Tsallake zuwa abun ciki

circa 1900–1700 BC

Jacob, Joseph & Egypt

Jacob wrestles with God and becomes Israel; Joseph is sold into slavery yet rises to save the world from famine.

840 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. Farawa 28:20kusan 1760 K.H.

    Sa’an nan Yaƙub ya yi alkawari cewa, “In Allah zai kasance tare da ni yă kuma lura da ni a wannan tafiya, yă kuma ba ni abinci in ci da tufafi in sa,

  2. Farawa 28:21kusan 1760 K.H.

    har in dawo lafiya zuwa gidan mahaifina, to, Ubangiji zai zama Allahna

  3. Farawa 28:22kusan 1760 K.H.

    kuma wannan dutsen da na kafa al’amudi, zai zama gidan Allah, kuma dukan abin da ka ba ni zan ba ka kashi ɗaya bisa goma.”

  4. Sa’an nan Yaƙub ya ci gaba da tafiyarsa har ya kai ƙasar mutanen gabashi.

  5. A can ya ga rijiya a jeji da garkuna uku na tumaki kwance kusa da ita, gama a wannan rijiya ce ake shayar da garkuna. Dutsen da ake rufe bakin rijiyar mai girma ne.

  6. Sa’ad da dukan garkuna suka taru a can, sai makiyayan su gungurar da dutsen daga bakin rijiyar su shayar da tumaki. Sa’an nan su mai da dutsen a wurinsa a bakin rijiya.

  7. Yaƙub ya tambayi makiyayan ya ce, “’Yan’uwa, ina kuka fito?” Suka amsa, “Mu daga Haran ne.”

  8. Sai ya ce musu, “Kun san Laban, jikan Nahor?” Suka amsa, “I, mun san shi.”

  9. Sa’an nan Yaƙub ya tambaye su, “Yana nan lafiya?” Suka ce, “I, yana lafiya, ga ma ’yarsa Rahila tafe da tumaki.”

  10. Ya ce, “Duba har yanzu da sauran rana da yawa, lokaci bai kai na tara garkuna ba. Ku shayar da tumaki ku mai da su wurin kiwo.”

  11. Suka amsa suka ce, “Ba za mu iya ba, sai dukan garkunan sun taru, aka kuma gungurar da dutsen daga bakin rijiyar. Sa’an nan za mu shayar da tumakin.”

  12. Tun yana cikin magana da su, sai ga Rahila ta zo da tumakin mahaifinta, gama ita makiyayyiya ce.

  13. Sa’ad da Yaƙub ya ga Rahila ’yar Laban, ɗan’uwan mahaifiyarsa, da tumakin Laban, sai ya tafi ya gungurar da dutsen daga bakin rijiyar, ya kuma shayar da tumakin kawunsa.

  14. Sa’an nan Yaƙub ya sumbaci Rahila, ya kuma ɗaga murya ya yi kuka.

  15. Ya riga ya faɗa wa Rahila cewa shi dangin mahaifinta ne kuma ɗan Rebeka. Saboda haka ta ruga da gudu ta faɗa wa mahaifinta.

  16. Nan da nan, da Laban ya sami labari game da Yaƙub, ɗan ’yar’uwarsa, ya gaggauta yă sadu da shi. Sai ya rungume shi ya sumbace shi, ya kuma kawo shi gidansa, a can kuwa Yaƙub ya faɗa masa dukan waɗannan abubuwa.

  17. Sa’an nan Laban ya ce masa, “Kai nama da jinina ne.” Bayan Yaƙub ya zauna da shi na wata guda cif,

  18. sai Laban ya ce masa, “Don kawai kai dangina ne na kusa, sai kawai ka yi mini aiki a banza? Faɗa mini abin da albashinka zai zama.”

  19. Laban dai yana da ’ya’ya mata biyu; sunan babbar Liyatu, sunan ƙaramar kuwa Rahila.

  20. Liyatu tana da raunannun idanu, amma Rahila dai tsarinta yana da kyau kuma kyakkyawa ce.

  21. Yaƙub ya ƙaunaci Rahila, sai ya ce, “Zan yi maka aiki na shekaru bakwai domin ƙaramar ’yarka Rahila.”

  22. Laban ya ce, “Ya fi kyau in ba ka ita, da in ba wani mutum dabam. Zauna tare da ni.”

  23. Farawa 29:20kusan 1753 K.H.

    Saboda haka Yaƙub ya yi bauta shekaru bakwai domin a ba shi Rahila, amma shekarun suka zama kamar ’yan kwanaki ne kawai gare shi saboda ƙaunar da yake mata.

  24. Farawa 29:21kusan 1753 K.H.

    Sa’an nan Yaƙub ya ce wa Laban, “Ba ni matata. Lokacina ya cika, ina kuma so in kwana da ita.”

  25. Farawa 29:22kusan 1753 K.H.

    Saboda haka Laban ya tara dukan mutanen wurin, ya yi biki.