Tsallake zuwa abun ciki

circa 1900–1700 BC

Jacob, Joseph & Egypt

Jacob wrestles with God and becomes Israel; Joseph is sold into slavery yet rises to save the world from famine.

840 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. Farawa 26:26kusan 1804 K.H.

    Ana cikin haka, sai Abimelek ya zo wurinsa daga Gerar, tare da Ahuzzat mai ba shi shawara da Fikol shugaban mayaƙansa.

  2. Farawa 26:27kusan 1804 K.H.

    Ishaku ya tambaye su, “Me ya kawo ku gare ni, da yake kun yi gāba da ni, kuka kuma kore ni?”

  3. Farawa 26:28kusan 1804 K.H.

    Suka amsa, “Mun ga a zahiri cewa Ubangiji yana tare da kai; saboda haka muka ce, ‘Dole rantsuwa ta kasance tsakaninmu da kai.’ Bari mu yi yarjejjeniya da kai

  4. Farawa 26:29kusan 1804 K.H.

    cewa ba za ka cuce mu ba, kamar yadda ba mu fitine ka ba, amma muka yi maka kirki, muka kuma sallame ka cikin salama. Yanzu kuwa kai albarkatacce ne na Ubangiji.”

  5. Farawa 26:30kusan 1804 K.H.

    Sai Ishaku ya shirya musu liyafa, suka ci suka kuma sha.

  6. Farawa 26:31kusan 1804 K.H.

    Kashegari da sassafe sai mutanen suka yi wa juna rantsuwa. Sa’an nan Ishaku ya sallame su, suka kuwa tafi cikin salama.

  7. Farawa 26:32kusan 1804 K.H.

    A wannan rana bayin Ishaku suka zo suka faɗa masa game da rijiyar da suka haƙa. Suka ce, “Mun sami ruwa!”

  8. Farawa 26:33kusan 1804 K.H.

    Sai ya kira ta Shiba, don haka har wa yau ana kira garin Beyersheba.

  9. Farawa 26:34kusan 1796 K.H.

    Sa’ad da Yaƙub ya kai shekaru arba’in da haihuwa, sai ya auri Yudit ’yar Beyeri mutumin Hitti, da kuma Basemat ’yar Elon mutumin Hitti.

  10. Farawa 26:35kusan 1796 K.H.

    Su ne suka zama sanadin baƙin ciki ga Ishaku da Rebeka.

  11. Farawa 27:1kusan 1760 K.H.

    Sa’ad da Ishaku ya tsufa idanunsa suka raunana har ba ya iya gani, sai ya kira Isuwa babban ɗansa ya ce masa, “Ɗana.” Isuwa kuwa ya amsa, ya ce “Ga ni.”

  12. Farawa 27:2kusan 1760 K.H.

    Ishaku ya ce, “Yanzu na tsufa kuma ban san ranar mutuwata ba.

  13. Farawa 27:3kusan 1760 K.H.

    Saboda haka yanzu, ka ɗauki makamanka, kwari da bakanka, ka tafi jeji ka farauto mini nama.

  14. Farawa 27:4kusan 1760 K.H.

    Ka shirya mini irin abinci mai daɗin da nake so, ka kawo mini in ci, domin in sa maka albarka kafin in mutu.”

  15. Farawa 27:5kusan 1760 K.H.

    Ashe, Rebeka tana ji sa’ad da Ishaku ya yi wa ɗansa Isuwa magana. Da Isuwa ya tafi jeji don yă farauto nama yă kawo,

  16. Farawa 27:6kusan 1760 K.H.

    sai Rebeka ta ce wa ɗanta Yaƙub, “Ka ji nan, na ji mahaifinka ya ce wa ɗan’uwanka Isuwa,

  17. Farawa 27:7kusan 1760 K.H.

    ‘Kawo mini nama ka shirya mini abinci mai daɗi don in ci, in sa maka albarka a gaban Ubangiji kafin in mutu.’

  18. Farawa 27:8kusan 1760 K.H.

    Saboda haka ɗana, ka saurara da kyau ka kuma yi abin da na faɗa maka.

  19. Farawa 27:9kusan 1760 K.H.

    Je garke ka kawo mini awaki biyu kyawawa, domin in shirya abinci mai daɗi wa mahaifinka, kamar yadda dai yake so.

  20. Farawa 27:10kusan 1760 K.H.

    Sa’an nan ka kai wa mahaifinka yă ci, domin yă sa maka albarka kafin yă mutu.”

  21. Farawa 27:11kusan 1760 K.H.

    Yaƙub ya ce wa mahaifiyarsa Rebeka, “Amma ɗan’uwana Isuwa mutum ne mai gashi a jiki, ni kuma jikina sumul yake.

  22. Farawa 27:12kusan 1760 K.H.

    A ce baba ya tattaɓa ni fa? Zai zama kamar ina ruɗunsa ne, wannan fa zai jawo mini la’ana a maimakon albarka.”

  23. Farawa 27:13kusan 1760 K.H.

    Mahaifiyarsa ta ce masa, “Ɗana, bari la’anar tă fāɗo a kaina. Kai dai yi abin da na faɗa, jeka ka kawo mini su.”

  24. Farawa 27:14kusan 1760 K.H.

    Sai ya tafi ya kamo su, ya kawo wa mahaifiyarsa, ta kuwa shirya abinci mai daɗi, yadda mahaifinsa yake so.

  25. Farawa 27:15kusan 1760 K.H.

    Sa’an nan Rebeka ta ɗauki riguna mafi kyau na Isuwa babban ɗanta, waɗanda take da su a gida ta sa wa ƙaramin ɗanta Yaƙub.