Tsallake zuwa abun ciki

circa 1900–1700 BC

Jacob, Joseph & Egypt

Jacob wrestles with God and becomes Israel; Joseph is sold into slavery yet rises to save the world from famine.

840 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. Farawa 27:16kusan 1760 K.H.

    Sai ta mamanne gashin awakin nan biyu a hannuwansa da bayan wuyarsa wanda ba gashi.

  2. Farawa 27:17kusan 1760 K.H.

    Sa’an nan ta ba wa ɗanta Yaƙub abinci mai daɗi da kuma burodin da ta yi.

  3. Farawa 27:18kusan 1760 K.H.

    Shi kuwa ya tafi wurin mahaifinsa ya ce, “Babana.” Shi kuma ya amsa “I, ɗana, wane ne?”

  4. Farawa 27:19kusan 1760 K.H.

    Yaƙub ya ce wa mahaifinsa, “Ni ne Isuwa ɗan farinka. Na yi yadda ka faɗa mini. Ina roƙonka tashi ka zauna ka ci naman, domin ka sa mini albarkarka.”

  5. Farawa 27:20kusan 1760 K.H.

    Ishaku ya tambayi ɗansa, “Yaya aka yi ka samo shi da sauri haka, ɗana?” Yaƙub ya amsa ya ce, “Ubangiji Allahnka ne ya ba ni nasara.”

  6. Farawa 27:21kusan 1760 K.H.

    Sai Ishaku ya ce wa Yaƙub, “Zo kusa don in taɓa ka, ɗana, domin in sani ko tabbatacce kai ne ɗana Isuwa ko babu.”

  7. Farawa 27:22kusan 1760 K.H.

    Yaƙub kuwa ya matsa kusa da mahaifinsa Ishaku, wanda ya tattaɓa shi, sa’an nan ya ce, “Muryan nan dai, muryar Yaƙub ce, amma hannuwan, hannuwan Isuwa ne.”

  8. Farawa 27:23kusan 1760 K.H.

    Bai gane shi ba, gama hannuwansa suna da gashi kamar na ɗan’uwansa Isuwa, saboda haka ya albarkace shi.

  9. Farawa 27:24kusan 1760 K.H.

    Ya tambaya, “Tabbatacce kai ne ɗana Isuwa?” Ya amsa ya ce “Ni ne.”

  10. Farawa 27:25kusan 1760 K.H.

    Sa’an nan ya ce, “Ɗana, kawo mini naman da ka farauto in ci, domin in sa maka albarka.” Yaƙub ya kawo masa ya kuwa ci; ya kuma kawo masa ruwan inabi ya kuma sha.

  11. Farawa 27:26kusan 1760 K.H.

    Sa’an nan mahaifinsa Ishaku ya ce masa, “Zo nan, ɗana ka sumbace ni.”

  12. Farawa 27:27kusan 1760 K.H.

    Saboda haka ya je gunsa ya sumbace shi. Sa’ad da Ishaku ya ji ƙanshin rigunansa, sai ya sa masa albarka ya ce, “Aha, ƙanshin ɗana yana kama da ƙanshin jejin da Ubangiji ya sa wa albarka ne.

  13. Farawa 27:28kusan 1760 K.H.

    Allah yă ba ka daga raɓar sama da kuma yalwar ƙasa, yalwar hatsi da sabon ruwan inabi.

  14. Farawa 27:29kusan 1760 K.H.

    Bari al’ummai su bauta maka mutane kuma su rusuna maka. Ka zama shugaba a kan ’yan’uwanka bari kuma ’ya’yan mahaifiyarka su rusuna maka. Bari waɗanda suka la’anta ka, su la’antu; waɗanda kuma suka sa maka albarka, su sami albarka.”

  15. Farawa 27:30kusan 1760 K.H.

    Bayan Ishaku ya gama sa masa albarka, Yaƙub yana fita daga mahaifinsa ke nan, sai ga ɗan’uwansa Isuwa ya dawo daga farauta.

  16. Farawa 27:31kusan 1760 K.H.

    Shi ma ya shirya abinci mai daɗi ya kawo wa mahaifinsa. Sa’an nan ya ce masa, “Babana, tashi ka zauna ka ci daga abin da na farauto, domin ka sa mini albarka.”

  17. Farawa 27:32kusan 1760 K.H.

    Mahaifinsa Ishaku ya tambaye shi, “Wane ne kai?” Ya amsa, “Ni ne ɗanka, ɗan farinka, Isuwa.”

  18. Farawa 27:33kusan 1760 K.H.

    Ishaku ya yi makyarkyata ƙwarai ya ce, “To, wane ne wannan da ya farauto nama ya kawo mini kafin ka zo, har na ci na kuma sa masa albarka? Tabbatacce zai zama mai albarka!”

  19. Farawa 27:34kusan 1760 K.H.

    Sa’ad da Isuwa ya ji kalmomin mahaifinsa, sai ya fashe da kuka mai zafi kuma da ƙarfi, ya ce wa mahaifinsa, “Ka albarkace ni, ni ma, baba!”

  20. Farawa 27:35kusan 1760 K.H.

    Amma ya ce, “Ɗan’uwanka ya zo da makirci ya karɓi albarkarka.”

  21. Farawa 27:36kusan 1760 K.H.

    Isuwa ya ce, “Ba saboda haka ne aka raɗa masa suna Yaƙub ba? Ya yi mini ƙwace sau biyu ke nan; ya ƙwace mini matsayina na ɗan fari, ga shi yanzu kuma ya karɓi albarkata.” Sa’an nan ya yi tambaya, “Ba sauran albarkar da ka rage mini?”

  22. Farawa 27:37kusan 1760 K.H.

    Ishaku ya amsa wa Isuwa, “Na mai da shi shugaba a kanka, na sa dukan dangoginsa su zama bayinsa, na kuma ba shi hatsi da sabon ruwan inabi. Saboda haka me kuma zan yi maka ɗana?”

  23. Farawa 27:38kusan 1760 K.H.

    Isuwa ya ce wa mahaifinsa, “Iyakar albarkar da kake da ita ke nan, baba? Ka albarkace ni ni ma, baba!” Sai Isuwa ya ɗaga murya ya yi kuka.

  24. Farawa 27:39kusan 1760 K.H.

    Mahaifinsa Ishaku ya amsa masa ya ce, “Ga shi, ni’imar ƙasar za tă nisanci mazauninka. Raɓar samaniya can ƙwanƙoli za tă nisance ka.

  25. Farawa 27:40kusan 1760 K.H.

    Za ka rayu ta wurin takobi za ka kuwa bauta wa ɗan’uwanka. Amma sa’ad da ka ɓalle, za ka kakkarye karkiyarsa daga wuyanka.”