Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Answers To Prayer

195 ayoyi · 85 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. In ka komo ga Maɗaukaki, za ka warke. In ka kawar da mugunta daga cikin gidanka.

  2. Za ka yi addu’a zuwa gare shi, zai kuwa ji ka, kuma za ka cika alkawuranka.

  3. Gama wane bege marar tsoron Allah yake da shi, lokacin da aka datse shi, lokacin da Allah ya ɗauke ransa?

  4. Ko Allah yana sauraron kukansa lokacin da ƙunci ya auko masa?

  5. Ba ya amsawa lokacin da mutane suka yi kira don taimako domin girman kan mugaye.

  6. Lalle Allah ba ya sauraron roƙonsu na wofi; Maɗaukaki ba ya kula da roƙonsu.

  7. Bayan Ayuba ya yi wa abokansa addu’a, Ubangiji ya sa shi ya sāke zama mai arziki ya ninka abin da yake da shi a dā sau biyu.

  8. Gama shi da yakan ɗauki fansa a kan mai kisa yakan tuna; ba ya ƙyale kukan masu wahala.

  9. Cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji; Na yi kuka ga Allahna don taimako. A Haikalinsa ya ji muryata, Kukana na neman taimako ya kai kunnensa.

  10. Ka sa abokan gābana suka juya suka gudu, na kuma hallaka abokan gābana.

  11. Sun nemi taimako, amma ba su sami wanda zai cece su ba, ga Ubangiji, amma bai amsa ba.

  12. Na nemi Ubangiji, ya kuwa amsa mini; ya cece ni daga dukan tsoro.

  13. Idanun Ubangiji suna a kan masu adalci kuma kunnuwansa suna sauraran kukansu;

  14. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Zabura ce. Na jira da haƙuri ga Ubangiji; ya juya wurina ya kuma ji kukata.

  15. ku kira gare ni a ranar wahala; zan cece ku, za ku kuwa girmama ni.”

  16. Da a ce na ji daɗin zunubi a zuciyata, da Ubangiji ba zai saurara ba;

  17. Yabo ga Allah, wanda bai ƙi addu’ata ba ko yă janye ƙaunarsa daga gare ni!

  18. Ubangiji ya ce, “Domin ya ƙaunace ni, zan kuɓutar da shi; zan kiyaye shi, gama ya yarda da sunana.

  19. Zai kira bisa sunana, zan kuma amsa masa; zan kasance tare da shi a lokacin wahala, zan kuɓutar da shi in kuma girmama shi.

  20. Musa da Haruna suna cikin firistocinsa, Sama’ila yana cikin waɗanda suka kira bisa sunansa; sun kira ga Ubangiji ya kuwa amsa musu.

  21. Amma ya lura da wahalarsu sa’ad da ya ji kukansu;

  22. Ina ƙaunar Ubangiji, gama ya ji muryata; ya ji kukata ta neman jinƙai.

  23. Domin ya juye kunnensa gare ni, zan kira gare shi muddin ina da rai.

  24. Zan yi hadayar godiya gare ka in kuma kira bisa sunan Ubangiji.

  25. Cikin azabata na yi kuka ga Ubangiji, ya kuwa amsa ta wurin ’yantar da ni.