Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Music

324 ayoyi · 57 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. An yi ƙasa da dukan alfarmarka zuwa kabari, tare da surutan garayunka; tsutsotsi sun bazu a ƙarƙashinka tsutsotsi kuma suka rufe ka.

  2. An ɗauke farin ciki da murna daga gonakin itatuwa masu ’ya’ya; babu wanda yake rerawa ko yake sowa a cikin gonakin inabi; babu wanda yake matsin ruwan inabi a wuraren matsi, gama na kawo ƙarshen yin sowa.

  3. “Ɗauki garaya, ki ratsa birni, Ya ke karuwar da aka manta da ita; kaɗa garaya da kyau, ki rera waƙoƙi masu yawa, saboda a tuna da ke.”

  4. Kaɗe-kaɗen garayu sun yi shiru, surutun masu murna ya daina, garayan farin ciki ya yi shiru.

  5. Babu sauran shan ruwan inabi suna rera waƙa; barasa ya zama da ɗaci ga masu shanta.

  6. Za ku kuma rera kamar a daren da kuke shagalin biki mai tsarki; zukatanku za su yi farin ciki kamar sa’ad da mutane sukan haura da busa zuwa dutsen Ubangiji, zuwa Dutse na Isra’ila.

  7. Kowane bugun da Ubangiji zai yi musu da bulalarsa na hukunci zai zama kiɗi ga ganguna da garaya, yayinda yake yaƙi da su da naushin hannunsa.

  8. Zan sāke gina ki za ki kuwa sāke ginuwa, ya Budurwar Isra’ila. Za ki kuma ɗauki ganganki ki fita don ki yi rawa da masu farin ciki.

  9. “Saboda haka zuciyata na makoki don Mowab kamar busa; tana makoki kamar busa saboda mutanen Kir Hareset. Arzikin da suka samu ta ƙare.

  10. Zan kawo ƙarshen waƙoƙinki masu surutu, ba kuwa za a ƙara jin kaɗe-kaɗen garayunki ba.

  11. Ka kasance a Eden, a lambun Allah; aka yi maka ado da kowane dutse mai daraja, yakutu, tofaz, da zumurrudu, kirisolit, onis da yasfa, saffaya, turkuwoyis da beril. Tsare-tsare da shirye-shiryenka an yi su da zinariya ne; a ranar da aka halicce ka an shirya su.

  12. Tabbatacce, gare su ba ka fi mai waƙar ƙauna da murya mai daɗi kana kuma yin kiɗa sosai ba, gama sukan ji maganarka amma ba sa amfani da ita.

  13. Waje da ƙofar ciki, a cikin filin ciki, akwai ɗakuna biyu, ɗaya a gefen ƙofar arewa yana kuma fuskantar kudu, wani kuma a gefen ƙofar kudu yana fuskantar arewa.

  14. Sai mai shela ya daga murya da ƙarfi ya ce, “Wannan shi ne abin da aka umarce ku ku yi, ya ku mutane da al’umma da kowane yare.

  15. Da zarar kuka ji karar ƙaho, da sarewa, da garaya da goge da molo da algaita da kowane irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe ku rusuna ku yi sujada ga wannan gunkin da sarki Nebukadnezzar ya kafa.

  16. Duk wanda bai rusuna ya yi sujada ba, nan take za a jefa shi a cikin tendarun wuta.”

  17. Saboda haka, da zarar suka ji karar ƙaho, da sarewa, garaya da goge da kowane irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe da kowane irin kaɗe-kaɗe kowane mutum da ko wace al’umma da kowane irin yare suka sunkuya suka yi sujada ga wannan siffa ta zinariya da sarki Nebukadnezzar ya kafa.

  18. Ya sarki, ka fitar da doka, cewa duk wanda ya ji karar ƙaho, da sarewa, da garayu da goge, da molo da algaita da kowane irin kayan kaɗe-kaɗe da bushe-bushe sai yă rusuna yă yi sujada ga siffar zinariya,

  19. kuma cewa duk wanda bai rusuna ya yi sujadar ba za a jefa shi cikin tanderun wuta.

  20. Amma sai ga waɗansu Yahudawa waɗanda ka ɗora su a kan harkokin yankin Babilon, wato, Shadrak, Meshak da Abednego waɗanda ba su kula da umarninka ba, ya sarki. Ba su bauta wa allolin ba balle su yi sujada ga gunkin zinariya da ka kafa.”

  21. Cikin fushi da hasala, Nebukadnezzar ya aika a kira Shadrak, Meshak da Abednego. Aka kawo waɗannan mutane a gaban sarki,

  22. sai Nebukadnezzar ya ce musu, “Gaskiya ne Shadrak, Meshak da Abednego, cewa kun ƙi ku bauta wa alloli kuka kuma ƙi yi sujada ga gunkin da na kafa?

  23. Yanzu sa’ad da kuka ji karar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo da algaita da kowane irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, in kuna a shirye ku rusuna ƙasa ku yi wa wannan gunkin da na yi sujada, to, da kyau. Amma in ba ku yi sujada ba, za a je fa ku yanzu a cikin tanderun wutar nan. In ga kowane ne allahn nan da zai kuɓutar da ku daga hannuna?”

  24. Sai Shadrak, Meshak da Abednego suka amsa wa sarki suka ce, “Ya Nebukadnezzar, ba mu bukata mu kāre kanmu a gabanka a kan wannan batu.

  25. Sa’an nan sarki ya koma fadarsa ya kwana bai ci ba, kuma babu wata liyafar da aka kawo masa. Ya kuma kāsa barci.