Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Answers To Prayer

195 ayoyi · 85 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Allah kuwa ya ji kukansu sai ya tuna da alkawarinsa da Ibrahim da Ishaku da Yaƙub.

  2. Sai Musa ya yi kuka ga Ubangiji ya ce, “Me zan yi da wannan jama’a? Suna shiri su jajjefe ni da duwatsu.”

  3. Ubangiji amsa wa Musa, “Ka ɗauki sandan da ka bugi ruwan Nilu da shi. Ka kira waɗansu shugabannin Isra’ila, ku wuce a gaban jama’ar.

  4. Zan tsaya a can a gabanka, kusa da dutsen Horeb. Ka bugi dutsen, ruwa kuwa zai fito daga gare shi domin mutane su sha.” Sai Musa ya yi haka a idon dattawan Isra’ila.

  5. Muddin hannun Musa yana a miƙe, sai Isra’ilawa su yi ta cin nasara, amma da zarar hannunsa ya sauka, sai Amalekawa su yi ta cin nasara.

  6. Sa’ad da hannuwan Musa suka gaji, sai Haruna da Hur suka ɗauki dutse suka sa ya zauna a kai. Sa’an nan su kuma suka tsaya gefe da gefe, suna riƙe da hannuwansa har fāɗuwar rana.

  7. Sai Yoshuwa kuwa ya ci nasara a kan Amalekawa da takobi.

  8. Amma Musa ya nemi tagomashin Ubangiji, Allahnsa ya ce, “Ya Ubangiji don me fushinka zai yi ƙuna a kan mutanenka, waɗanda ka fisshe su daga Masar da ikon hannunka mai girma?

  9. Don me za ka sa Masarawa su ce, ‘Ai, da mugun nufi ne ya fito da su don yă shafe su daga fuskar duniya’? Ka juya daga fushinka mai zafi, ka ji tausayi, kada ka kawo masifa a kan mutanenka.

  10. Ka tuna da bayinka Ibrahim, Ishaku da Isra’ila, waɗanda ka rantse da kanka cewa, ‘Zan mai da zuriyarka kamar taurarin sama kuma zan ba wa zuriyarka wannan ƙasa wadda na yi musu alkawari, za tă kuma zama abin gādonsu har abada.’ ”

  11. Sai Ubangiji ya yi juyayi, bai kuwa kawo wa mutanensa bala’in da ya yi niyya ba.

  12. Saboda ƙishirwa ta kama shi ƙwarai, sai ya ce wa Ubangiji, “Ka ba bawanka wannan babbar nasara. To, sai in mutu da ƙishirwa, har in shiga a hannun marasa kaciyan nan su kashe ni?”

  13. Sa’an nan Allah ya buɗe wani rami a Lehi, ruwa kuwa ya fito daga ciki. Da Samson ya sha, sai ƙarfinsa ya dawo, ya kuma wartsake. Aka sa wa wannan maɓulɓula suna En Hakkore, yana nan a Lehi har wa yau.

  14. Wannan yaron ne na roƙa daga wurin Ubangiji, ya kuwa ba ni abin da na roƙa daga gare shi.

  15. Sama’ila ya kama ɗan rago ya miƙa shi ɗungum hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Ya yi roƙo ga Ubangiji a madadin Isra’ila, Ubangiji kuwa ya amsa addu’arsa.

  16. Sama’ila ya ce wa Shawulu, “Don me ka dame ni, ta wurin hauro da ni?” Shawulu ya ce, “Ina cikin babban damuwa ce, Filistiyawa sun fāɗa mini, Allah kuma ya juya mini baya. Bai amsa mini, ko ta mafarki, ko kuma ta annabawa ba, saboda haka na kira ka don ka gaya mini abin yi.”

  17. Saboda haka ka ba bawanka zuciyar ganewa, don yă shugabanci mutanenka, yă kuma iya rarrabe tsakanin abin da yake daidai da abin da ba daidai ba. Gama wa zai iya shugabance wannan mutanenka masu girma haka?”

  18. zan yi abin da ka roƙa. Zan ba ka zuciya mai hikima da ta ganewa, har yă zama ba a taɓa samun wani kamar ka ba, ba kuwa za a taɓa samunsa ba.

  19. Sai sarki ya ce wa mutumin Allah, “Ka roƙi Ubangiji Allahnka, ka kuma yi addu’a domina don hannuna ya warke.” Saboda haka mutumin Allah ya yi roƙo ga Ubangiji, hannun sarki kuwa ya warke, ya kuma zama kamar yadda yake a dā.

  20. A lokacin hadaya, sai annabi Iliya ya zo gaba ya yi addu’a, ya ce, “Ya Ubangiji Allah na Ibrahim, na Isra’ila da kuma na Yaƙub, bari a sani a yau cewa kai Allah ne a cikin Isra’ila, a kuma san cewa ni bawanka ne, na kuma yi dukan waɗannan abubuwa bisa umarninka.

  21. Ka amsa mini, ya Ubangiji, ka amsa mini, saboda waɗannan mutane su san cewa kai, ya Ubangiji, kai ne Allah, su kuma san cewa kana sāke juye zukatansu zuwa gare ka.”

  22. Sai wutar Ubangiji ya fāɗo, ya cinye hadayar, itacen, duwatsun da kuma ƙasar, ya lashe ruwan da yake cikin wuriyar.

  23. Sai ya shiga, ya rufe ƙofa, daga shi sai yaron, ya kuma yi addu’a ga Ubangiji.

  24. Sa’an nan ya hau gadon yă kwanta a bisa yaron, ya miƙe a kansa, baki da baki, ido da ido, hannu da hannu. Yayinda ya miƙe kansa a kan yaron, sai jikin yaron ya ɗau ɗumi.

  25. Elisha ya tashi, ya yi ta kai komo a cikin ɗakin. Sa’an nan ya sāke koma kan gadon yă miƙe a kan yaron, sai yaron ya yi atishawa sau bakwai, ya kuma buɗe idanunsa.