Tsallake zuwa abun ciki

circa 6 BC – AD 30

The Life of Jesus

The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.

3,779 ayoyi · 4 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Mattiyu 4:11kusan 26 M.

    Sa’an nan Iblis ya bar shi, mala’iku kuwa suka zo suka yi masa hidima.

  2. Mattiyu 4:12kusan 26 M.

    Da Yesu ya ji labari cewa an kulle Yohanna a kurkuku, sai ya koma zuwa Galili.

  3. Mattiyu 4:13kusan 26 M.

    Ya bar Nazaret, ya je ya zauna a Kafarnahum, wadda take a bakin tafki wajen Zebulun da Naftali

  4. Mattiyu 4:14kusan 26 M.

    don a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya cewa,

  5. Mattiyu 4:15kusan 26 M.

    “Ƙasar Zebulun da ƙasar Naftali, da kuke a hanyar zuwa tekun Galili, a ƙetaren Urdun, wannan yankin Galili ta Al’ummai,

  6. Mattiyu 4:16kusan 26 M.

    mutanen da suke zama cikin duhu sun ga babban haske; haske kuma ya haskaka a kan waɗanda suke zama a inuwar mutuwa.”

  7. Mattiyu 4:17kusan 26 M.

    Tun daga wannan lokaci, Yesu ya fara wa’azi yana cewa, “Ku tuba, gama mulkin sama ya yi kusa.”

  8. Mattiyu 4:18kusan 26 M.

    Da Yesu yana kan tafiya a bakin Tekun Galili, sai ya ga waɗansu ’yan’uwa guda biyu, Siman wanda ake kira Bitrus da ɗan’uwansa Andarawus. Suna jefa abin kamun kifi a tafki, gama su masunta ne.

  9. Mattiyu 4:19kusan 26 M.

    Sai Yesu ya ce, “Zo, ku bi ni, ni kuwa zan mai da ku masu jan mutane zuwa wurina.”

  10. Mattiyu 4:20kusan 26 M.

    Nan da nan suka bar abin kamun kifinsu suka bi shi.

  11. Mattiyu 4:21kusan 26 M.

    Da ya ci gaba daga nan, sai ya ga waɗansu ’yan’uwa guda biyu, Yaƙub ɗan Zebedi da ɗan’uwansa Yohanna. Suna cikin jirgin ruwa tare da mahaifinsu Zebedi, suna shirya abin kamun kifinsu. Yesu ya kira su,

  12. Mattiyu 4:22kusan 26 M.

    nan take suka bar jirgin ruwan da mahaifinsu suka kuwa bi Yesu.

  13. Mattiyu 4:23kusan 26 M.

    Yesu ya zazzaga dukan Galili, yana koyarwa a cikin majami’unsu, yana wa’azin labari mai daɗi na mulkin sama, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiyar mutane.

  14. Mattiyu 4:24kusan 26 M.

    Labarinsa ya bazu ko’ina a Suriya, mutane kuwa suka kawo masa dukan waɗanda suke fama da cututtuka iri-iri, da waɗanda suke da zafin ciwo, da masu aljanu, da waɗanda suke masu farfaɗiya, da shanyayyu, ya kuwa warkar da su.

  15. Mattiyu 4:25kusan 26 M.

    Taron mutane mai yawa daga Galili, Dekafolis, Urushalima, Yahudiya da kuma yankin hayin Urdun suka bi shi.

  16. Mattiyu 5:1kusan 31 M.

    Ganin taron mutane, sai ya hau kan gefen dutse ya zauna. Almajiransa kuwa suka zo wurinsa,

  17. Mattiyu 5:2kusan 31 M.

    sai ya fara koya musu. Yana cewa,

  18. Mattiyu 5:3kusan 31 M.

    “Masu albarka ne waɗanda suke matalauta a ruhu, gama mulkin sama nasu ne.

  19. Mattiyu 5:4kusan 31 M.

    Masu albarka ne waɗanda suke makoki, gama za a yi musu ta’aziyya.

  20. Mattiyu 5:5kusan 31 M.

    Masu albarka ne waɗanda suke masu tawali’u, gama za su gāji duniya.

  21. Mattiyu 5:6kusan 31 M.

    Masu albarka ne waɗanda suke jin yunwa da ƙishirwa don gani an yi adalci, gama za a ƙosar da su.

  22. Mattiyu 5:7kusan 31 M.

    Masu albarka ne waɗanda suke masu jinƙai, gama za a nuna musu jinƙai.

  23. Mattiyu 5:8kusan 31 M.

    Masu albarka ne waɗanda suke masu tsabtar zuciya, gama za su ga Allah.

  24. Mattiyu 5:9kusan 31 M.

    Masu albarka ne waɗanda suke masu ƙulla zumunci, gama za a kira su ’ya’yan Allah.

  25. Mattiyu 5:10kusan 31 M.

    Masu albarka ne waɗanda ake tsananta musu don gani an yi adalci, gama mulkin sama nasu ne.