- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1900–1700 BC
Jacob, Joseph & Egypt
Jacob wrestles with God and becomes Israel; Joseph is sold into slavery yet rises to save the world from famine.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Farawa 27:41kusan 1760 K.H.
Isuwa ya riƙe Yaƙub a zuciya saboda albarkar da mahaifinsa ya sa masa. Ya ce wa kansa, “Kwanakin mutuwar mahaifina sun yi kusa; sa’an nan zan kashe ɗan’uwana Yaƙub.”
- Farawa 27:42kusan 1760 K.H.
Sa’ad da aka faɗa wa Rebeka abin da babban ɗanta Isuwa ya faɗa, sai ta kira ɗanta Yaƙub ta ce masa, “Ɗan’uwanka Isuwa yana ta’azantar da kansa da tunanin kashe ka.
- Farawa 27:43kusan 1760 K.H.
To, fa, ɗana, yi abin da na ce; gudu nan take zuwa wurin ɗan’uwana Laban a Haran.
- Farawa 27:44kusan 1760 K.H.
Zauna tare da shi na ɗan lokaci sai ɗan’uwanka ya huce.
- Farawa 27:45kusan 1760 K.H.
Sa’ad da ɗan’uwanka ya daina fushi da kai, ya kuma manta da abin da ka yi masa, zan aika don ka dawo daga can. Don me zan rasa ku biyu a rana guda?”
- Farawa 27:46kusan 1760 K.H.
Sa’an nan Rebeka ta ce wa Ishaku, “Ni fa na gaji da matan Hittiyawan nan. In Yaƙub ya auri mata daga cikin matan ƙasan nan, wato, daga matan Hittiyawa irin waɗannan, rayuwata ba za tă daɗa mini kome ba.”
- Farawa 28:1kusan 1760 K.H.
Saboda haka Ishaku ya kira Yaƙub, ya kuma albarkace shi, sa’an nan ya umarce shi ya ce, “Kada ka auri mace daga Kan’ana.
- Farawa 28:2kusan 1760 K.H.
Tashi nan da nan ka tafi Faddan Aram, zuwa gidan mahaifin mahaifiyarka Betuwel. Ka ɗauko wa kanka mata a can daga cikin ’ya’ya matan Laban ɗan’uwan mahaifiyarka.
- Farawa 28:3kusan 1760 K.H.
Bari Allah Maɗaukaki yă albarkace ka, yă kuma sa ka yi ta haihuwa ka riɓaɓɓanya har ka zama ƙungiyar jama’o’i.
- Farawa 28:4kusan 1760 K.H.
Bari Allah yă ba ka da kuma zuriyarka albarkar da ya ba wa Ibrahim, don ka amshi ƙasar da kake baƙunci, ƙasar da Allah ya ba wa Ibrahim.”
- Farawa 28:5kusan 1760 K.H.
Sa’an nan Ishaku ya sallami Yaƙub, ya kuwa tafi Faddan Aram, zuwa wurin Laban ɗan Betuwel mutumin Aram. Laban ne ɗan’uwan Rebeka, wadda take mahaifiyar Yaƙub da Isuwa.
- Farawa 28:6kusan 1760 K.H.
Yanzu Isuwa ya san cewa Ishaku ya albarkaci Yaƙub ya kuma aike shi zuwa Faddan Aram don yă auri mata daga can, ya kuma san cewa sa’ad da ya albarkace shi, ya umarce shi cewa, “Kada ka auro wata mace daga cikin Kan’aniyawa,”
- Farawa 28:7kusan 1760 K.H.
ya kuma san cewa Yaƙub ya yi biyayya da mahaifinsa da kuma mahaifiyarsa, ya kuwa tafi Faddan Aram.
- Farawa 28:8kusan 1760 K.H.
Sai Isuwa ya gane cewa matan Kan’aniyawa ba su gamshi mahaifinsa Ishaku ba;
- Farawa 28:9kusan 1760 K.H.
saboda haka sai ya tafi wurin Ishmayel ya auri Mahalat, ’yar’uwar Nebayiwot da kuma ’yar Ishmayel ɗan Ibrahim, ban da matan da yake da su.
- Farawa 28:10kusan 1760 K.H.
Yaƙub ya bar Beyersheba ya kama hanyar Haran.
- Farawa 28:11kusan 1760 K.H.
Sa’ad da ya kai wani wuri, sai ya dakata domin yă kwana, gama rana ta riga ta fāɗi. Ya ɗauki dutse daga cikin duwatsun wurin, ya sa shi ya zama matashin kansa, sa’an nan ya kwanta don yă yi barci.
- Farawa 28:12kusan 1760 K.H.
Ya yi mafarki inda ya ga wata matakalar hawa, tsaye a ƙasa, kanta ta kai sama, mala’ikun Allah kuwa suna hawa, suna sauka a kanta.
- Farawa 28:13kusan 1760 K.H.
A can bisantaUbangiji ya tsaya, ya kuma ce, “Ni ne Ubangiji Allah na mahaifinka Ibrahim da kuma Allah na Ishaku. Zan ba ka, kai da kuma zuriyarka, ƙasar da kake kwance a kai.
- Farawa 28:14kusan 1760 K.H.
Zuriyarka za tă zama kamar ƙurar ƙasa, za ka kuma bazu zuwa yamma da kuma gabas, zuwa arewa da kuma kudu. Dukan mutanen duniya za su sami albarka ta wurinka da kuma ta wurin ’ya’yanka.
- Farawa 28:15kusan 1760 K.H.
Ina tare da kai, zan lura da kai duk inda ka tafi, zan kuma dawo da kai zuwa wannan ƙasa. Ba zan rabu da kai ba sai na cika abin da na yi maka alkawari.”
- Farawa 28:16kusan 1760 K.H.
Sa’ad da Yaƙub ya farka daga barci, sai ya yi tunani ya ce, “Tabbatacce Ubangiji yana a wannan wuri, ban kuwa sani ba.”
- Farawa 28:17kusan 1760 K.H.
Ya ji tsoro, ya kuma ce, “Wane irin wuri ne mai banrazana haka! Lalle wannan gidan Allah ne, kuma nan ne ƙofar sama.”
- Farawa 28:18kusan 1760 K.H.
Kashegari da sassafe, sai Yaƙub ya ɗauki dutsen da ya yi matashin kai da shi, ya kafa shi al’amudi, ya kuma zuba mai a kansa.
- Farawa 28:19kusan 1760 K.H.
Ya kira wannan wuri Betel ko da yake dā ana kiran birnin Luz ne.