Tsallake zuwa abun ciki

circa 800–400 BC

The Hebrew Prophets

God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.

3,706 ayoyi · 14 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Yowel 2:28kusan 800 K.H.

    “Daga baya kuma, zan zuba Ruhuna a bisan dukan mutane. ’Ya’yanku maza da mata za su yi annabci, tsofaffinku za su yi mafarkai, matasanku za su ga wahayoyi.

  2. Yowel 2:29kusan 800 K.H.

    Har ma a bisan bayina, maza da mata, zan zuba Ruhuna a kwanakin nan.

  3. Yowel 2:30kusan 800 K.H.

    Zan nuna abubuwan banmamaki a cikin sammai da kuma a kan duniya, za a ga jini da wuta da murtukewar hayaƙi.

  4. Yowel 2:31kusan 800 K.H.

    Rana za tă duhunta wata kuma yă zama jini kafin isowar babbar ranan nan mai banrazana ta Ubangiji.

  5. Yowel 2:32kusan 800 K.H.

    Amma dukan waɗanda suka nemi Ubangiji za su tsira. Kamar yadda Ubangiji ya ce, gama a Dutsen Sihiyona da Urushalima akwai ceto, a cikin waɗannan da Ubangiji ya kira.

  6. Yowel 3:1kusan 800 K.H.

    “A waɗancan kwanaki da kuma a wancan lokaci, sa’ad da zan maido da arzikin Yahuda da Urushalima,

  7. Yowel 3:2kusan 800 K.H.

    zan tattara dukan al’ummai in kuma kawo su Kwarin Yehoshafat Can zan yi musu shari’a game da gādona, mutanena Isra’ila, gama sun warwatsar da mutanena a cikin al’ummai sun kuma raba ƙasata.

  8. Yowel 3:3kusan 800 K.H.

    Sun jefa ƙuri’a a kan mutanena suna kuma sayar da yara maza don karuwanci, sun sayar da ’yan matan domin ruwan inabi wanda za su sha.

  9. Yowel 3:4kusan 800 K.H.

    “Yanzu mene ne damuwarku da ni, ya Taya da Sidon da kuma dukan mazaunan yankunan Filistiya? Kuna ƙoƙari ku sāka mini don abin da na yi ne? In kuna sāka mini ne, to, da gaggawa zan mayar muku da sakayya a kanku.

  10. Yowel 3:5kusan 800 K.H.

    Gama kun kwashe azurfata da zinariyata kun kuma washe dukiyata mafi kyau kun kai cikin haikalinku.

  11. Yowel 3:6kusan 800 K.H.

    Kun sayar da mutanen Yahuda da na Urushalima ga mutanen Hellenawa, don ku aika da su nesa da ƙasarsu.

  12. Yowel 3:7kusan 800 K.H.

    “Duba, zan dawo da su daga wuraren da kuka sayar da su, in kuma yi muku abin da kuka yi musu.

  13. Yowel 3:8kusan 800 K.H.

    Zan sayar da ’ya’yanku maza da mata ga mutanen Yahuda, su kuma za su sayar da su ga mutanen Sabenawa, al’umma da take nesa da ku.” Ubangiji ya faɗa.

  14. Yowel 3:9kusan 800 K.H.

    Ku yi shelar wannan ga al’ummai. Ku yi shirin yaƙi! Ku tā da jarumawa! Bari mayaƙa su ja kusa su kai hari.

  15. Yowel 3:10kusan 800 K.H.

    Ku bubbuge garemaninku su zama takuba da kuma laujenku su zama māsu. Bari raunana su ce, “Ni mai ƙarfi ne!”

  16. Yowel 3:11kusan 800 K.H.

    Ku gaggauta, dukanku al’ummai daga kowane ɓangare, ku tattaru a can. Ka sauko da mayaƙanka, ya Ubangiji!

  17. Yowel 3:12kusan 800 K.H.

    “Bari a tā da dukan al’ummai; bari su kutsa zuwa Kwarin Yehoshafat gama a can zan zauna in shari’anta dukan al’ummai daga kowane ɓangare.

  18. Yowel 3:13kusan 800 K.H.

    Ku fito da lauje, gama girbi ya nuna. Ku zo, ku tattaka inabin, gama wurin matsewar ruwan inabi ya cika randunan tarawa kuma sun cika har suna zuba, muguntarsu da girma take!”

  19. Yowel 3:14kusan 800 K.H.

    Dubun dubbai suna a cikin kwarin yanke shawara! Gama ranar Ubangiji ta yi kusa a cikin kwarin yanke shawara.

  20. Yowel 3:15kusan 800 K.H.

    Za a duhunta rana da wata, taurari kuma ba za su ba da haske ba.

  21. Yowel 3:16kusan 800 K.H.

    Ubangiji zai yi ruri daga Sihiyona tsawa kuma daga Urushalima; duniya da sararin sama za su yi rawan jiki. Amma Ubangiji zai zama mafakar mutanensa, mafaka ga mutanensa Isra’ila.

  22. Yowel 3:17kusan 800 K.H.

    “Sa’an nan za ku san cewa ni, Ubangiji Allahnku, ina zaune a Sihiyona, dutsena mai tsarki. Urushalima za tă zama mai tsarki; baƙi ba za su ƙara mamaye ta ba.

  23. Yowel 3:18kusan 800 K.H.

    “A wannan rana duwatsu za su ɗiga da sabon ruwan inabi, tuddai kuma za su malmalo madara; dukan rafuffukan Yahuda za su yi ta gudano da ruwa. Maɓulɓula kuma za tă fito daga gidan Ubangiji haka ma ruwa a kwarin itatuwan ƙirya.

  24. Yowel 3:19kusan 800 K.H.

    Amma Masar za tă zama kango, Edom kuma hamada marar amfani, saboda kama-karyar da aka yi wa mutanen Yahuda, a ƙasar da aka zub da jinin marasa laifi.

  25. Yowel 3:20kusan 800 K.H.

    Za a zauna a Yahuda har abada Urushalima kuma daga tsara zuwa tsara.