Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446–1406 BC

The Wilderness Years

Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.

2,247 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ƙidaya 13:5kusan 1490 K.H.

    Shafat ɗan Hori, daga kabilar Simeyon;

  2. Ƙidaya 13:6kusan 1490 K.H.

    Kaleb ɗan Yefunne, daga kabilar Yahuda;

  3. Ƙidaya 13:7kusan 1490 K.H.

    Igal ɗan Yusuf, daga kabilar Issakar;

  4. Ƙidaya 13:8kusan 1490 K.H.

    Hosheya ɗan Nun, daga kabilar Efraim;

  5. Ƙidaya 13:9kusan 1490 K.H.

    daga kabilar Benyamin, Falti ɗan Rafu;

  6. Ƙidaya 13:10kusan 1490 K.H.

    Gaddiyel ɗan Sodi, daga kabilar Zebulun;

  7. Ƙidaya 13:11kusan 1490 K.H.

    Gaddi ɗan Susi, daga kabilar Manasse (wata kabilar Yusuf);

  8. Ƙidaya 13:12kusan 1490 K.H.

    Ammiyel ɗan Gemalli, daga kabilar Dan;

  9. Ƙidaya 13:13kusan 1490 K.H.

    Setur ɗan Mika’ilu, daga kabilar Asher;

  10. Ƙidaya 13:14kusan 1490 K.H.

    Nabi ɗan Bofsi, daga kabilar Naftali;

  11. Ƙidaya 13:15kusan 1490 K.H.

    Geyuwel ɗan Maki, daga kabilar Gad.

  12. Ƙidaya 13:16kusan 1490 K.H.

    Waɗannan su ne sunayen mutanen da Musa ya aika su binciki ƙasar. (Sai Musa ya ba Hosheya ɗan Nun, suna Yoshuwa.)

  13. Ƙidaya 13:17kusan 1490 K.H.

    Sa’ad da Musa ya aike su domin su binciki Kan’ana ya ce, “Ku haura, ku ratsa ta Negeb har zuwa ƙasar tudu.

  14. Ƙidaya 13:18kusan 1490 K.H.

    Ku ga yadda ƙasar take, ku ga ko mutanen da suke zama a can ƙarfafa ne, ko raunannu, ko su kima ne, ko kuma suna da yawa.

  15. Ƙidaya 13:19kusan 1490 K.H.

    Wace irin ƙasa ce suke zama a ciki, Mai kyau ce, ko mummuna? Waɗanne irin birane ne suke zama a ciki? Suna da katanga, ko babu?

  16. Ƙidaya 13:20kusan 1490 K.H.

    Yaya ƙasar take? Tana da wadata, ko babu? Akwai itatuwa, ko babu? Ku yi iya ƙoƙarinku ku ɗebo daga cikin albarkar ƙasar ku kawo.” (Lokacin farkon nunan inabi ne.)

  17. Ƙidaya 13:21kusan 1490 K.H.

    Saboda haka suka haura, suka binciki ƙasar daga Hamadan Zin har zuwa Rehob, wajen Lebo Hamat.

  18. Ƙidaya 13:22kusan 1490 K.H.

    Suka kuma haura ta Negeb, suka iso Hebron, inda Ahiman, da Sheshai, da Talmai, zuriyar Anak, suke zama. (An gina Hebron da shekara bakwai kafin a gina Zowan a Masar.)

  19. Ƙidaya 13:23kusan 1490 K.H.

    Da suka iso Kwarin Eshkol, sai suka yanko reshe guda na nonon inabi tare da ’ya’yansa cunkus. Mutum biyu suka ɗauka shi rataye a sanda a kafaɗarsu, suka haɗa tare da rumman da kuma ɓaure.

  20. Ƙidaya 13:24kusan 1490 K.H.

    Sai aka kira wurin Kwarin Eshkol saboda nonon inabin da suka yi cunkus, wanda Isra’ilawa suka yanko a wurin.

  21. Ƙidaya 13:25kusan 1490 K.H.

    A ƙarshen kwana arba’in sai suka komo daga bincikensu.

  22. Ƙidaya 13:26kusan 1490 K.H.

    Suka dawo wurin Musa, da Haruna, da dukan jama’ar Isra’ilawa, a Kadesh, a Hamadan Faran. A can suka ba da rahoton ga dukan taron da yake wurin, suka kuma nuna musu amfanin ƙasar.

  23. Ƙidaya 13:27kusan 1490 K.H.

    Suka ce wa Musa, “Mun je ƙasar da ka aike mu, ƙasar tana zub da madara da zuma! Ga kuma amfaninta.

  24. Ƙidaya 13:28kusan 1490 K.H.

    Amma fa mazaunan can ɗin ƙarfafa ne, an kuma kewaye biranen da manya-manyan katanga. Mun kuma ga zuriyar Anak a can.

  25. Ƙidaya 13:29kusan 1490 K.H.

    Amalekawa suna zama a Negeb; Hittiyawa, Yebusiyawa da kuma Amoriyawa, suna zama ne a ƙasar tudu. Kan’aniyawa kuma suna zama kusa da teku da kuma a bakin Urdun.”