Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Journey of Israel Through The Desert

759 ayoyi · 177 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sai Musa da Haruna suka tashi daga taron, suka tafi ƙofar Tentin Sujada, suka fāɗi rubda ciki, sai ɗaukakar Ubangiji ta bayyana musu.

  2. Ubangiji ya ce wa Musa,

  3. “Ka ɗauki sandanka, kai da Haruna, ɗan’uwanka, ku tara jama’a, ku yi magana da dutsen a gabansu ya ba da ruwan da yake cikinsa. Za ka sa ruwa ya ɓuɓɓugo musu daga dutsen. Ta haka za ka ba taron jama’a da garkunansu ruwan sha.”

  4. Sai Musa ya je ya ɗauki sandan kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

  5. Shi da Haruna, suka tara jama’a a gaban dutsen, Musa ya ce musu, “Ku saurara, ku ’yan tawaye, dole mu kawo muku ruwa daga wannan dutse?”

  6. Sai Musa ya ɗaga hannu, ya bugi dutsen sau biyu da sandansa. Ruwa kuwa ya yi ta kwararowa, jama’a da dabbobinsu suka sha.

  7. Musa ya aiki manzanni daga Kadesh zuwa wurin sarkin Edom cewa, “Ga abin da ɗan’uwanka Isra’ila ya ce ka san duk irin wahalolin da ya same mu.

  8. Kakanninmu sun gangaro zuwa Masar, muka zauna can shekaru da yawa. Masarawa suka wulaƙanta mu, da kuma kakanninmu,

  9. amma da muka yi kuka a gaban Ubangiji, ya kuwa ji mu, sai ya aiko mala’ika, ya fitar da mu daga Masar. “Yanzu ga mu a Kadesh, garin da yake kan iyakar yankinka.

  10. Muna roƙonka, ka yarda mana mu bi ta ƙasarka. Ba za mu bi ta wani fili, ko gonar inabi ba, ko mu sha ruwa daga wata rijiya ba. Za mu bi ta babban hanyar sarki, ba kuwa za mu kauce dama, ko hagu ba, har mu wuce yankinka.”

  11. Amma Edom ya amsa ya ce, “Ba za ku bi ta nan ba; in kuka kuskura, za mu fito, mu yaƙe ku da takobi.”

  12. Sai Isra’ilawa suka amsa, suka ce, “Za mu bi ta babbar hanya, in mu, ko dabbobinmu suka sha ruwanku, za mu biya. Mu dai muna so mu wuce ne kawai.”

  13. Sai mutanen Edom suka sāke amsa suka ce, “Ba za ku bi nan ba dai.” Sai Edom ya fito da runduna mai ƙarfi da yawa gaske a kan Isra’ila.

  14. Da yake Edom suka ƙi su bar su su ratsa yankinsu, sai Isra’ila suka juya suka janye daga gare su.

  15. Sa’ad da sarkin Arad, mutumin Kan’ana, wanda yake zaune a Negeb, da ya ji cewa Isra’ila yana zuwa ta hanyar Atarim, sai ya fito, yă yaƙi Isra’ilawa, yă kuma kama waɗansunsu.

  16. Sai Isra’ila suka yi alkawari wa Ubangiji suka ce, “In ka ba da waɗannan mutane a hannunmu, za mu hallaka dukan garuruwansu ƙaf.”

  17. Ubangiji kuwa ya saurari kukan Isra’ila, ya kuma ba da Kan’aniyawa a gare su. Suka hallaka su da biranensu ƙaf; saboda haka aka sa wa wurin suna Horma.

  18. Mutanen suka zo wurin Musa, suka ce, “Mun yi zunubi, da muka yi wa Ubangiji da kai gunaguni. Ka yi addu’a don Ubangiji yă ɗauke mana macizan nan.” Saboda haka Musa ya yi addu’a domin mutane.

  19. Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ƙera siffar maciji ka rataye shi a bisa doguwar sanda; kowa da maciji ya sare shi, idan ya dubi macijin nan da ka rataye, zai rayu.”

  20. Saboda haka Musa ya ƙera macijin tagulla, ya kuma rataye shi bisa doguwar sanda. Sa’an nan duk wanda maciji ya sare shi, ya kuma dubi macijin tagullar, zai warke.

  21. Suka tashi daga nan, suka sauka kusa da Arnon wanda yake a hamadar da ta miƙe zuwa iyakar Amoriyawa. Arnon shi ne iyakar Mowab, wanda yake tsakanin Mowab da Amoriyawa.

  22. Shi ya sa Littafin Yaƙoƙin Ubangiji ya ce, “Waheb ta cikin yankin Sufa, da kwaruruka na tuddan Arnon,

  23. da gangaren kwaruruka, wanda ya nausa zuwa garin Ar, ya kuma dangana da kan iyakar Mowab.”

  24. Isra’ila suka aiki manzanni wurin Sihon sarkin Amoriyawa su ce,

  25. “Ka bari mu ratsa ta ƙasarka. Ba za mu shiga wata gona ba, ba za mu kuma shiga gonar inabi, ko mu sha ruwa daga wata rijiya ba. Za mu bi ta babbar hanyar sarki, har mu fita ƙasarka.”