Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446–1406 BC

The Wilderness Years

Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.

2,247 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ƙidaya 10:17kusan 1490 K.H.

    Sa’an nan aka saukar da tabanakul ƙasa, Gershonawa da mutanen Merari da suke ɗauke da shi suka kama hanya.

  2. Ƙidaya 10:18kusan 1490 K.H.

    Sai ɓangarori sansanin Ruben suka biyo, bisa ga ƙa’idar da aka yi, aka kuma umarta. Elizur ɗan Shedeyur ne shugaba.

  3. Ƙidaya 10:19kusan 1490 K.H.

    Shelumiyel ɗan Zurishaddai ne shugaban ɓangaren kabilar Simeyon,

  4. Ƙidaya 10:20kusan 1490 K.H.

    Eliyasaf ɗan Deyuwel kuma shi ne shugaban ɓangaren kabilar Gad.

  5. Ƙidaya 10:21kusan 1490 K.H.

    Sai Kohatawa suka kama hanya, ɗauke da kayayyaki masu tsarki, domin kafin su kai wurin da za a kafa sansani, a riga an kafa tabanakul.

  6. Ƙidaya 10:22kusan 1490 K.H.

    Biye da waɗannan kuma sai ɓangaren sansanin kabilar Efraim suka biyo bisa ga ƙa’ida da aka yi, aka kuma umarta. Elishama ɗan Ammihud ne shugaba.

  7. Ƙidaya 10:23kusan 1490 K.H.

    Gamaliyel ɗan Fedazur ne shugaban ɓangaren kabilar Manasse,

  8. Ƙidaya 10:24kusan 1490 K.H.

    Abidan ɗan Gideyoni kuma shi ne shugaban ɓangaren kabilar Benyamin.

  9. Ƙidaya 10:25kusan 1490 K.H.

    A ƙarshe, a matsayi masu gadin bayan dukan ɓangarori, sai ɓangaren sansanin Dan suka tashi bisa ga ƙa’idar da aka yi, aka kuma umarta. Ahiyezer ɗan Ammishaddai ne shugaba.

  10. Ƙidaya 10:26kusan 1490 K.H.

    Fagiyel ɗan Okran ne shugaban ɓangaren kabilan Asher,

  11. Ƙidaya 10:27kusan 1490 K.H.

    Ahira ɗan Enan kuma shi ne shugaban kabilar Naftali.

  12. Ƙidaya 10:28kusan 1490 K.H.

    Wannan shi ne tsarin tafiyar ɓangarorin Isra’ilawa, sa’ad da sukan kama hanya.

  13. Ƙidaya 10:29kusan 1490 K.H.

    Sai Musa ya ce wa Hobab ɗan Reyuwel Bamidiyane surukinsa, “Yanzu fa, muna shirin tashi ne daga nan, domin mu tafi inda Ubangiji ya ce, ‘Zan ba ku.’ Ka zo tare da mu, za mu kuwa yi maka alheri, gama Ubangiji ya yi wa Isra’ilawa alkawari abubuwa masu kyau.”

  14. Ƙidaya 10:30kusan 1490 K.H.

    Ya amsa, ya ce “A’a, ba zan tafi ba; zan koma ƙasata da kuma wurin mutanena.”

  15. Ƙidaya 10:31kusan 1490 K.H.

    Amma Musa ya ce, “Ina roƙonka kada ka rabu da mu. Ka san inda ya kamata mu kafa sansani a hamada, za ka kuma zama idanunmu.

  16. Ƙidaya 10:32kusan 1490 K.H.

    In ka zo tare da mu, za mu raba duk abin alherin Ubangiji ya ba mu tare da kai.”

  17. Ƙidaya 10:33kusan 1490 K.H.

    Saboda haka suka kama hanya daga dutsen Ubangiji, suka yi tafiya kwana uku. Akwatin alkawarin Ubangiji ya ja gabansu a waɗannan kwanaki uku, don yă samo musu masauƙi.

  18. Ƙidaya 10:34kusan 1490 K.H.

    A duk lokacin da suka tashi daga sansani, girgijen Ubangiji ya inuwantar da su da rana.

  19. Ƙidaya 10:35kusan 1490 K.H.

    Duk kuma sa’ad da akwatin ya kama hanya, sai Musa ya ce, “Ka tashi, ya Ubangiji! Ka sa maƙiyanka su warwatse; masu ƙinka kuma su gudu a gabanka.”

  20. Ƙidaya 10:36kusan 1490 K.H.

    Duk sa’ad da akwatin ya sauka kuma, sai Musa ya ce, “Ka komo, ya Ubangiji, a wurin dubban da ba a iya ƙidayawa na iyalan Isra’ila.”

  21. Ƙidaya 11:1kusan 1490 K.H.

    Da Ubangiji ya ji gunagunin da mutanen suke yi saboda wahalarsu, sai ya husata ƙwarai. Sai wuta daga Ubangiji ta yi ta ci a cikinsu har ta ƙone waɗansu wurare na sansanin.

  22. Ƙidaya 11:2kusan 1490 K.H.

    Da jama’ar suka yi wa Musa kuka, sai ya yi addu’a ga Ubangiji, wutar kuwa ta mutu.

  23. Ƙidaya 11:3kusan 1490 K.H.

    Saboda haka aka kira wannan wuri Tabera, gama a wurin ne wuta daga Ubangiji ta ƙuna a cikinsu.

  24. Ƙidaya 11:4kusan 1490 K.H.

    Wata rana, baƙin da suke cikinsu, suka fara kwaɗayin waɗansu abinci, har suka sa Isra’ilawa suka fara kuka, suna cewa, “Da mun sami nama mun ci mana!

  25. Ƙidaya 11:5kusan 1490 K.H.

    Mun tuna da kifin da muka ci kyauta a Masar, haka ma kayan lambu irin su kukumba, guna, safa, albasa da kuma tafarnuwa.