Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Journey of Israel Through The Desert

759 ayoyi · 177 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sai Musa da Haruna suka je gaban Tentin Sujada,

  2. Ubangiji kuma ya ce wa Musa,

  3. “Ku nisanci wannan taro, gama yanzu nan zan hallaka su.” Sai Musa da Haruna suka fāɗi rubda ciki.

  4. Sai Musa ya ce wa Haruna, “Ka ɗauki farantinka ka sa turare a ciki, da wuta daga bagade, ka yi maza ka tafi wajen taron, ka yi kafara dominsu. Gama fushin Ubangiji ya riga ya sauko; an kuma fara annoba.”

  5. Saboda haka Haruna ya yi kamar yadda Musa ya faɗa, ya ruga a guje zuwa tsakiyar taron. An riga an fara annobar a cikin mutane, amma Haruna ya miƙa turaren ya kuma yi kafara dominsu.

  6. Ya tsaya tsakanin matattu da masu rai, annobar kuwa ta tsaya.

  7. Amma mutane 14,700 ne suka mutu a annobar, ban da waɗanda suka mutu a sanadin Kora.

  8. Sai Haruna ya komo wurin Musa a ƙofar Tentin Sujada, gama annobar ta ƙare.

  9. Ubangiji ya ce wa Musa,

  10. “Ka yi magana da Isra’ilawa, ka kuma karɓi sanduna goma sha biyu daga wurinsu, sanda guda daga kowane shugaban gidan kakanninsu. Ka rubuta sunan kowa a sandansa.

  11. A kan sandan Lawi kuwa ka rubuta sunan Haruna, gama dole a sami sanda ɗaya saboda shugaban gidan kakanninsu.

  12. Ka ajiye su a Tentin Sujada, a gaba akwatin Alkawari, inda zan sadu da kai.

  13. Sandan mutumin da na zaɓa zai yi toho, da haka zan raba kaina da gunagunin da Isra’ilawa suke yi.”

  14. Saboda haka Musa ya yi magana da Isra’ilawa, sai shugabanninsu suka ba shi sanduna goma sha biyu, sanda ɗaya don shugaba, bisa ga gidajen kakanninsu, sandan Haruna kuma yana a cikinsu.

  15. Sai Musa ya ajiye sandunan a gaban Ubangiji a cikin Tentin Sujada.

  16. Kashegari da Musa ya shiga cikin Tentin Sujada sai ga sandan Haruna na gidan Lawiyawa ya yi toho, ya yi furanni, ya kuma yi ’ya’yan almon.

  17. Sai Musa ya fitar wa dukan Isra’ilawa dukan sandunan da suke daga gaban Ubangiji. Suka duba, kowa kuma ya ɗauki sandansa.

  18. Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka mayar da sandan Haruna a akwatin Alkawari, don a ajiye shi alama ga masu tawaye. Wannan zai kawo ƙarshen gunaguninsu a kaina, domin kada su mutu.”

  19. Musa kuwa ya aikata kamar dai yadda Ubangiji ya umarce shi.

  20. Sai Isra’ilawa suka ce wa Musa, “To, ai in haka ne, mun ƙare ke nan!

  21. Idan an ce duk wanda ya zo kusa da tabanakul na Ubangiji zai mutu, ai rayuwarmu kamar mun mutu ke nan.”

  22. Sai aka rasa ruwa da jama’a za su sha, mutane suka taru, suka tayar wa Musa da Haruna.

  23. Suka yi gunaguni wa Musa suka ce, “Da ma mun mutu sa’ad da ’yan’uwanmu suka mutu a gaban Ubangiji!

  24. Don me ka kawo jama’ar Ubangiji a wannan hamada, don mu da dabbobinmu mu mutu a nan ke nan?

  25. Don me ka fitar da mu daga Masar zuwa wannan banzan wuri, inda babu hatsi ko ɓaure, inabi ko rumman. Kuma babu ruwan da za a sha?”