Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Righteousness of God

73 ayoyi · 46 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Adalcinka ya kai sararin sama, ya Allah, kai da ka yi manyan abubuwa. Wane ne kamar ka, ya Allah?

  2. Harshena zai ba da labarin ayyukanka masu adalci dukan yini, gama waɗanda suka so su cutar da ni sun sha kunya suka kuma rikice.

  3. Ga yadda mugaye suke, kullum ba su da damuwa, arzikinsu yana ta ƙaruwa.

  4. Tabbatacce a banza na bar zuciyata da tsabta; a banza na wanke hannuwa don nuna rashin laifi.

  5. Dukan yini na sha annoba; an hukunta ni kowace safiya.

  6. Da na ce, “Zan faɗa haka,” da na bashe ’ya’yanka.

  7. Sa’ad da na yi ƙoƙari in gane wannan, sai ya zama danniya a gare ni

  8. sai da na shiga wuri mai tsarki na Allah; sa’an nan na gane abin da ƙarshensu zai zama.

  9. Ƙauna da aminci za su sadu; adalci da salama za su yi wa juna sumba.

  10. za su rera a gaban Ubangiji, gama yana zuwa, yana zuwa don yă hukunta duniya. Zai hukunta duniya cikin adalci mutane kuma cikin amincinsa.

  11. Gizagizai da baƙin duhu sun kewaye shi; adalci da gaskiya su ne tushen kursiyinsa.

  12. Sammai sun yi shelar adalcinsa, dukan mutane kuma suka ga ɗaukakarsa.

  13. Ubangiji ya sanar da cetonsa ya kuma bayyana adalcinsa ga al’ummai.

  14. bari su rera a gaban Ubangiji, gama yana zuwa domin yă hukunta duniya. Zai hukunta duniya da adalci mutane kuma cikin gaskiya.

  15. Amma daga madawwami zuwa madawwami ƙaunar Ubangiji tana tare da waɗanda suke tsoronsa, adalcinsa kuma tare da ’ya’yansu,

  16. Ayyukansa masu ɗaukaka da kuma daraja ne, adalcinsa kuma zai dawwama har abada.

  17. Ubangiji mai alheri ne da kuma mai adalci; Allahnmu yana cike da tausayi.

  18. Zan yabe ka da zuciya ta gaskiya yayinda nake koyon dokokinka masu adalci.

  19. Ina marmarin farillanka ƙwarai! Ka kiyaye raina cikin adalcinka.

  20. Da tsakar dare nakan tashi in gode maka saboda dokokinka masu adalci.

  21. Idanuna sun gaji, da jiran cetonka, da jiran alkawarinka mai adalci.

  22. Mai adalci ne kai, ya Ubangiji, dokokinka kuma daidai ne.

  23. Farillan da ka shimfiɗa masu adalci ne; su kuma abin dogara ne ƙwarai.

  24. Adalcinka dawwammame ne dokar kuma gaskiya ce.

  25. Farillanka daidai ne har abada; ka ba ni ganewa don in rayu.