Tsallake zuwa abun ciki

circa 800–400 BC

The Hebrew Prophets

God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.

3,706 ayoyi · 14 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Yowel 2:3kusan 800 K.H.

    A gabansu wuta tana ci, a bayansu ga harshen wuta yana ci, A gabansu ƙasa ta yi kamar gonar Eden, a bayansu kuma jeji ne wofi, babu abin da ya kuɓuce musu.

  2. Yowel 2:4kusan 800 K.H.

    Suna da kamannin dawakai; suna gudu kamar dokin yaƙi.

  3. Yowel 2:5kusan 800 K.H.

    Da motsi kamar na kekunan yaƙi sun tsallake ƙwanƙolin duwatsu, kamar ƙarar harshen wuta mai cin tattaka, kamar runduna mai ƙarfi wadda ta ja dāgār yaƙi.

  4. Yowel 2:6kusan 800 K.H.

    Da ganinsu, al’ummai sun kamu da azaba; kowace fuska ta yanƙwane.

  5. Yowel 2:7kusan 800 K.H.

    Sukan auka kamar jarumawa; sukan hau katanga kamar sojoji. Kowa yana takawa bisa ga tsari, ba mai kaucewa.

  6. Yowel 2:8kusan 800 K.H.

    Ba sa turin juna, kowane yakan miƙe gaba. Sukan kutsa cikin abokan gāba ba mai tsai da su.

  7. Yowel 2:9kusan 800 K.H.

    Sukan ruga cikin birni, suna gudu a kan katanga. Sukan hau gidaje, sukan shiga ta tagogi kamar ɓarayi.

  8. Yowel 2:10kusan 800 K.H.

    A gabansu duniya takan girgiza, sararin sama kuma yakan jijjigu, rana da wata su yi duhu, taurari kuma ba sa ba da haske.

  9. Yowel 2:11kusan 800 K.H.

    Ubangiji ya yi tsawa wa shugaban mayaƙansa; sojojinsa sun fi a ƙirge masu ƙarfi ne kuma su waɗanda suke biyayya da umarninsa. Ranar Ubangiji da girma take; mai banrazana. Wa zai iya jure mata?

  10. Yowel 2:12kusan 800 K.H.

    “Ko yanzu”, in ji Ubangiji, “Ku juyo gare ni da dukan zuciyarku, da azumi da kuka da makoki.”

  11. Yowel 2:13kusan 800 K.H.

    Ku kyakkece zuciyarku ba rigunanku ba. Ku juyo ga Ubangiji Allahnku, gama shi mai alheri ne mai tausayi kuma mai jinkirin fushi da yawan ƙauna, yakan kuma janye daga aika da bala’i.

  12. Yowel 2:14kusan 800 K.H.

    Wa ya sani? Ko zai juya yă kuma ji tausayi yă sa mana albarka ta wurin hadaya ta gari da hadaya ta sha wa Ubangiji Allahnku.

  13. Yowel 2:15kusan 800 K.H.

    A busa ƙaho a Sihiyona, a yi shelar azumi mai tsarki, a kira tsarkakan taro.

  14. Yowel 2:16kusan 800 K.H.

    A tattara mutane; ku tsarkake taron; ku kawo dattawa wuri ɗaya; ku kuma tara yara, da waɗanda suke shan mama. Bari ango yă bar ɗakinsa amarya kuma lolokinta.

  15. Yowel 2:17kusan 800 K.H.

    Bari firistocin da suke yin hidima a gaban Ubangiji, su yi kuka tsakanin filin haikali da bagade. Bari su ce, “Ka cece mutanenka, ya Ubangiji. Kada ka bar gādonka yă zama abin dariya, da abin ba’a a cikin al’ummai. Me zai sa a ce a cikin mutane, ‘Ina Allahnsu yake?’ ”

  16. Yowel 2:18kusan 800 K.H.

    Ta haka Ubangiji zai yi kishin ƙasarsa yă kuma ji tausayin mutanensa.

  17. Yowel 2:19kusan 800 K.H.

    Ubangiji zai amsa musu ya ce, “Ina aika da hatsi, sabon ruwan inabi, da mai, isashe da zai ƙosar da ku sosai; ba kuma zan ƙara maishe ku abin dariya ga al’ummai ba.

  18. Yowel 2:20kusan 800 K.H.

    “Zan kori sojojin arewa nesa da ku, in tura su cikin busasshiyar ƙasa marar amfani kuma, kuma da sawunsu na gaba zan tura su zuwa gabashin teku da kuma sawunsu na baya tura su zuwa yammanci a Bahar Rum. Warinsu kuma zai bazu; ɗoyinsu zai tashi.” Tabbatacce ya yi al’amura masu girma.

  19. Yowel 2:21kusan 800 K.H.

    Kada ki ji tsoro, ya ƙasa; ki yi murna ki kuma yi farin ciki. Tabbatacce Ubangiji ya yi abubuwa masu girma.

  20. Yowel 2:22kusan 800 K.H.

    Kada ku ji tsoro, ya ku namun jeji, gama wuraren kiwo sun yi kore shar. Itatuwa suna ba da ’ya’yansu; itacen ɓaure da na inabi suna ba da amfaninsu.

  21. Yowel 2:23kusan 800 K.H.

    Ku yi murna, ya ku mutanen Sihiyona, ku yi farin ciki cikin Ubangiji Allahnku, gama ya ba ku ruwan bazara cikin adalci. Yakan aika muku yayyafi a yalwace, na bazara da na kaka, kamar dā.

  22. Yowel 2:24kusan 800 K.H.

    Masussukai za su cika da hatsi; randuna za su cika da sabon ruwan inabi da mai suna zuba.

  23. Yowel 2:25kusan 800 K.H.

    “Zan mayar muku da abin da fāra suka ci a waɗannan shekaru waɗanda ɗango da fāra masu gaigayewa, da kuma sauran fāra da tarin fāra babban mayaƙan da na aika don su fāɗa muku.

  24. Yowel 2:26kusan 800 K.H.

    Za ku sami a wadace ku ci, har sai kun ƙoshi, za ku kuma yabi sunan Ubangiji Allahnku, wanda ya yi muku ayyukan banmamaki; mutanena ba za su ƙara shan kunya ba.

  25. Yowel 2:27kusan 800 K.H.

    Sa’an nan za ku sani ina cikin Isra’ila, cewa ni ne Ubangiji Allahnku, babu wani kuma; mutanena ba za su ƙara shan kunya ba.