- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1446–1406 BC
The Wilderness Years
Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Ƙidaya 11:31kusan 1490 K.H.
Ana nan, sai Ubangiji ya kawo wata iska mai tsanani ta koro makware daga teku. Ta bar su birjik kewaye da sansani, tsayinsu daga ƙasa ya kai kamu biyu, misalin tafiyar nisan yini guda ta kowace fuska.
- Ƙidaya 11:32kusan 1490 K.H.
Dukan yini da dukan dare da kuma kashegari, mutane suka fito suka tattara makware. Ba wanda ya kāsa tara ƙasa da garwa goma. Sai suka shanya abinsu kewaye da sansanin.
- Ƙidaya 11:33kusan 1490 K.H.
Amma da suna cikin cin naman, tun ba su ma haɗiye ba, sai Ubangiji ya husata sosai a kan jama’ar, ya buge su da annoba mai zafi.
- Ƙidaya 11:34kusan 1490 K.H.
Saboda haka aka kira wannan wuri Kibrot Hatta’awa, gama a can ne aka binne mutanen nan makwaɗaita.
- Ƙidaya 11:35kusan 1490 K.H.
Daga Kibrot Hatta’awa, mutane suka yi tafiya zuwa Hazerot, a can suka sauka.
- Ƙidaya 12:1kusan 1490 K.H.
Miriyam da Haruna suka fara zargin Musa saboda matarsa ’yar ƙasar Kush da ya aura.
- Ƙidaya 12:2kusan 1490 K.H.
Suka ce, “Ubangiji ya yi magana ta wurin Musa ne kaɗai? Ashe, bai yi magana ta wurinmu mu ma ba?” Ubangiji kuwa ya ji wannan.
- Ƙidaya 12:3kusan 1490 K.H.
(Musa kuwa mutum ne mai tawali’u ƙwarai, mafi tawali’u fiye da kowane mutum a duniya.)
- Ƙidaya 12:4kusan 1490 K.H.
Nan da nan Ubangiji ya ce wa Musa, da Haruna da kuma Miriyam, “Ku fita ku tafi Tentin Sujada, dukanku uku.” Sai dukansu uku suka tafi.
- Ƙidaya 12:5kusan 1490 K.H.
Sai Ubangiji ya sauko a cikin ginshiƙin girgije; ya tsaya a bakin ƙofar Tenti, ya kira Haruna da Miriyam. Sa’ad da su biyu suka gusa gaba,
- Ƙidaya 12:6kusan 1490 K.H.
sai ya ce, “Ku ji abin da zan faɗa, “Duk lokacin da akwai annabin Ubangiji a cikinku, nakan bayyana kaina gare shi cikin wahayi, in yi magana da shi cikin mafarkai.
- Ƙidaya 12:7kusan 1490 K.H.
Amma ba haka nake magana da Musa bawana ba; na sa shi yă lura da dukan jama’ata Isra’ila.
- Ƙidaya 12:8kusan 1490 K.H.
Da shi nake magana fuska da fuska, a fili kuma, ba a kacici-kacici ba; yakan ga siffar Ubangiji. To, me ya sa ba ku ji tsoro ku yi magana a kan bawana Musa ba?”
- Ƙidaya 12:9kusan 1490 K.H.
Sai fushin Ubangiji ya yi ƙuna a kansu, ya kuma rabu da su.
- Ƙidaya 12:10kusan 1490 K.H.
Da girgijen ya tashi daga bisa Tentin, sai ga Miriyam tsaye, kuturwa, fari fat. Haruna kuwa ya juya wajenta ya ga ta kuturce;
- Ƙidaya 12:11kusan 1490 K.H.
sai Haruna ya ce wa Musa, “Ranka yă daɗe, ina roƙonka kada ka hukunta mu, gama zunubin da muka yi, mun yi ne cikin wauta.
- Ƙidaya 12:12kusan 1490 K.H.
Kada ka sa ta zama kamar haifaffen mataccen jariri daga cikin mahaifiya wanda rabin jikin ruɓaɓɓe ne.”
- Ƙidaya 12:13kusan 1490 K.H.
Saboda haka sai Musa ya yi kuka ga Ubangiji ya ce, “Ya Allah, ina roƙonka ka warkar da ita!”
- Ƙidaya 12:14kusan 1490 K.H.
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Da a ce mahaifinta ne ya tofa mata miyau a fuskarta, ashe, ba za tă ji kunya har kwana bakwai ba? A fitar da ita bayan sansani kwana bakwai; bayan haka za a iya dawo da ita.”
- Ƙidaya 12:15kusan 1490 K.H.
Haka aka fitar da Miriyam bayan sansani kwana bakwai, mutane kuwa ba su ci gaba da tafiya ba sai da aka dawo da ita.
- Ƙidaya 12:16kusan 1490 K.H.
Bayan haka sai mutane suka bar Hazerot suka sauka a Hamadan Faran.
- Ƙidaya 13:1kusan 1490 K.H.
Ubangiji ya ce wa Musa,
- Ƙidaya 13:2kusan 1490 K.H.
“Ka aiki waɗansu mutane zuwa ƙasar Kan’ana, wadda nake ba Isra’ilawa. Daga kowace kabila, ka aiki ɗaya daga cikin shugabanninta.”
- Ƙidaya 13:3kusan 1490 K.H.
Saboda haka bisa ga umarnin Ubangiji, Musa ya aike su daga Hamadan Faran. Dukansu kuwa shugabanni ne na Isra’ilawa.
- Ƙidaya 13:4kusan 1490 K.H.
Shugabannin kuwa su ne, Shammuwa ɗan Zakkur, daga kabilar Ruben;