Tsallake zuwa abun ciki

circa 1900–1700 BC

Jacob, Joseph & Egypt

Jacob wrestles with God and becomes Israel; Joseph is sold into slavery yet rises to save the world from famine.

840 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. Farawa 44:19kusan 1707 K.H.

    Ranka yă daɗe ya tambayi bayinka ya ce, ‘Kuna da mahaifi ko ɗan’uwa?’

  2. Farawa 44:20kusan 1707 K.H.

    Muka kuwa amsa, ‘Muna da mahaifi tsoho, akwai kuma ɗa matashi, wanda aka haifa masa cikin tsufarsa. Ɗan’uwansa ya rasu, shi ne kuwa ɗa kaɗai na mahaifiyarsa da ya rage, mahaifinsa kuwa yana ƙaunarsa.’

  3. Farawa 44:21kusan 1707 K.H.

    “Sai ka ce wa bayinka, ‘Ku kawo mini shi don in gan shi da kaina.’

  4. Farawa 44:22kusan 1707 K.H.

    Muka kuwa ce wa ranka yă daɗe, ‘Saurayin ba zai iya barin mahaifinsa ba, gama in ya bar shi, mahaifinsa zai mutu.’

  5. Farawa 44:23kusan 1707 K.H.

    Amma ka faɗa wa bayinka, ‘Sai kun kawo ƙaramin ɗan’uwanku tare da ku, in ba haka ba, ba za ku sāke ganin fuskata ba.’

  6. Farawa 44:24kusan 1707 K.H.

    Sa’ad da muka koma wurin bawanka mahaifinmu, sai muka faɗa masa abin da ranka yă daɗe ya ce.

  7. Farawa 44:25kusan 1707 K.H.

    “Sai mahaifinmu ya ce, ‘Ku koma ku sayo ƙarin abinci.’

  8. Farawa 44:26kusan 1707 K.H.

    Amma muka ce, ‘Ba za mu iya gangarawa ba, sai in ƙaramin ɗan’uwanmu yana tare da mu. Ba za mu iya ganin fuskar mutumin ba, sai ƙaramin ɗan’uwanmu yana tare mu.’

  9. Farawa 44:27kusan 1707 K.H.

    “Bawanka mahaifinmu ya ce mana, ‘Kun san cewa matata ta haifa mini ’ya’ya biyu maza.

  10. Farawa 44:28kusan 1707 K.H.

    Ɗayansu ya tafi daga gare ni, na kuwa ce, “Tabbatacce an yayyage shi kaca-kaca.” Ban kuwa gan shi ba tuntuni.

  11. Farawa 44:29kusan 1707 K.H.

    In kun ɗauki wannan daga wurina shi ma wani abu ya same shi, za ku kawo furfura kaina zuwa kabari cikin baƙin ciki.’

  12. Farawa 44:30kusan 1707 K.H.

    “Saboda haka yanzu, in saurayin ba ya nan tare da mu sa’ad da na koma ga bawanka mahaifina, in kuma mahaifina, wanda ransa yana daure kurkusa da ran saurayin,

  13. Farawa 44:31kusan 1707 K.H.

    ya ga cewa saurayin ba ya nan, zai mutu. Bayinka za su sa bawanka, mahaifinmu, yă mutu cikin baƙin ciki, da tsufansa.

  14. Farawa 44:32kusan 1707 K.H.

    Gama ni baranka na ɗauki lamunin saurayin a wurin mahaifinsa da cewa, ‘In ban komo maka da shi ba, sai alhakinsa yă zauna a kaina a gaban mahaifina, dukan raina!’

  15. Farawa 44:33kusan 1707 K.H.

    “To, yanzu, ina roƙonka bari bawanka yă zauna a nan a matsayin bawanka, ranka yă daɗe a maimakon saurayin, a kuma bar saurayin yă koma da ’yan’uwansa.

  16. Farawa 44:34kusan 1707 K.H.

    Yaya zan koma ga mahaifina, in saurayin ba ya tare da ni? A’a! Kada ka bari in ga baƙin cikin da zai auko wa mahaifina.”

  17. Farawa 45:1kusan 1707 K.H.

    Yusuf bai ƙara iya daurewa a gaban dukan masu yi masa hidima ba, sai ya yi kuka da ƙarfi ya ce, “Kowa yă tashi daga gabana!” Saboda haka ba kowa a wurin sa’ad da Yusuf ya sanar da kansa ga ’yan’uwansa.

  18. Farawa 45:2kusan 1707 K.H.

    Sai ya yi kuka da ƙarfi har Masarawa suka ji, har labarin ya kai gidan Fir’auna.

  19. Farawa 45:3kusan 1707 K.H.

    Yusuf kuwa ya ce wa ’yan’uwansa, “Ni ne Yusuf! Mahaifina yana nan da rai har yanzu?” Amma ’yan’uwansa ba su iya amsa masa ba, gama sun firgita ƙwarai a gabansa.

  20. Farawa 45:4kusan 1707 K.H.

    Sa’an nan Yusuf ya ce wa ’yan’uwansa, “Ku zo kusa da ni.” Da suka yi haka, sai ya ce, “Ni ne ɗan’uwanku Yusuf, wannan da kuka sayar zuwa Masar!

  21. Farawa 45:5kusan 1707 K.H.

    Yanzu dai, kada ku damu, kada kuma ku yi fushi da kanku saboda kun sayar da ni a nan, gama Allah ya aiko ni gabanku ne don in ceci rayuka.

  22. Farawa 45:6kusan 1707 K.H.

    Ga shi shekaru biyu ke nan ake yunwa a ƙasar, kuma da sauran shekara biyar masu zuwa da ba za a yi noma ko girbi ba.

  23. Farawa 45:7kusan 1707 K.H.

    Amma Allah ya aiko ni gabanku ne don in adana muku raguwa a duniya, in kuma ceci rayukanku ta wurin ceto mai girma.

  24. Farawa 45:8kusan 1707 K.H.

    “Saboda haka fa, ba ku ba ne kuka aiko ni nan, Allah ne. Ya mai da ni mahaifi ga Fir’auna, shugaban dukan gidansa da kuma mai mulkin dukan Masar.

  25. Farawa 45:9kusan 1707 K.H.

    Yanzu sai ku gaggauta zuwa wurin mahaifina ku faɗa masa, ‘Abin da ɗanka Yusuf ya ce; Allah ya mai da ni shugaban dukan Masar. Gangaro wurina; kada ka jinkirta.