Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446–1406 BC

The Wilderness Years

Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.

2,247 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ƙidaya 9:15kusan 1490 K.H.

    A ranar da aka kafa Tenti na Alkawari, sai girgije ya rufe shi. Daga yamma har safe, girgijen da yake bisa tabanakul ya yi kama da wuta.

  2. Ƙidaya 9:16kusan 1490 K.H.

    Haka ya ci gaba da kasancewa; girgijen ya rufe shi, da dare kuma sai ya yi kamar wuta.

  3. Ƙidaya 9:17kusan 1490 K.H.

    Duk sa’ad da aka ɗaga girgijen daga Tentin, sai Isra’ilawa su kama hanya; duk inda girgijen ya tsaya, a nan Isra’ilawa za su yi sansani.

  4. Ƙidaya 9:18kusan 1490 K.H.

    Da umarnin Ubangiji, Isra’ilawa suke tashi. Da umarninsa kuma suke sauka. Muddin girgijen yana tsaye a bisa tabanakul, sukan yi ta zamansu a sansanoni.

  5. Ƙidaya 9:19kusan 1490 K.H.

    Sa’ad da girgijen ya ci gaba da kasancewa a bisan tabanakul na dogon lokaci, Isra’ilawa sukan bi umarnin Ubangiji, ba kuwa za su tashi ba.

  6. Ƙidaya 9:20kusan 1490 K.H.

    Wani lokaci girgijen yakan yi ’yan kwanaki ne kawai a bisa tabanakul; da umarnin Ubangiji sukan kafa sansani da umarninsa kuma su tashi.

  7. Ƙidaya 9:21kusan 1490 K.H.

    Wani lokaci girgijen yakan zauna daga yamma har safiya ne kawai, sa’ad da kuma aka ɗaga shi da safe, sai su kama hanya. Ko da rana, ko da dare, duk sa’ad da aka ɗaga girgijen, sai su ma su tashi.

  8. Ƙidaya 9:22kusan 1490 K.H.

    Ko girgijen ya yi kwana biyu a bisa tabanakul, ko wata guda, ko shekara, Isra’ilawa za su zauna a sansani ba kuwa za su tashi ba; amma sa’ad da aka ɗaga shi, sai su kuma su tashi.

  9. Ƙidaya 9:23kusan 1490 K.H.

    Da umarnin Ubangiji sukan kafa sansani, da umarninsa kuma sukan tashi. Sukan bi umarnin Ubangiji, bisa ga umarninsa ta wurin Musa.

  10. Ƙidaya 10:1kusan 1490 K.H.

    Ubangiji ya ce wa Musa,

  11. Ƙidaya 10:2kusan 1490 K.H.

    “Ka ƙera kakaki guda biyu na azurfa, ka kuma yi amfani da su don kira taron jama’a wuri ɗaya, don kuma ka riƙa sanar da su lokacin tashi daga sansani.

  12. Ƙidaya 10:3kusan 1490 K.H.

    Sa’ad da aka busa su biyu, dukan jama’a za su taru a gabanka a ƙofar Tentin Sujada.

  13. Ƙidaya 10:4kusan 1490 K.H.

    In ɗaya ne kaɗai aka busa, sai shugabannin kabilan Isra’ila, su taru a gabanka.

  14. Ƙidaya 10:5kusan 1490 K.H.

    Sa’ad da aka ji karar busar kakaki, sai sansanin da yake a gabashi, su kama hanya.

  15. Ƙidaya 10:6kusan 1490 K.H.

    A kara ta biyu, sansanin da yake a kudanci, su kama hanya. Busan kakaki zai zama alama ta kama hanya.

  16. Ƙidaya 10:7kusan 1490 K.H.

    In don a tara jama’a ne, sai a busa kakaki, amma ba da irin alama ɗaya ba.

  17. Ƙidaya 10:8kusan 1490 K.H.

    “’Ya’yan Haruna, firistoci ne, za su busa kakaki. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla gare ku da kuma tsararraki masu zuwa.

  18. Ƙidaya 10:9kusan 1490 K.H.

    Duk lokacin da za ku tafi yaƙi a ƙasarku, in akwai waɗansu da suke matsa muku, za ku yi amfani da waɗannan kakaki ta wurin hura su, alama ce, cewa za a je yaƙi. Sa’an nan Ubangiji Allahnku zai tuna da ku, yă cece ku daga maƙiyanku.

  19. Ƙidaya 10:10kusan 1490 K.H.

    Haka ma in kuna cikin jin daɗinku, musamman lokacin da kuke bukukkuwanku, kamar Bikin Sabon Wata da dai kowane Bikinku, za ku hura waɗannan kakaki lokacin da kuke miƙa hadayunku na ƙonawa, da hadayunku na salama, za su kuma zama muku abin tunawa a gaban Allahnku. Ni ne Ubangiji Allahnku.”

  20. Ƙidaya 10:11kusan 1490 K.H.

    A rana ta ashirin ga wata na biyu, a shekara ta biyu, sai girgijen ya tashi daga tabanakul na Shaida.

  21. Ƙidaya 10:12kusan 1490 K.H.

    Sai Isra’ilawa suka tashi daki-daki daga Hamadar Sinai, suna tafiya daga wuri zuwa wuri, har sai da girgijen ya tsaya a Hamadar Faran.

  22. Ƙidaya 10:13kusan 1490 K.H.

    Suka kama hanya, a wannan lokaci, bisa umarnin Ubangiji, ta wurin Musa.

  23. Ƙidaya 10:14kusan 1490 K.H.

    Ɓangarorin sansanin Yahuda suka fara tashi, bisa ga ƙa’idar da aka yi, aka kuma umarta. Nashon ɗan Amminadab ne shugaba.

  24. Ƙidaya 10:15kusan 1490 K.H.

    Netanel ɗan Zuwar ne shugaban ɓangaren kabilar Issakar,

  25. Ƙidaya 10:16kusan 1490 K.H.

    Eliyab ɗan Helon kuma shi ne shugaban ɓangaren kabilar Zebulun.