Tsallake zuwa abun ciki

circa 1900–1700 BC

Jacob, Joseph & Egypt

Jacob wrestles with God and becomes Israel; Joseph is sold into slavery yet rises to save the world from famine.

840 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. Farawa 45:10kusan 1707 K.H.

    Za ka yi zama a yankin Goshen, ka kasance kusa da ni. Kai, ’ya’yanka da kuma jikokinka, garkunanka da shanunka, da kuma dukan abin da kake da shi.

  2. Farawa 45:11kusan 1707 K.H.

    Zan tanada maka a nan, domin akwai saura shekaru biyar na yunwa masu zuwa. In ba haka ba, kai da gidanka da dukan mallakarka za ku zama gajiyayyu.’

  3. Farawa 45:12kusan 1707 K.H.

    “Ku kanku kun gani, haka ma ɗan’uwana Benyamin, cewa tabbatacce ni ne nake magana da ku.

  4. Farawa 45:13kusan 1707 K.H.

    Faɗa wa mahaifina game da dukan girman da aka ba ni a Masar, da kuma game da kome da kuka gani. Ku kuma kawo mahaifina a nan da sauri.”

  5. Farawa 45:14kusan 1707 K.H.

    Sa’an nan ya rungume ɗan’uwansa Benyamin ya yi kuka, sai Benyamin ya rungume shi yana kuka.

  6. Farawa 45:15kusan 1707 K.H.

    Ya sumbaci dukan ’yan’uwansa, ya kuma yi kuka a kansu. Bayan haka sai ’yan’uwansa suka yi masa magana.

  7. Farawa 45:16kusan 1707 K.H.

    Sa’ad da labarin ya kai fadan Fir’auna cewa ’yan’uwan Yusuf sun zo, sai Fir’auna da dukan hafsoshin suka ji daɗi.

  8. Farawa 45:17kusan 1707 K.H.

    Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Faɗa wa ’yan’uwanka, ‘Yi wannan; ku jibge dabbobinku ku koma zuwa ƙasar Kan’ana,

  9. Farawa 45:18kusan 1707 K.H.

    Ku kawo mahaifinku da iyalanku zuwa wurina. Zan ba ku mafi kyau na ƙasar Masar, za ku kuwa ci moriyar ƙasar.’

  10. Farawa 45:19kusan 1707 K.H.

    “An kuma umarce ka, ka faɗa musu, ‘Ku yi wannan, ku ɗauki wagonu daga Masar domin ’ya’yanku da matanku, ku ɗauki mahaifinku ku zo.

  11. Farawa 45:20kusan 1707 K.H.

    Kada ku damu da mallakarku, gama mafi kyau na Masar za su zama naku.’ ”

  12. Farawa 45:21kusan 1707 K.H.

    Sai ’ya’yan Isra’ila maza suka yi haka. Yusuf ya ba su wagonu kamar yadda Fir’auna ya umarta, ya kuma ba su guzuri don tafiyarsu.

  13. Farawa 45:22kusan 1707 K.H.

    Ya ba da sababbin riguna ga kowannensu amma ga Benyamin ya ba shi shekel ɗari uku na azurfa da riguna kashi biyar.

  14. Farawa 45:23kusan 1707 K.H.

    Ga kuma abin da ya aika wa mahaifinsa, jakuna goma da aka jibge da abubuwa mafi kyau na Masar, da jakuna mata guda goma ɗauke da hatsi da burodi da waɗansu tanade-tanade don tafiyarsa.

  15. Farawa 45:24kusan 1707 K.H.

    Sa’an nan ya sallami ’yan’uwansa, yayinda suke barin wurin ya ce musu, “Kada ku yi faɗa a hanya!”

  16. Farawa 45:25kusan 1707 K.H.

    Saboda haka suka haura, suka fita daga Masar, suka zo wurin maihaifinsu Yaƙub a ƙasar Kan’ana.

  17. Farawa 45:26kusan 1707 K.H.

    Suka faɗa masa, “Yusuf yana da rai! Gaskiya, shi ne mai mulkin dukan Masar.” Gaban Yaƙub ya fāɗi, domin bai gaskata su ba.

  18. Farawa 45:27kusan 1707 K.H.

    Amma sa’ad da suka faɗa masa kome da Yusuf ya faɗa musu, da kuma sa’ad da ya ga wagonun da Yusuf ya aika don a ɗauke shi a kai da shi can, sai ya farfaɗo, ya dawo cikin hankalinsa.

  19. Farawa 45:28kusan 1707 K.H.

    Sai Yaƙub ya ce, “Na yarda! Ɗana Yusuf yana da rai har yanzu. Zan tafi in gan shi kafin in mutu.”

  20. Farawa 46:1kusan 1706 K.H.

    Saboda haka Isra’ila ya kama hanya da dukan abin da yake nasa, sa’ad da ya kai Beyersheba, sai ya miƙa hadayu ga Allah na Ishaku, mahaifinsa.

  21. Farawa 46:2kusan 1706 K.H.

    Allah kuwa ya yi magana ga Isra’ila a wahayi da dare ya ce, “Yaƙub! Yaƙub!” Yaƙub kuwa ya amsa ya ce, “Ga ni.”

  22. Farawa 46:3kusan 1706 K.H.

    Sai Allah ya ce, “Ni ne Allah, Allah na mahaifinka. Kada ka ji tsoron zuwa Masar, gama zan mai da kai al’umma mai girma a can.

  23. Farawa 46:4kusan 1706 K.H.

    Zan gangara zuwa Masar tare da kai, tabbatacce zan sāke dawo da kai. Kuma hannun Yusuf zai rufe idanunka.”

  24. Farawa 46:5kusan 1706 K.H.

    Sa’an nan Yaƙub ya bar Beyersheba, ’ya’yan Isra’ila maza, suka ɗauki mahaifinsu Yaƙub da ’ya’yansu da matansu a cikin wagonun da Fir’auna ya aika don a kawo shi.

  25. Farawa 46:6kusan 1706 K.H.

    Suka kuma ɗauki dabbobinsu da mallakarsu, da suka samu a Kan’ana, Yaƙub kuwa da dukan zuriyarsa suka tafi Masar.