Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Answers To Prayer

195 ayoyi · 85 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. ya ce, ‘Korneliyus, Allah ya ji addu’arka, ya kuma tuna da kyautanka ga matalauta.

  2. Saboda haka aka tsare Bitrus a kurkuku, amma ikkilisiya ta nace da addu’a ga Allah dominsa.

  3. Ba zato ba tsammani sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana haske kuma ya haskaka a ɗakin. Ya bugi Bitrus a gefe ya kuma tashe shi ya ce, “Maza, ka tashi!” Sarƙoƙin kuwa suka zube daga hannuwansa.

  4. Wajen tsakar dare Bulus da Sila suna addu’a suna rera waƙoƙi ga Allah, sauran ’yan kurkuku kuwa suna sauraronsu.

  5. Ba zato ba tsammani sai aka yi wata babbar girgizar ƙasa har tushen ginin kurkukun ya jijjiga. Nan da nan sai duk ƙofofin kurkukun suka bubbuɗe, sarƙoƙin kowa kuma suka ɓaɓɓalle.

  6. Mahaifinsa kuwa yana kwanciya a gado yana fama da zazzaɓi da atuni. Bulus ya shiga ciki don yă gan shi, bayan ya yi masa addu’a, sai ya ɗibiya masa hannuwa ya warkar da shi.

  7. Sau uku na roƙi Ubangiji yă raba ni da wannan abu.

  8. Amma ya ce mini, “Alherina ya ishe ka, domin a cikin rashin ƙarfi ne ake ganin cikar ikona.” Saboda haka, zan ƙara yin taƙama da farin ciki game da rashin ƙarfina, domin ikon Yesu Kiristi yă zauna tare da ni.

  9. Bari ɗaukaka ta tabbata a gare shi shi wanda yake da ikon yin aiki a cikinmu, yana kuma aikata abubuwa fiye da dukan abin da muke roƙo, ko muke tunani.

  10. A lokacin da Yesu ya yi rayuwa a duniya, ya yi addu’o’i da roƙe-roƙe tare da kuka mai zafi da kuma hawaye ga wannan wanda yake da ikon cetonsa daga mutuwa, aka kuwa ji shi saboda tsananin bangirman da ya yi.

  11. Amma sa’ad da ya roƙa, dole yă gaskata, ba tare da shakka ba, domin shi mai shakka, yana kama da raƙumar ruwan tekun da iska take kori tana kuma ɓuɓɓugowa.

  12. Kada irin wannan mutum yă yi tsammani zai sami wani abu daga Ubangiji;

  13. Sa’ad da kuka roƙa, ba kwa samu, don kun roƙa da mugun nufi, don ku kashe abin da kuka samu a kan sha’awace-sha’awacenku.

  14. Addu’ar da aka yi cikin bangaskiya, za tă warkar da marar lafiya, Ubangiji zai tashe shi. In ya yi zunubi kuwa za a gafarta masa.

  15. Saboda haka, ku furta wa juna zunubanku, ku yi addu’a saboda juna, domin ku sami warkarwa. Addu’ar mai adalci tana da iko da kuma amfani.

  16. Iliya mutum ne kamar mu. Ya yi addu’a da gaske don kada a yi ruwan sama, ba a kuma yi ruwan sama a ƙasar ba har shekaru uku da rabi.

  17. Ya sāke yin addu’a, sai sammai suka ba da ruwan sama, ƙasa kuma ta ba da amfaninta.

  18. Muna kuma samun dukan abin da muka roƙa daga gare shi, domin muna biyayya da umarnansa, muna kuma yin abin da ya gamshe shi.

  19. Wannan shi ne ƙarfin halin da muke da shi sa’ad da muke zuwa a gaban Allah, gama mun san cewa kome muka roƙa bisa ga nufinsa, yakan saurare mu.

  20. In kuwa muka san cewa yana sauraranmu, ko mene ne muka roƙa, mun sani, mun riga mun sami abin da muka roƙa daga gare shi ke nan.