Tsallake zuwa abun ciki

circa 800–400 BC

The Hebrew Prophets

God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.

3,706 ayoyi · 14 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Amos 2:10kusan 787 K.H.

    Na fitar da ku daga ƙasar Masar, na kuma bishe ku tsawon shekaru arba’in a cikin hamada don in ba ku ƙasar Amoriyawa.

  2. Amos 2:11kusan 787 K.H.

    “Na kuma tā da annabawa daga cikin ’ya’yanku maza waɗansu kuma su zama keɓaɓɓu daga cikin samarinku. Ba haka ba ne, mutanen Isra’ila?” In ji Ubangiji.

  3. Amos 2:12kusan 787 K.H.

    “Amma kuka sa keɓaɓɓun suka sha ruwan inabi kuka kuma umarci annabawa kada su yi annabci.

  4. Amos 2:13kusan 787 K.H.

    “Saboda haka, yanzu zan murƙushe ku kamar yadda amalanke yakan murƙushe sa’ad da aka yi masa labtun hatsi.

  5. Amos 2:14kusan 787 K.H.

    Masu gudu da sauri ba za su tsira ba, masu ƙarfi ba za su iya yin amfani da ƙarfinsu ba, jarumi kuma ba zai iya ceton ransa ba.

  6. Amos 2:15kusan 787 K.H.

    ’Yan baka ba za su iya dāgewa ba, masu saurin gudu ba za su tsira ba mahayin dawakai kuma ba zai tsere da ransa ba.

  7. Amos 2:16kusan 787 K.H.

    Ko jarumawa mafi jaruntaka za su gudu tsirara a ranan nan,” in ji Ubangiji.

  8. Amos 3:1kusan 787 K.H.

    Ku ji wannan maganar da Ubangiji ya yi game da ku, ya ku jama’ar Isra’ila, a kan dukan iyalin da na fitar daga Masar.

  9. Amos 3:2kusan 787 K.H.

    “Ku ne kaɗai na zaɓa cikin dukan al’umman duniya; saboda haka zan hukunta ku saboda dukan zunubanku.”

  10. Amos 3:3kusan 787 K.H.

    Mutum biyu za su iya yin tafiya tare in ba su yarda su yi haka ba?

  11. Amos 3:4kusan 787 K.H.

    Zaki yakan yi ruri a jeji in bai sami kama nama ba? Zai yi gurnani a cikin kogonsa in bai kama kome ba?

  12. Amos 3:5kusan 787 K.H.

    Tsuntsu yakan fāɗa a tarko a ƙasa inda ba a sa tarko ba, ko tarko yakan zargu daga ƙasa in ba abin da ya taɓa shi?

  13. Amos 3:6kusan 787 K.H.

    Idan aka busa ƙaho a ciki birni mutane ba sa yin rawar jiki? Sa’ad da bala’i ya auko wa birni, ba Ubangiji ne ya sa a kawo shi ba?

  14. Amos 3:7kusan 787 K.H.

    Ba shakka, Ubangiji Mai Iko Duka ba ya yin wani abu ba tare da ya sanar wa bayinsa annabawa ba.

  15. Amos 3:8kusan 787 K.H.

    Zaki ya yi ruri, wa ba zai tsorata ba? Ubangiji Mai Iko Duka ya yi magana, wa ba zai yi annabci ba?

  16. Amos 3:9kusan 787 K.H.

    Ku yi shela ga kagarun Ashdod da kuma ga kagarun Masar. “Ku tara kanku a tuddan Samariya; ku ga rashin jituwar da take a cikinta, da kuma zaluncin da ake yi a cikin mutanenta.”

  17. Amos 3:10kusan 787 K.H.

    “Ba su ma san yadda za su yi abin da yake daidai ba,” in ji Ubangiji, “sun ɓoye ganima da abubuwan da suka washe a cikin kagarunsu.”

  18. Amos 3:11kusan 787 K.H.

    Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce, “Abokin gāba zai ƙwace ƙasar, zai saukar da mafakarku, zai washe kagarunku.”

  19. Amos 3:12kusan 787 K.H.

    Ga abin da Ubangiji ya ce, “Kamar yadda makiyayi yakan ceci daga bakin zaki ƙasusuwa ƙafafu biyu kawai ko kunne ɗaya, haka za a ceci Isra’ilawa, masu zama a Samariya da kan gado kawai da kuma a ɗan ƙyalle a kan dogayen kujerunsu.”

  20. Amos 3:13kusan 787 K.H.

    “Ku ji wannan ku kuma yi wa gidan Yaƙub gargaɗi,” in ji Ubangiji, Ubangiji Allah Maɗaukaki.

  21. Amos 3:14kusan 787 K.H.

    “A ranar da zan hukunta Isra’ila saboda zunubanta, zan hallaka bagadan Betel; za a yayyanka ƙahonin bagadan za su fāɗa ƙasa

  22. Amos 3:15kusan 787 K.H.

    Zan rushe gidan rani da na damina; gidajen da aka yi musu ado da hauren giwa za a rushe su haka ma duk za a rurrushe manyan gidaje,” in ji Ubangiji.

  23. Amos 4:1kusan 787 K.H.

    Ku kasa kunne ga wannan, ya ku shanun Bashan a kan Dutsen Samariya, ku matan da kuke cin zalin matalauta, kuke kuma danne matalauta, kuna kuma ce wa mazanku, “Ku kawo mana abin sha!”

  24. Amos 4:2kusan 787 K.H.

    Ubangiji Mai Iko Duka ya rantse da tsarkinsa. “Tabbatacce lokaci yana zuwa da za a jawo ku da ƙugiyoyi, na ƙarshenku za a kama da ƙugiyar kifi.

  25. Amos 4:3kusan 787 K.H.

    Dukanku za ku wuce ta kai tsaye ta inda katangar ta tsage, za a jefar da ku a Harmon,” in ji Ubangiji.