Tsallake zuwa abun ciki

circa 1900–1700 BC

Jacob, Joseph & Egypt

Jacob wrestles with God and becomes Israel; Joseph is sold into slavery yet rises to save the world from famine.

840 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. Farawa 43:3kusan 1707 K.H.

    Amma Yahuda ya ce masa, “Mutumin ya gargaɗe mu sosai cewa, ‘Ba za ku sāke ganin fuskata ba sai in ɗan’uwanku yana tare da ku.’

  2. Farawa 43:4kusan 1707 K.H.

    In za ka aika da ɗan’uwanmu tare da mu, za mu gangara mu sayo maka abinci.

  3. Farawa 43:5kusan 1707 K.H.

    Amma in ba za ka aika da shi ba, ba za mu gangara ba, gama mutumin ya ce mana, ‘Ba za ku sāke ganin fuskata ba sai ko in ɗan’uwanku yana tare da ku.’ ”

  4. Farawa 43:6kusan 1707 K.H.

    Isra’ila ya yi tambaya, “Me ya sa kuka kawo wannan damuwa a kaina ta wurin faɗa wa mutumin cewa kuna da wani ɗan’uwa?”

  5. Farawa 43:7kusan 1707 K.H.

    Suka amsa, “Mutumin ya yi mana tambaya sosai game da kanmu da iyalinmu. Ya tambaye mu, ‘Mahaifinku yana da rai har yanzu? Kuna da wani ɗan’uwa?’ Mu dai mun amsa tambayoyinsa ne. Ta yaya za mu sani zai ce, ‘Ku kawo ɗan’uwanku a nan’?”

  6. Farawa 43:8kusan 1707 K.H.

    Sa’an nan Yahuda ya ce wa Isra’ila mahaifinsa, “Ka aika saurayin tare da ni za mu kuwa tafi nan da nan, saboda mu da ’ya’yanmu mu rayu, kada mu mutu.

  7. Farawa 43:9kusan 1707 K.H.

    Ni kaina zan tabbatar da lafiyarsa; na ɗauki lamuninsa, a hannuna za ka neme shi. In ban dawo da shi gare ka, in sa shi nan a gabanka ba, zan ɗauki laifin a gabanka dukan kwanakina.

  8. Farawa 43:10kusan 1707 K.H.

    Ai, da ba mun jinkirta ba, da mun komo har sau biyu.”

  9. Farawa 43:11kusan 1707 K.H.

    Sa’an nan mahaifinsu Isra’ila ya ce musu, “In dole ne a yi haka, to, sai ku yi. Ku sa waɗansu amfani mafi kyau na ƙasar a buhunanku, ku ɗauka zuwa wurin mutumin a matsayin kyauta, da ɗan man ƙanshi na shafawa, da kuma ’yar zuma, da kayan yaji, da ƙaro, da tsabar citta da kuma almon.

  10. Farawa 43:12kusan 1707 K.H.

    Ku ɗauki ninki biyu na yawan azurfa tare da ku, gama dole ku mayar da azurfan da aka sa a cikin bakunan buhunanku. Mai yiwuwa an yi haka a kuskure ne.

  11. Farawa 43:13kusan 1707 K.H.

    Ku ɗauki ɗan’uwanku kuma ku koma wurin mutumin nan da nan.

  12. Farawa 43:14kusan 1707 K.H.

    Bari Allah Maɗaukaki yă nuna muku alheri a gaban mutumin saboda yă bar ɗan’uwanku da Benyamin su dawo tare da ku. Ni kuwa, in na yi rashi, na yi rashi.”

  13. Farawa 43:15kusan 1707 K.H.

    Saboda haka mutanen suka ɗauki kyautar, da kuma kuɗin da ya ninka na farko. Suka kuma ɗauki Benyamin, suka gaggauta suka gangara zuwa Masar suka kuma gabatar da kansu ga Yusuf.

  14. Farawa 43:16kusan 1707 K.H.

    Sa’ad da Yusuf ya ga Benyamin tare da su, sai ya ce wa mai hidimar gidansa, “Ka shigar da mutanen cikin gida, ka yanka dabba ka shirya, gama mutanen za su ci abincin rana tare da ni.”

  15. Farawa 43:17kusan 1707 K.H.

    Mutumin ya yi kamar yadda Yusuf ya faɗa masa, ya kuwa ɗauki mutanen zuwa gidan Yusuf.

  16. Farawa 43:18kusan 1707 K.H.

    Mutanen dai suka firgita sa’ad da aka ɗauke su zuwa gidansa. Suka yi tunani, “An kawo mu nan ne saboda azurfan da aka sa a cikin buhunanmu da farko. Yana so yă fāɗa mana, yă kuma sha ƙarfinmu, yă ƙwace mu kamar bayi, yă kuma kwashe jakunanmu.”

  17. Farawa 43:19kusan 1707 K.H.

    Saboda haka suka je wurin mai yin wa Yusuf hidima, suka yi masa magana a bakin ƙofar gida.

  18. Farawa 43:20kusan 1707 K.H.

    Suka ce, “Ranka yă daɗe, mun zo nan ƙaro na farko don mu saya abinci,

  19. Farawa 43:21kusan 1707 K.H.

    amma a inda muka tsaya don mu kwana, da muka buɗe buhunanmu sai kowannenmu ya sami azurfansa daidai a bakin buhunsa. Saboda haka ga kuɗin a hannunmu, mun sāke komowa da su.

  20. Farawa 43:22kusan 1707 K.H.

    Mun kuma kawo ƙarin azurfa tare da mu don mu saya abinci. Ba mu san wa ya sa azurfanmu a cikin buhunanmu ba.”

  21. Farawa 43:23kusan 1707 K.H.

    Sai mai hidimar ya ce, “Ba kome, kada ku ji tsoro. Allahnku, Allahn mahaifinku ne ya ba ku dukiyar a cikin buhunanku; ni dai, na karɓi azurfanku.” Sa’an nan ya fitar musu da Simeyon.

  22. Farawa 43:24kusan 1707 K.H.

    Mai yin hidimar ya ɗauki mutane zuwa gidan Yusuf ya ba su ruwa su wanke ƙafafunsu, ya kuma tanada wa jakunansu abinci.

  23. Farawa 43:25kusan 1707 K.H.

    Suka shirya kyautansu domin isowar Yusuf da rana, gama sun ji cewa zai ci abinci a nan.

  24. Farawa 43:26kusan 1707 K.H.

    Sa’ad da Yusuf ya zo gida, sai suka ba shi kyautai da suka kawo, suka rusuna a gabansa har ƙasa.

  25. Farawa 43:27kusan 1707 K.H.

    Ya tambaye su, yaya suke, sa’an nan ya ce, “Yaya tsohon nan mahaifinku da kuka faɗa mini? Yana da rai har yanzu?”