- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 2100–1900 BC
Abraham: The Covenant
God calls Abram from Ur, establishes an everlasting covenant, and promises a son through whom all nations will be blessed.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Farawa 24:58kusan 1857 K.H.
Saboda haka suka kira Rebeka suka ce mata, “Za ki tafi tare da mutumin nan?” Sai ta ce, “Zan tafi.”
- Farawa 24:59kusan 1857 K.H.
Saboda haka suka sallame Rebeka, ’yar’uwarsu, duk da uwar goyonta da bawan Ibrahim da mutanensa.
- Farawa 24:60kusan 1857 K.H.
Suka kuma albarkaci Rebeka suka ce mata, “’Yar’uwarmu, bari ki zama mahaifiyar dubu dubbai, bari zuriyarki su mallaki ƙofofin abokan gābansu.”
- Farawa 24:61kusan 1857 K.H.
Sa’an nan Rebeka da bayinta mata suka shirya suka hau raƙumansu suka koma tare da mutumin. Da haka bawan ya ɗauki Rebeka ya tafi.
- Farawa 24:62kusan 1857 K.H.
Ishaku kuwa ya zo daga Beyer-Lahai-Royi, gama yana zama a Negeb.
- Farawa 24:63kusan 1857 K.H.
Wata rana da yamma ya fita zuwa fili domin yă yi tunani, sa’ad da ya ɗaga ido, sai ya ga raƙuma suna zuwa.
- Farawa 24:64kusan 1857 K.H.
Rebeka ma ta ɗaga ido sai ta ga Ishaku. Ta sauka daga raƙuminta da sauri,
- Farawa 24:65kusan 1857 K.H.
ta ce wa bawan, “Wane ne mutumin can a fili, da yake zuwa yă tarye mu?” Bawan ya ce, “Maigidana ne.” Saboda haka ta ɗauki mayafinta to rufe kanta.
- Farawa 24:66kusan 1857 K.H.
Sai bawan ya faɗa wa Ishaku duk abin da ya yi.
- Farawa 24:67kusan 1857 K.H.
Ishaku ya kawo ta cikin tentin mahaifiyarsa Saratu, ya kuma auri Rebeka. Ta haka ta zama matarsa, ya kuwa ƙaunace ta; Ishaku kuma ya ta’azantu bayan rasuwar mahaifiyarsa.
- Farawa 25:1kusan 1853 K.H.
Ibrahim ya auro wata mace, mai suna Ketura.
- Farawa 25:2kusan 1852 K.H.
Ta haifa masa Zimran, Yokshan, Medan, Midiyan, Ishbak da Shuwa.
- Farawa 25:3kusan 1824 K.H.
Yokshan shi ne mahaifin Sheba da Dedan. Zuriyar Dedan su ne mutanen Ashur, da mutanen Letush, da kuma mutanen Lewummin.
- Farawa 25:4kusan 1804 K.H.
’Ya’yan Midiyan maza su ne, Efa, Efer, Hanok, Abida, da kuma Elda’a. Dukan waɗannan zuriyar Ketura ce.
- Farawa 25:5kusan 1829 K.H.
Ibrahim ya bar wa Ishaku kome da ya mallaka.
- Farawa 25:6kusan 1829 K.H.
Amma yayinda Ibrahim yake da rai, ya ba wa ’ya’yan ƙwarƙwaransa maza kyautai, ya kuma sallame su daga ɗansa Ishaku zuwa ƙasashen gabas.
- Farawa 25:7kusan 1821 K.H.
Duka-duka, Ibrahim ya yi shekara ɗari da saba’in da biyar.
- Farawa 25:8kusan 1821 K.H.
Sa’an nan Ibrahim ya ja numfashinsa na ƙarshe, ya kuma mutu da kyakkyawar tsufa, tsoho da kuma shekaru masu yawa; aka kuma tara shi ga mutanensa.
- Farawa 25:9kusan 1821 K.H.
’Ya’yansa maza kuwa Ishaku da Ishmayel suka binne shi cikin kogon Makfela, kusa da Mamre, a cikin filin Efron ɗan Zohar mutumin Hitti,
- Farawa 25:10kusan 1821 K.H.
filin da Ibrahim ya saya daga Hittiyawa. A nan aka binne Ibrahim tare da matarsa Saratu.
- Farawa 25:11kusan 1821 K.H.
Bayan rasuwar Ibrahim, Allah ya albarkaci ɗansa Ishaku wanda a lokacin yana zama kusa da Beyer-Lahai-Royi.
- Farawa 25:12kusan 1821 K.H.
Waɗannan su ne zuriyar Ishmayel ɗan Ibrahim, wanda Hagar mutuniyar Masar, baranyar Saratu, ta haifa wa Ibrahim.
- Farawa 25:13kusan 1821 K.H.
Ga jerin sunayen ’ya’yan Ishmayel maza bisa ga haihuwarsu, Nebayiwot ɗan farin Ishmayel, Kedar, Adbeyel, Mibsam,
- Farawa 25:14kusan 1821 K.H.
Mishma, Duma, Massa,
- Farawa 25:15kusan 1821 K.H.
Hadad, Tema, Yetur, Nafish da Kedema.