Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Music

324 ayoyi · 57 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Jakadu za su zo daga Masar; Kush za tă miƙa kanta ga Allah.

  2. Ku rera wa Allah, ya masarautan duniya, ku rera yabo ga Ubangiji, Sela

  3. gare shi wanda yake hawan daɗaɗɗen sararin sama, wanda yake tsawa da babbar murya.

  4. Ku yi shelar ikon Allah, wanda ɗaukakarsa take a bisa Isra’ila, wanda ikonsa yake a cikin sarari.

  5. Kai mai banmamaki ne, ya Allah, cikin wurinka mai tsarki; Allah na Isra’ila yakan ba da iko da kuma ƙarfi ga mutanensa. Yabo ya tabbata ga Allah!

  6. Zan yabe ka da garaya saboda amincinka, ya Allah; zan rera yabo gare ka da molo, Ya Mai Tsarki na Isra’ila.

  7. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit. Ta Asaf. Ku rera don farin ciki ga Allah ƙarfinmu; ku yi sowa ga Allah na Yaƙub!

  8. Ku fara kaɗe-kaɗe, ku buga ganga, ku kaɗa garaya da molo masu daɗi.

  9. Ku busa ƙahon rago a Sabon Wata, da kuma sa’ad da wata ya kai tsakiya, a ranar Bikinmu;

  10. Yayinda suke kaɗe-kaɗe za su rera, “Dukan maɓulɓulaina suna cikinki.”

  11. Zabura ce. Waƙa ce. Domin ranar Asabbaci. Yana da kyau a yabi Ubangiji a kuma yi kiɗi ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka,

  12. don a yi shelar ƙaunarka da safe amincinka kuma da dare,

  13. da kiɗin molo mai tsirkiya goma da kuma ƙarar garaya.

  14. Ku zo, bari mu rera don farin ciki ga Ubangiji; bari mu yi sowa da ƙarfi ga Dutsen cetonmu.

  15. Bari mu zo gabansa da godiya mu rera gare shi da kiɗi da waƙa.

  16. Zabura ce. Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji, gama ya yi abubuwa masu banmamaki; hannunsa na dama da hannunsa mai tsarki sun yi masa aikin ceto.

  17. Ubangiji ya sanar da cetonsa ya kuma bayyana adalcinsa ga al’ummai.

  18. Ya tuna da ƙaunarsa da kuma amincinsa ga gidan Isra’ila; dukan iyakar duniya sun ga ceton Allahnmu.

  19. Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya, ku ɓarke da waƙa ta murna tare da kiɗi;

  20. ku yi kiɗi ga Ubangiji da garaya, da garaya da ƙarar rerawa,

  21. tare da bushe-bushe da karar ƙahon rago, ku yi sowa don farin ciki a gaban Ubangiji, Sarki.

  22. Bari teku su yi ruri, da kuma kome da yake cikinsa, duniya da kuma kome da yake cikinta.

  23. Bari koguna su tafa hannuwansu, bari duwatsu su rera tare don farin ciki;

  24. Zan rera ga Ubangiji dukan raina; zan rera yabo ga Allahna muddin ina raye.

  25. Ku rera gare shi, ku rera yabo gare shi; ku faɗa dukan abubuwan mamakin da ya aikata.