Tsallake zuwa abun ciki

circa 800–400 BC

The Hebrew Prophets

God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.

3,706 ayoyi · 14 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Amos 4:4kusan 787 K.H.

    “Ku tafi Betel ku yi ta aikata zunubi; ku je Gilgal ku ƙara yin zunubi. Ku kawo hadayunku kowace safiya, zakkarku kowace shekara uku.

  2. Amos 4:5kusan 787 K.H.

    Ku ƙona burodinku mai yisti kamar hadaya ta godiya, ku yi fariya game da hadayunku na yarda rai, ku yi taƙama game da su, ya ku Isra’ilawa, gama abin da kuke jin daɗin aikata ke nan,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

  3. Amos 4:6kusan 787 K.H.

    “Na bar ku da yunwa a kowace birni, da kuma rashin abinci a kowane gari, duk da haka ba ku juyo gare ni ba,” in ji Ubangiji.

  4. Amos 4:7kusan 787 K.H.

    “Na kuma hana muku ruwan sama tun shuke-shuken suna wata uku kafin lokacin girbi. Na sa aka yi ruwan sama a wani gari, sai na hana a yi a wani gari. Wata gona ta sami ruwan sama; wata gona kuma ta bushe.

  5. Amos 4:8kusan 787 K.H.

    Mutane suna tangaɗi daga gari zuwa gari suna neman ruwa amma ba su sami isashen ruwan sha ba, duk da haka ba ku juyo gare ni ba,” in ji Ubangiji.

  6. Amos 4:9kusan 787 K.H.

    “Sau da yawa na ɓata gonakinku da fumfuna da kuma cuta. Fāri suka cinye itatuwanku na inabi da na ɓaure, da na zaitun duk da haka ba ku juyo gare ni ba,” in ji Ubangiji.

  7. Amos 4:10kusan 787 K.H.

    “Na aiko muku annoba yadda na yi a Masar. Na karkashe samarinku da takobi, tare da kamammun dawakanku. Na cika hancinku da warin sansaninku, duk da haka ba ku juyo gare ni ba” in ji Ubangiji.

  8. Amos 4:11kusan 787 K.H.

    “Na hallaka waɗansunku kamar yadda na hallaka Sodom da Gomorra. Kuna kama da itace mai cin wutar da na cire daga cikin wuta, duk da haka ba ku juyo gare ni ba,” in ji Ubangiji.

  9. Amos 4:12kusan 787 K.H.

    “Saboda haka ga abin da zan yi da ku, ya Isra’ila, don kuwa zan yi muku haka, sai ku yi shirin gamuwa da Allahnku, ya Isra’ila.”

  10. Amos 4:13kusan 787 K.H.

    Shi wanda ya yi duwatsu, ya halicci iska, ya kuma bayyana wa mutum tunaninsa, shi wanda ya juya safiya ta zama duhu yana takawa a wurare masu tsawo na duniya, Ubangiji Allah Maɗaukaki ne sunansa.

  11. Amos 5:1kusan 787 K.H.

    Ku ji wannan magana, ya gidan Isra’ila, ina makokin nan dominku.

  12. Amos 5:2kusan 787 K.H.

    “Budurwa Isra’ila ta fāɗi, ba za tă ƙara tashi ba, an yashe ta a ƙasarta, ba wanda zai ɗaga ta.”

  13. Amos 5:3kusan 787 K.H.

    Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce, “Birnin da ta fitar da masu ƙarfi dubbai don Isra’ila guda ɗari kaɗai za su dawo; garin da ya fitar da masu ƙarfi ɗari kuwa goma kaɗai za su dawo.”

  14. Amos 5:4kusan 787 K.H.

    Ga abin da Ubangiji ya ce wa gidan Isra’ila. “Ku neme ni ku rayu;

  15. Amos 5:5kusan 787 K.H.

    kada ku nemi Betel, kada ku je Gilgal, kada ku yi tafiya zuwa Beyersheba. Gama ba shakka Gilgal za tă tafi bauta, za a kuwa mai da Betel ba kome ba.”

  16. Amos 5:6kusan 787 K.H.

    Ku nemi Ubangiji ku kuma rayu, ko kuwa zai ratsa yă share gidan Yusuf kamar wuta; zai cinye Betel kuwa ba zai sami wanda zai kashe ta ba.

  17. Amos 5:7kusan 787 K.H.

    Ku ne masu mai da gaskiya ta koma ɗaci ku kuma zubar da adalci.

  18. Amos 5:8kusan 787 K.H.

    (Shi wanda ya yi Taurarin nan da ake ce Kaza da ’Ya’yanta da kuma Mai Farauta da Kare, wanda ya mai da duhu ya zama haske ya kuma baƙanta rana ta zama dare, yakan kwashe ruwan teku ya zubar a ƙasa, Ubangiji ne sunansa,

  19. Amos 5:9kusan 787 K.H.

    yakan kawo hallaka a mafaka mai ƙarfi yakan kuma mai da birnin mai katanga ya zama kufai).

  20. Amos 5:10kusan 787 K.H.

    Ba ku son mai yin gaskiya a ɗakin shari’a kuna ƙin mai faɗar gaskiya.

  21. Amos 5:11kusan 787 K.H.

    Kuna matsa wa matalauta kuna sa su dole su ba ku hatsi. Saboda haka, ko da yake kun gina gidajen duwatsu, ba za ku zauna a cikinsu ba; ko da yake kun nome gonaki masu kyau, ba za ku sha ruwan inabinsu ba.

  22. Amos 5:12kusan 787 K.H.

    Gama na san yawan laifofinku da kuma girman zunubanku. Kuna danne masu adalci kuna kuma cin hanci kuna kuma hana a yi wa matalauta shari’ar adalci a majalisa.

  23. Amos 5:13kusan 787 K.H.

    Saboda haka mai hankali yakan yi shiru a lokuta kamar haka, gama lokutan mugaye ne.

  24. Amos 5:14kusan 787 K.H.

    Ku yi nagarta, ba mugunta ba; don ku rayu sa’an nan Ubangiji Allah Maɗaukaki zai kasance da ku, kamar yadda kuka ce zai yi.

  25. Amos 5:15kusan 787 K.H.

    Ku ƙi mugunta, ku ƙaunaci nagarta; ku dinga yin shari’ar gaskiya a ɗakunan shari’a. Mai yiwuwa Ubangiji Allah Maɗaukaki zai ji tausayin raguwar Yusuf.