, suna kuma birkitar mana da gari,

  9. ta wurin koyar da al’adun da ba daidai ba ne mu Romawa mu karɓa ko mu aikata.”

  10. Sai taron suka fāɗa wa Bulus da Sila gaba ɗaya, alƙalan kuwa suka yi umarni a tuɓe su a kuma yi musu dūka.

  11. Bayan an yi musu bulala sosai, sai aka jefa su cikin kurkuku, aka umarci mai gadin kurkukun yă tsare su da kyau.

  12. Da karɓan irin umarnan nan, sai ya sa su can cikin ɗakin kurkuku na ciki-ciki, kuma ya ɗaura ƙafafunsu a turu.

  13. Wajen tsakar dare Bulus da Sila suna addu’a suna rera waƙoƙi ga Allah, sauran ’yan kurkuku kuwa suna sauraronsu.

  14. “Yanzu kuma Ruhu ya tilasta ni, za ni Urushalima, ba tare da sanin abin da zai faru da ni a can ba.

  15. Na dai san cewa a kowace birni Ruhu Mai Tsarki yakan gargaɗe ni cewa kurkuku da shan wuya suna jirana.

  16. Amma ni ban ɗauki raina a bakin kome ba, in dai zan iya gama tserena in kuma kammala aikin da Ubangiji Yesu ya ba ni aikin shaida bisharar alherin Allah.

  17. Sai Bulus ya amsa ya ce, “Don me kuke kuka kuna kuma ɓata mini zuciya? A shirye nake ba ma a daure ni kawai ba, amma har ma in mutu a Urushalima saboda sunan Ubangiji Yesu.”

  18. Da kwana bakwai ɗin suka yi kusan cika, waɗansu Yahudawa daga lardin Asiya suka ga Bulus a haikali. Sai suka zuga taron duka, suka kama shi,

  19. suna ihu suna cewa “Mutanen Isra’ila ku taimake mu! Ga mutumin da yake koya wa dukan mutane ko’ina cewa su ƙi mutanenmu da dokarmu da kuma wannan wuri. Ban da haka ma, ya kawo Hellenawa a cikin filin haikali ya ƙazantar da wurin nan mai tsarki.”

  20. (Dā ma can sun ga Turofimus mutumin Afisa a birni tare da Bulus suka yi tsammani Bulus ya kawo shi filin haikali.)

  21. Duk birnin ya ruɗe, mutane suka zaburo da gudu daga kowane gefe. Suka kama Bulus, suka ja shi daga haikali, nan da nan aka rurrufe ƙofofi.

  22. Yayinda suke ƙoƙari su kashe shi, sai labari ya kai ga shugaban ƙungiyar sojan Roma cewa birnin Urushalima duk ta hargitse.

  23. Nan da nan ya ɗibi waɗansu hafsoshi da sojoji suka gangara a guje wurin taron. Da masu hargitsin suka ga shugaban ƙungiyar sojan da sojojinsa, sai suka daina dūkan Bulus.

  24. Shugaban ƙungiyar sojan ya zo ya kama shi ya ba da umarni a daure shi da sarƙoƙi biyu. Sa’an nan ya yi tambaya ko shi wane ne, da kuma abin da ya yi.

  25. Taron suka saurari Bulus sai da ya yi wannan magana. Sa’an nan suka ɗaga muryoyinsu suka yi ihu suka ce, “A raba duniya da wannan mutum! Bai cancanci yă rayu ba!”