Tsallake zuwa abun ciki

circa 1900–1700 BC

Jacob, Joseph & Egypt

Jacob wrestles with God and becomes Israel; Joseph is sold into slavery yet rises to save the world from famine.

840 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. Farawa 43:28kusan 1707 K.H.

    Suka amsa, “Bawanka mahaifinmu yana da rai har yanzu da kuma ƙoshin lafiya.” Suka kuma rusuna suka yi mubaya’a.

  2. Farawa 43:29kusan 1707 K.H.

    Da ya ɗaga idanu, sai ya ga ɗan’uwansa Benyamin, ɗan mahaifiyarsa, sai ya yi tambaya, “Wannan ne ƙaramin ɗan’uwanku, wanda kuka faɗa mini a kai?” Ya kuma ce, “Allah yă yi maka albarka, ɗana.”

  3. Farawa 43:30kusan 1707 K.H.

    Saboda motsi mai zurfi da zuciyarsa ta yi da ganin ɗan’uwansa, sai Yusuf ya gaggauta ya fita, ya nemi wuri yă yi kuka. Ya shiga ɗakinsa ya yi kuka a can.

  4. Farawa 43:31kusan 1707 K.H.

    Bayan ya wanke fuskarsa, sai ya fito ya daure, ya umarta, “A kawo abinci.”

  5. Farawa 43:32kusan 1707 K.H.

    Sai aka raba musu abinci, nasa shi kaɗai su kuma su kaɗai, domin Masarawa ba sa cin abinci tare da Ibraniyawa, gama wannan abin ƙyama ne ga Masarawa.

  6. Farawa 43:33kusan 1707 K.H.

    Aka zaunar da ’yan’uwan Yusuf a gabansa bisa ga shekarunsu, daga ɗan fari zuwa auta. ’Yan’uwan kuwa suka duddubi juna suna mamaki.

  7. Farawa 43:34kusan 1707 K.H.

    Daga teburin da yake a gaban Yusuf aka riƙa ɗibar rabonsu ana kai musu, amma rabon Benyamin ya yi biyar ɗin na kowannensu. Suka kuwa sha, suka yi murna tare da shi.

  8. Farawa 44:1kusan 1707 K.H.

    Yusuf kuwa ya ba wa mai yin masa hidima a gida, waɗannan umarnai cewa, “Cika buhunan mutanen nan da abinci iyakar yadda za su iya ɗauka, ka kuma sa kuɗin kowanne a bakin buhunsa.

  9. Farawa 44:2kusan 1707 K.H.

    Sa’an nan ka sa kwaf nawa, wannan na azurfa a bakin buhun autan, tare da kuɗinsa na hatsi.” Sai mai hidimar ya yi kamar yadda Yusuf ya umarta.

  10. Farawa 44:3kusan 1707 K.H.

    Da gari ya waye, sai aka sallami mutanen tare da jakunansu.

  11. Farawa 44:4kusan 1707 K.H.

    Ba su yi nisa da birnin ba sa’ad da Yusuf ya ce wa mai yin masa hidima, “Tashi, ka bi waɗannan mutane nan da nan, in ka same su, ka ce musu, ‘Me ya sa kuka sāka alheri da mugunta?

  12. Farawa 44:5kusan 1707 K.H.

    Ba da wannan kwaf ne maigidana yake sha daga ciki yana kuma yin amfani da shi don duba? Wannan mugun abu ne da kuka yi.’ ”

  13. Farawa 44:6kusan 1707 K.H.

    Sa’ad da ya same su, sai ya maimaita waɗannan kalmomi gare su.

  14. Farawa 44:7kusan 1707 K.H.

    Amma suka ce masa, “Me ya sa ranka yă daɗe yake faɗin irin waɗannan abubuwa? Allah yă sawwaƙe bayinka su yi irin wannan abu!

  15. Farawa 44:8kusan 1707 K.H.

    Mun ma dawo maka da kuɗin da muka samu a cikin bakunan buhunanmu daga ƙasar Kan’ana. Saboda haka me zai sa mu saci azurfa ko zinariya daga gidan maigidanka?

  16. Farawa 44:9kusan 1707 K.H.

    In aka sami wani daga cikin bayinka da shi, zai mutu; sai sauran su zama bayin mai girma.”

  17. Farawa 44:10kusan 1707 K.H.

    Sai ya ce, “To, shi ke nan, bari yă zama yadda kuka faɗa. Duk wanda aka same shi da kwaf na azurfan zai zama bawana, sauran kuwa za su ’yantu daga zargin.”

  18. Farawa 44:11kusan 1707 K.H.

    Da sauri kowannensu ya sauko da buhunsa ƙasa, ya buɗe.

  19. Farawa 44:12kusan 1707 K.H.

    Sa’an nan mai hidimar ya fara bincike, farawa daga babba, ya ƙare a ƙaramin. Aka kuwa sami kwaf ɗin a buhun Benyamin.

  20. Farawa 44:13kusan 1707 K.H.

    Ganin wannan sai suka kyakkece rigunansu. Sa’an nan suka jibga wa jakunansu kaya, suka koma birni.

  21. Farawa 44:14kusan 1707 K.H.

    Yusuf yana nan har yanzu a gida sa’ad da Yahuda da ’yan’uwansa suka shiga, suka fāɗi rub da ciki a ƙasa a gabansa.

  22. Farawa 44:15kusan 1707 K.H.

    Yusuf ya ce musu, “Mene ne wannan da kuka yi? Ba ku san cewa mutum kamar ni yana iya gane abubuwa ta wurin duba ba?”

  23. Farawa 44:16kusan 1707 K.H.

    Yahuda ya amsa ya ce, “Me za mu ce wa ranka yă daɗe? Yaya kuma za mu wanke kanmu daga wannan zargi? Allah ya tona laifin bayinka. Ga mu, za mu zama bayinka, da mu da wanda aka sami kwaf ɗin a hannunsa.”

  24. Farawa 44:17kusan 1707 K.H.

    Amma Yusuf ya ce, “Allah yă sawwaƙe in yi haka! Mutumin da aka sami kwaf ɗin a hannunsa ne kaɗai zai zama bawana. Sauranku, ku koma ga mahaifinku da salama.”

  25. Farawa 44:18kusan 1707 K.H.

    Sai Yahuda ya haura zuwa wurinsa ya ce, “Ranka yă daɗe, roƙo nake, bari bawanka yă yi magana da ranka yă daɗe. Kada ka yi fushi da bawanka, ko da yake daidai kake da Fir’auna kansa.