Lehi
31.7500, 34.9700 Duba a Google Maps
Ayoyin da suka ambaci Lehi
Filistiyawa suka haura suka yi sansani a Yahuda, suka bazu kusa da Lehi.
Yayinda ya zo gab da Lehi, sai Filistiyawa suka sheƙo a guje da ihu suka nufo shi. Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko da iko a kansa. Igiyoyin da suke daure a hannuwansa kuwa suka zama kamar abin da wuta ta babbaka, suka tsintsinke suka zuba daga hannuwansa.
Sa’an nan Allah ya buɗe wani rami a Lehi, ruwa kuwa ya fito daga ciki. Da Samson ya sha, sai ƙarfinsa ya dawo, ya kuma wartsake. Aka sa wa wannan maɓulɓula suna En Hakkore, yana nan a Lehi har wa yau.