Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Titles and Names of the Wicked

82 ayoyi · 68 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Mugayen mutane da masu ruɗi kuwa, ƙara muni za su riƙa yi, suna yaudara, ana kuma yaudararsu.

  2. Ku mazinata, ba ku san cewa abokantaka da duniya gāba ce da Allah ba? Duk wanda ya zaɓa yă zama abokin duniya ya zama abokin gāban Allah ke nan.

  3. ko ga gwamnoni, waɗanda ya aika domin su hukunta masu laifi su kuma yabi masu aikata abin da yake daidai.

  4. Idanunsu sun cike da zina, ba sa ƙoshi da yin zunubi; suna jarrabtar waɗanda ba tsayayyu ba; gwanaye ne a kan kwaɗayi, la’anannun iri!

  5. Suna yin musu alkawarin ’yanci, yayinda su kansu bayi ne ga aikin lalata gama mutum bawa ne ga duk abin da ya mallake shi.

  6. Ta haka muka san waɗanda suke ’ya’yan Allah da kuma waɗanda suke ’ya’yan Iblis. Duk wanda ba ya yin abin da yake daidai, ba ɗan Allah ba ne; haka ma wanda ba ya ƙaunar ɗan’uwansa.

  7. Na faɗa haka ne domin waɗansu mutanen da aka rubuta hukuncinsu tun dā sun shiga cikinku a ɓoye. Su fa marasa tsoron Allah ne. Su ne waɗanda suka mai da alherin Allahnmu ya zama dalilin yin fasikanci, suna kuma mūsun Yesu Kiristi wanda shi ne Makaɗaici Mai Iko Duka da kuma Ubangijinmu.