- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1900–1700 BC
Jacob, Joseph & Egypt
Jacob wrestles with God and becomes Israel; Joseph is sold into slavery yet rises to save the world from famine.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Farawa 46:7kusan 1706 K.H.
Ya ɗauki ’ya’yansa maza da jikokinsa da ’ya’yansa mata da jikokinsa mata, dukan zuriyarsa zuwa Masar.
- Farawa 46:8kusan 1706 K.H.
Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan Isra’ila maza (Yaƙub da zuriyarsa) waɗanda suka tafi Masar, Ruben ɗan farin Yaƙub.
- Farawa 46:9kusan 1706 K.H.
’Ya’yan Ruben maza su ne, Hanok, Fallu, Hezron da Karmi.
- Farawa 46:10kusan 1706 K.H.
’Ya’yan Simeyon maza su ne, Yemuwel, Yamin, Ohad, Yakin, Zohar da Sha’ul ɗan mutuniyar Kan’ana.
- Farawa 46:11kusan 1706 K.H.
’Ya’yan Lawi maza su ne, Gershon, Kohat da Merari.
- Farawa 46:12kusan 1706 K.H.
’Ya’yan Yahuda maza su ne, Er, Onan, Shela, Ferez da Zera (amma Er da Onan sun mutu a ƙasar Kan’ana). ’Ya’yan Ferez maza su ne, Hezron da Hamul.
- Farawa 46:13kusan 1706 K.H.
’Ya’yan Issakar maza su ne, Tola, Fuwa, Yoshub da Shimron.
- Farawa 46:14kusan 1706 K.H.
’Ya’yan Zebulun maza su ne, Sered, Elon da Yaleyel.
- Farawa 46:15kusan 1706 K.H.
Waɗannan su ne ’ya’yan Liyatu maza da ta haifa wa Yaƙub a Faddan Aram, ban da ’yarsa Dina. ’Ya’yansa maza da mata duka, mutum talatin da uku ne.
- Farawa 46:16kusan 1706 K.H.
’Ya’yan Gad maza su ne, Zafon, Haggi, Shuni, Ezbon, Eri, Arodi da Areli.
- Farawa 46:17kusan 1706 K.H.
’Ya’yan Asher maza su ne, Imna, Ishba, Ishbi da Beriya. ’Yar’uwarsu ita ce Sera. ’Ya’yan Beriya maza su ne, Heber da Malkiyel.
- Farawa 46:18kusan 1706 K.H.
Waɗannan su ne ’ya’yan da Zilfa ta haifa wa Yaƙub, ita ce Laban ya ba wa ’yarsa Liyatu. ’Ya’yan duka, su sha shida ne.
- Farawa 46:19kusan 1706 K.H.
’Ya’yan Yaƙub maza waɗanda Rahila ta haifa su ne, Yusuf da Benyamin.
- Farawa 46:20kusan 1706 K.H.
A Masar, Asenat ’yar Fotifera, firist na On ta haifi Manasse da Efraim wa Yusuf.
- Farawa 46:21kusan 1706 K.H.
’Ya’yan Benyamin maza su ne, Bela, Beker, Ashbel, Gera, Na’aman, Ehi, Rosh, Muffim, Huffim da Ard.
- Farawa 46:22kusan 1706 K.H.
Waɗannan su ne ’ya’yan Rahila maza waɗanda ta haifa wa Yaƙub, dukansu mutum goma sha huɗu ne.
- Farawa 46:23kusan 1706 K.H.
Yaron Dan shi ne, Hushim.
- Farawa 46:24kusan 1706 K.H.
’Ya’yan Naftali maza su ne, Yazeyel, Guni, Yezer da Shillem.
- Farawa 46:25kusan 1706 K.H.
Waɗannan su ne ’ya’ya mazan da Bilha ta haifa wa Yaƙub, ita ce Laban ya ba wa ’yarsa Rahila. ’Ya’yan suka su bakwai ne.
- Farawa 46:26kusan 1706 K.H.
Dukan waɗanda suka tafi Masar tare da Yaƙub, waɗanda suke zuriyarsa kai tsaye ban da matan ’ya’yansa maza, su mutum sittin da shida ne.
- Farawa 46:27kusan 1706 K.H.
In aka haɗa da ’ya’yan nan maza guda biyu waɗanda aka haifa wa Yusuf a Masar, membobin iyalin Yaƙub, waɗanda suka tafi Masar, duka su saba’in ne.
- Farawa 46:28kusan 1706 K.H.
To, Yaƙub ya aiki Yahuda yă yi gaba yă sadu da Yusuf, don yă nuna musu hanyar da za su bi zuwa yankin Goshen. Da suka isa yankin Goshen,
- Farawa 46:29kusan 1706 K.H.
sai Yusuf ya kintsa keken yaƙinsa ya haura zuwa Goshen don yă taryi mahaifinsa, Isra’ila. Nan da nan da isowar Yusuf a wurin mahaifinsa, sai ya rungumi mahaifinsa, ya yi kuka na dogon lokaci.
- Farawa 46:30kusan 1706 K.H.
Isra’ila ya ce wa Yusuf, “Yanzu ina a shirye in mutu, da yake na gani da kaina cewa har yanzu kana da rai.”
- Farawa 46:31kusan 1706 K.H.
Sa’an nan Yusuf ya ce wa ’yan’uwansa da gidan mahaifinsa, “Zan haura in yi magana da Fir’auna, zan kuwa ce masa, ‘’Yan’uwana da gidan mahaifina, waɗanda suke zaune a ƙasar Kan’ana, sun zo wurina.