Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Answers To Prayer

195 ayoyi · 85 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Za ku neme ni ku kuwa same ni sa’ad da kuka neme ni da dukan zuciyarku.

  2. ‘Kira gare ni zan kuwa amsa maka in kuma faɗa maka manyan abubuwan da ba a iya kaiwa, da ba ka sani ba.’

  3. Na yi kira ga sunanka, ya Ubangiji, daga rami mai zurfi.

  4. Ka ji roƙona, “Kada ka toshe kunnuwanka ka ƙi jin roƙona na neman taimako.”

  5. Ya ce mini, “Ɗan mutum, ka ga wannan? Za ka ga abubuwan da suke masu banƙyama fiye da wannan.”

  6. Sa’an nan ya kawo ni cikin fili na cikin gidan Ubangiji, a can kuwa a ƙofar haikali, tsakanin shirayi da bagade, akwai kamar mutum ashirin da biyar. Suka ba haikalin Ubangiji baya suna fuskanta wajen gabas, suna rusuna wa rana a gabas.

  7. Ya ce mini, “Ka ga wannan, ɗan mutum? Ƙaramin abu ne gidan Yahuda su yi abubuwan banƙyamar da suke yi a nan? Dole ne su cika ƙasar da rikici su kuma ci gaba da tsokane ni in yi fushi? Dube su suna tsokanata!

  8. Saboda haka zan hukunta su cikin fushi; Ba zan dube su da tausayi ko kuwa in ƙyale su ba. Ko da yake suna ihu a kunnuwana, ba zan saurare su ba.”

  9. “Ɗan mutum, ka yi magana da dattawan Isra’ila ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa kun zo ne ku nemi shawarata? Muddin ina raye, ba zan bari ku nemi shawarata ba, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’

  10. Yayinda da nake magana da addu’a, ina furta zunubina da zunubin mutanena Isra’ila ina miƙa koke-kokena ga Ubangiji Allahna saboda tudunsa mai tsarki,

  11. yayinda nake cikin addu’a, sai Jibra’ilu, mutumin nan da na gani a wahayin da ya wuce, ya zo wurina gaggauce wajen lokacin yin hadaya ta yamma.

  12. Ya umarce ni ya kuma ce mini, “Daniyel, yanzu na zo domin in ba ka hikima da ganewa.

  13. Da zarar ka fara addu’a, an amsa, wadda na zo in faɗa maka, gama ana ƙaunar ka sosai. Saboda haka, ka yi lura da saƙon ka kuma fahimci wahayin.

  14. Sai ya ci gaba da cewa, “Kada ka ji tsoro, Daniyel. Gama tun daga ran da ka fara sa zuciya ga neman ganewa, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gaban Allahnka, an ji addu’arka, amsar addu’arka ce ta kawo ni.

  15. Ya ce, “A cikin damuwata na yi kira ga Ubangiji, ya kuwa amsa mini. Daga cikin zurfi kabari na yi kiran neman taimako, ka kuwa saurari kukata.

  16. Sai Ubangiji ya umarci kifin, kifin kuwa ya amayar da Yunana a gaɓan teku.

  17. ku da kuke ƙin abu mai kyau kuke ƙaunar mugunta, ku da kuke feɗe mutanena kuke tuge nama daga ƙasusuwansu;

  18. ku da kuke cin naman mutanena, ku feɗe fatar jikinsu kuke kakkarya ƙasusuwansu, kuke yayyanka su gunduwa-gunduwa kamar naman da za a toya, kamar naman da za a sa a dafa.”

  19. Sa’an nan za su kira ga Ubangiji, amma ba zai amsa musu ba. A wannan lokaci zai ɓoye fuskarsa daga gare su saboda irin muguntar da suka yi.

  20. “Amma suka ƙi su saurara; da taurinkai suka juya bayansu suka kuma toshe kunnuwansu.

  21. Suka taurare zukatansu kamar dutse, suka ƙi jin abin da doka ko kuma maganar Ubangiji Maɗaukaki take faɗi wadda ya aika ta wurin Ruhunsa ta wurin annabawan farko. Saboda haka Ubangiji Maɗaukaki ya ji fushi ƙwarai.

  22. “ ‘Sa’ad da na yi kira, ba su saurara ba; saboda haka sa’ad da suka kira, ba zan saurara ba,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.

  23. “Kun ajiye abinci mai ƙazanta a kan bagadena. “Sai kuka ce, ‘Yaya muka ƙazantar da kai?’ “Ta wurin cewa teburin Ubangiji abin reni ne.

  24. Sa’ad da kuka kawo makauniyar dabba don ku miƙa mini hadaya, wannan daidai ne? Sa’ad da kuka miƙa gurguwar dabba ko marar lafiya, wannan daidai ne? Ku gwada ba wa gwamnanku irin wannan ku gani! Kuna gani zai ji daɗinku? Zai karɓe ku ne?” In ji Ubangiji Maɗaukaki.

  25. “To, firistoci yanzu ku gwada ku roƙi Allah yă yi mana alheri. Da irin hadayun nan a hannuwanku ne zai ji ku?” In ji Ubangiji Maɗaukaki.