Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Music

324 ayoyi · 57 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sai mutanen suka yi gunaguni a kan Musa, suna cewa, “Me za mu sha?”

  2. Sai Musa ya yi kuka ga Ubangiji, Ubangiji kuwa ya nuna masa wani itace. Sai ya jefa shi cikin ruwan, sai ruwan ya zama mai daɗi. A can Ubangiji ya yi musu doka da farilla, a can kuma ya gwada su.

  3. Ya ce, “In kun kasa kunne ga muryar Ubangiji Allahnku kuka yi abin da yake daidai a idanunsa, in kun mai da hankali ga umarnansa, kuka kiyaye dukan farillansa, ba zan kawo muku wani ciwon da na kawo a kan Masarawa ba, gama ni ne Ubangiji da nake warkar da ku.”

  4. Sai suka zo Elim inda akwai maɓulɓulan ruwa goma sha biyu da itatuwan dabino saba’in, suka sauka a can, kusa da ruwa.

  5. “Ka ƙera kakaki guda biyu na azurfa, ka kuma yi amfani da su don kira taron jama’a wuri ɗaya, don kuma ka riƙa sanar da su lokacin tashi daga sansani.

  6. Sai Isra’ilawa suka rera wannan waƙa, “Ki ɓuɓɓugo da ruwa, Ke rijiya! Rera waƙa game da ita,

  7. game da rijiyar da ’ya’yan sarki suka haƙa, rijiyar da manyan mutane masu sandunan sarauta suka nuna da sandunansu.” Sa’an nan suka tashi daga hamadar, suka tafi Mattana,

  8. daga Mattana, suka tafi Nahaliyel, daga Nahaliyel, suka tafi Bamot,

  9. daga Bamot kuma suka tafi kwarin da yake cikin Mowab inda ƙwanƙolin Fisga yake fuskantar hamada.

  10. Da Yoshuwa ya gama yin wa mutane magana, sai firistoci guda bakwai waɗanda suke riƙe da ƙahoni guda bakwai a gaban Ubangiji suka sha gaba suna busa ƙahoninsu, akwatin alkawari kuwa yana biye da su.

  11. Sa’ad da Yefta ya komo gida a Mizfa, wa ya fito yă tarye shi, ’yarsa tilo, tana rawa kiɗin ganguna! Ita ce kaɗai ’yarsa. Ban da ita ba shi da ɗa ko ’ya.

  12. “Bayan wannan, za ka tafi Gebiya ta Allah, inda sansanin Filistiyawa yake. Kana shiga garin, za ka sadu da jerin gwanon annabawa suna gangarowa daga tudu, ana kaɗa garaya, ana bugan ganguna, ana hura sarewa, ana kuma bugan molo, a gabansu, su kuma za su yi ta annabci.

  13. Ruhun Ubangiji zai sauko a kanka da iko, za ka kuma yi annabci tare da su. Za a canja ka ka zama dabam.

  14. To, fa, Ruhun Ubangiji ya riga ya rabu da Shawulu, sai mugun ruhu daga Ubangiji ya soma ba shi wahala.

  15. Ma’aikatan Shawulu suka ce masa, “Duba, ga mugun ruhu daga Allah yana ba ka wahala.

  16. Ranka yă daɗe, muna so ka ba mu izini mu tafi, mu nemo wanda ya iya kiɗan molo, domin duk sa’ad da mugun ruhun nan daga Allah ya tashi, sai yă kaɗa molon don hankalinka yă kwanta.”

  17. Saboda haka Shawulu ya ce wa ma’aikatansa, “Ku nemo wanda ya iya kiɗan molo sosai ku kawo mini.”

  18. Duk lokacin da ruhun nan daga Allah ya sauko a kan Shawulu, sai Dawuda yă ɗauki molonsa yă kaɗa. Sa’an nan sauƙi yă zo wa Shawulu, mugun ruhu kuma yă rabu da shi.

  19. Yayinda mutane suke dawowa gida bayan da Dawuda ya kashe Bafilistin, mata suka fito daga dukan biranen Isra’ila don su sadu da Sarki Shawulu, suna waƙoƙi da raye-raye masu farin ciki, da ganguna da sarewa.

  20. Suna rawa suna cewa, “Shawulu ya kashe dubbansa, Dawuda kuwa ya kashe dubun dubbai.”

  21. da akwatin alkawarin Allah yake ciki. Ahiyo kuwa yana tafiya a gaban Abinadab.

  22. Dawuda da dukan gidan Isra’ila suka yi biki sosai da dukan ƙarfinsu a gaban Ubangiji, da waƙoƙi, da molaye, da garayu, da ganguna, da kacau-kacau da kuma kuge.

  23. yayinda shi da dukan gidan Isra’ila suka hauro da akwatin alkawarin Ubangiji da sowa da kuma busar ƙahoni.

  24. Yanzu ina da shekara tamanin. Zan iya bambanta abu mai daɗi da marar daɗi kuma ne? Bawanka zai iya jin ɗanɗano abin da yake ci, ko yake sha ne? Har yanzu zan iya jin muryoyin mawaƙan maza da mata? Don me bawanka zai zama ƙari kaya ga ranka yă daɗe?

  25. Dukan mutane kuwa suka haura suka bi shi, suna busan sarewa, suna farin ciki sosai, har ƙasa ta girgiza saboda sowa.