Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Titles and Names of the Wicked

82 ayoyi · 68 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Kowace safiya zan rufe bakunan dukan mugaye a ƙasar; zan yanke kowane mai aikata mugunta daga birnin Ubangiji.

  2. Ka miƙa hannunka daga bisa; ka cece ni ka kuma kuɓutar da ni daga manyan ruwaye, daga hannuwan baƙi

  3. Tsoron Ubangiji shi ne masomin ilimi, amma wawaye sun rena hikima da horo.

  4. Ɗana, in masu zunubi sun jarabce ka, kada ka yarda.

  5. Kada ka sa ƙafa a kan hanyar mugaye kada ka bi gurbin mugaye.

  6. Mugun mutum kan mai da hankali ga mugayen leɓuna; maƙaryaci yakan kasa kunne ga harshen ƙarairayi.

  7. Kash, ya ke al’umma mai zunubi, mutane cike da laifi, tarin masu aikata mugunta, ’ya’yan da aka miƙa wa lalaci! Sun yashe Ubangiji; sun rena Mai Tsarkin nan na Isra’ila suka juya masa baya.

  8. Ka rabu da mutanenka, gidan Yaƙub. Sun cika da ayyukan sihiri da aka kawo daga Gabas; suna yin duba kamar Filistiyawa suna tafa hannuwa tare da marasa sanin Allah.

  9. ba za a haɗa ka tare da su a jana’iza ba, gama ka hallaka ƙasarka ka kuma kashe mutanenka. Ba za a ƙara ambaci zuriyarka masu aikata mugunta ba.

  10. “Kaiton ’ya’ya masu tayarwa,” in ji Ubangiji, “ga waɗanda suke ƙulle-ƙullen da ba nawa ba, suna yin yarjejjeniya, amma ba ta Ruhuna ba, suna jibga zunubi a kan zunubi;

  11. Waɗannan mutane masu tawaye, ’ya’ya masu ruɗu, ’ya’yan da ba sa niyya su saurara ga umarnan Ubangiji.

  12. Wane ne kuke yi wa ba’a? Ga wa kuke masa gwalo kuna kuma fitar da harshe? Ashe, ku ba tarin ’yan tawaye ba ne, zuriyar maƙaryata?

  13. Dukan yini ina miƙa hannuwana ga mutane masu tayarwa, waɗanda suna tafiya a hanyoyin da ba su da kyau, suna bin tunaninsu,

  14. Kuna da azanci sosai a bin masoya! Kai, ko mafiya muni cikin mata tana iya koya daga hanyoyinku.

  15. “Mutanena wawaye ne; ba su san ni ba. Su ’ya’ya ne marasa azanci; ba su da fahimi. Suna da dabarar aikata mugunta; ba su san yadda za su aikata alheri ba.”

  16. Su duka masu taurinkai ne, ’yan tawaye, suna yawo suna baza jita-jita. Su tagulla ne da ƙarfe; dukansu lalatattu ne.

  17. Mutanen da nake aikan ka masu ƙin ji ne da kuma taurinkai. Ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya faɗa.’

  18. Kuma ko su ji ko kada su ji, gama su gida ne mai tawaye, za su san cewa akwai annabi a cikinsu.

  19. Amma kai, ɗan mutum, ka saurari abin da zan faɗa maka. Kada ka yi tawaye kamar wannan gidan ’yan tawaye; ka buɗe bakinka ka kuma ci abin da na ba ka.”

  20. ɗan mutum, kana zama a cikin mutane masu tawaye, Suna da idanun gani amma ba sa gani, suna da kunnuwan ji amma ba sa ji, gama ’yan tawaye ne.

  21. “Tun daga kwanakin Gibeya, kun yi zunubi, ya Isra’ila, a can kuwa kuka ci gaba. Yaƙi bai cimma masu aikata mugunta a Gibeya ba?

  22. Amma da Yohanna ya ga Farisiyawa da Sadukiyawa da yawa suna zuwa inda yake yin baftisma, sai ya ce musu, “Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku ku guje wa fushin nan mai zuwa?

  23. Ku macizai, ta yaya ku da kuke mugaye za ku iya magana kirki? Gama daga baki, mutum yakan faɗi abin da yake cikin zuciya.

  24. Sai ya amsa ya ce, “Mugaye da masu zinan zamanin nan suna neman wata alama mai banmamaki! Amma babu wadda za a nuna musu, sai dai alama ta annabi Yunana.

  25. Sai yă je yă ɗebo waɗansu ruhohi bakwai da suka fi shi mugunta, su kuwa zo su shiga su zauna a can. Ƙarshen mutumin nan fa zai fi farkonsa muni. Haka zai zama ga wannan mugun zamani.”