Tsallake zuwa abun ciki

circa 1900–1700 BC

Jacob, Joseph & Egypt

Jacob wrestles with God and becomes Israel; Joseph is sold into slavery yet rises to save the world from famine.

840 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. Farawa 29:23kusan 1753 K.H.

    Amma da yamma ta yi, sai ya ɗauki ’yarsa Liyatu ya ba da ita ga Yaƙub, sai Yaƙub ya kwana da ita.

  2. Farawa 29:24kusan 1753 K.H.

    Laban kuma ya ba da baranyarsa Zilfa wa ’yarsa tă zama mai hidimarta.

  3. Farawa 29:25kusan 1753 K.H.

    Sa’ad da safiya ta yi, sai ga Liyatu! Saboda haka Yaƙub ya ce wa Laban, “Mene ne ke nan ka yi mini? Na yi maka bauta domin Rahila, ba haka na yi ba? Don me ka ruɗe ni?”

  4. Farawa 29:26kusan 1753 K.H.

    Laban ya amsa, “Ba al’adarmu ba ce a nan a ba da ’ya ƙarama aure kafin ’yar fari.

  5. Farawa 29:27kusan 1753 K.H.

    Ka gama makon amaryanci na ’yar nan; sa’an nan za mu ba ka ƙaramar ita ma, don ƙarin waɗansu shekaru bakwai na aiki.”

  6. Farawa 29:28kusan 1753 K.H.

    Haka kuwa Yaƙub ya yi. Ya gama mako guda da Liyatu, sa’an nan Laban ya ba shi ’yarsa Rahila tă zama matarsa.

  7. Farawa 29:29kusan 1753 K.H.

    Laban ya ba da baranyarsa Bilha wa ’yarsa Rahila ta zama mai hidimarta.

  8. Farawa 29:30kusan 1753 K.H.

    Yaƙub ya kwana da Rahila ita ma, ya kuwa ƙaunaci Rahila fiye da Liyatu. Ya kuma yi wa Laban aiki na ƙarin waɗansu shekaru bakwai.

  9. Farawa 29:31kusan 1753 K.H.

    Sa’ad da Ubangiji ya ga ba a ƙaunar Liyatu, sai ya buɗe mahaifarta, amma Rahila ta zama bakararriya.

  10. Farawa 29:32kusan 1752 K.H.

    Sai Liyatu ta yi ciki ta haifi ɗa. Ta sa masa suna Ruben, gama ta ce, “Domin Ubangiji ya ga wahalata. Tabbatacce mijina zai ƙaunace ni yanzu.”

  11. Farawa 29:33kusan 1751 K.H.

    Ta sāke yin ciki, sa’ad da kuma ta haifi ɗa sai ta ce, “Gama Ubangiji ya ji cewa ba a ƙaunata, ya ba ni wannan shi ma.” Saboda haka ta ba shi suna Simeyon.

  12. Farawa 29:34kusan 1750 K.H.

    Har yanzu ta yi ciki, sa’ad da kuma ta haifi ɗa sai ta ce, “Yanzu, a ƙarshe mijina zai manne mini, gama na haifa masa ’ya’ya maza uku.” Saboda haka ta ba shi suna Lawi.

  13. Farawa 29:35kusan 1749 K.H.

    Ta sāke yin ciki, sa’ad da ta haifi ɗa sai ta ce, “A wannan lokaci zan yabi Ubangiji.” Saboda haka ta ba shi suna Yahuda. Sa’an nan ta daina haihuwa.

  14. Sa’ad da Rahila ta ga cewa ba tă haifa wa Yaƙub ’ya’ya ba, sai ta fara kishin ’yar’uwarta. Saboda haka ta ce wa Yaƙub, “Ka ba ni ’ya’ya, ko kuwa in mutu!”

  15. Yaƙub ya fusata da ita ya ce, “Ina a matsayin Allah ne wanda ya hana ke samun ’ya’ya?”

  16. Sa’an nan ta ce, “Ga Bilha, mai baiwata, ka kwana da ita don tă haifa mini ’ya’ya, ta gare ta kuwa ni ma in gina iyali.”

  17. Saboda haka ta ba shi baranyarta Bilha tă zama matarsa. Yaƙub kuwa ya kwana da ita,

  18. ta kuwa yi ciki, ta kuma haifi ɗa.

  19. Farawa 30:6kusan 1748 K.H.

    Sa’an nan Rahila ta ce, “Allah ya baratar da ni; ya saurari roƙona ya kuma ba ni ɗa.” Saboda wannan ta ba shi suna Dan.

  20. Farawa 30:7kusan 1747 K.H.

    Baranyar Rahila ta sāke yin ciki ta kuma haifi wa Yaƙub ɗa na biyu.

  21. Farawa 30:8kusan 1747 K.H.

    Sai Rahila ta ce, “Na yi kokawa sosai da ’yar’uwata, na kuwa yi nasara.” Saboda haka ta kira shi Naftali.

  22. Farawa 30:9kusan 1748 K.H.

    Sa’ad da Liyatu ta ga cewa ta daina haihuwa, sai ta ɗauki mai hidimarta Zilfa ta ba da ita ga Yaƙub tă zama matarsa.

  23. Farawa 30:10kusan 1748 K.H.

    Baranyar Liyatu, Zilfa ta haifa wa Yaƙub ɗa.

  24. Farawa 30:11kusan 1748 K.H.

    Sai Liyatu ta ce, “Na yi sa’a!” Saboda haka ta ba shi suna Gad.

  25. Farawa 30:12kusan 1748 K.H.

    Zilfa baranyar Liyatu ta haifa wa Yaƙub ɗa na biyu.