Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Righteousness of God

73 ayoyi · 46 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Wace al’umma ce mai girma haka wadda take da ƙa’idodi da dokoki masu adalci kamar waɗannan ƙunshin dokokin da nake sa a gabanku a yau?

  2. da muryoyin mawaƙa a wuraren ruwaye. Suna faɗi ayyukan adalcin Ubangiji, ayyukan adalcin mayaƙansa a Isra’ila. “Sa’an nan mutanen Ubangiji suka gangara zuwa ƙofofin birni.

  3. Yanzu ku tsaya nan zan yi fito-na-fito da ku da shaida a gaban Ubangiji kan dukan ayyuka masu alherin da Ubangiji ya aikata saboda ku da kakanninku.

  4. Ya Ubangiji Allah na Isra’ila, kai mai adalci ne! Yau an bar mu da sauran da ya tsira. Ga mu nan a gabanka masu zunubi, gama ba wanda zai iya tsayawa a gabanka.”

  5. Kai ka sami zuciyarsa da aminci a gare ka, ka kuma yi alkawari da shi cewa za ka ba zuriyarsa ƙasar Kan’aniyawa, da ta Hittiyawa, da ta Amoriyawa, da ta Ferizziyawa, da ta Yebusiyawa, da kuma ta Girgashiyawa. Ka kiyaye alkawarinka domin kai mai adalci ne.

  6. Daga nesa na sami sanina; zan nuna cewa Mahaliccina shi mai gaskiya ne.

  7. Ka bi da ni, ya Ubangiji, cikin adalcinka saboda abokan gābana, ka fayyace hanyarka a gabana.

  8. Ya Allah mai adalci, wanda yake binciken tunani da zukata, ka kawo ƙarshen rikicin mugaye ka kuma sa adalai su zauna lafiya.

  9. Zan gode wa Ubangiji saboda adalcinsa zan kuma rera yabo ga sunan Ubangiji Mafi Ɗaukaka.

  10. Gama Ubangiji mai adalci ne, yana ƙaunar gaskiya masu adalci za su ga fuskarsa.

  11. Tsoron Ubangiji yakan kawo tsabtar zuciya, zai kasance har abada. Farillan Ubangiji tabbatattu ne, kuma gaba ɗaya masu adalci ne.

  12. Za su yi shelar adalcinsa ga mutanen da ba a riga an haifa ba, gama ya aikata shi.

  13. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. A gare ka, ya Ubangiji, na nemi mafaka; kada ka bari in taɓa shan kunya; ka cece ni cikin rahamarka.

  14. Ka nuna ni marar laifi ne ciki adalcinka, Ya Ubangiji Allahna; kada ka bari su yi farin ciki a kaina.

  15. Harshena zai yi zancen adalcinka da kuma yabonka dukan yini.

  16. Adalcinka yana kama da manyan duwatsu, hukuncinka kamar zurfi mai girma. Ya Ubangiji, kana lura da mutum da dabba.

  17. Ka ci gaba da ƙaunarka ga waɗanda suka san ka, adalcinka ga masu gaskiyar zuciya.

  18. Ba na ɓoye adalcinka cikin zuciyata; ina maganar amincinka da cetonka. Ban ɓoye ƙaunarka da gaskiyarka a gaban taron jama’arka mai girma ba.

  19. Kamar sunanka, ya Allah, yabonka ya kai iyakokin duniya; hannunka na dama ya cika da adalci.

  20. Sammai kuwa sun yi shelar adalcinsa gama Allah kansa alƙali ne. Sela

  21. Ka cece ni daga laifin jini, ya Allah, Allahn da ya cece ni, harshena kuwa zai rera adalcinka.

  22. Ka neme su da laifi a kan laifi; kada ka bar su su sami rabo a cikin cetonka.

  23. Ka kuɓutar da ni ka cece ni cikin adalcinka; ka juya kunnenka gare ni ka kuma cece ni.

  24. Bakina zai ba da labarin adalcinka, zai yi maganar cetonka dukan yini, ko da yake ban san yawansa ba.

  25. Zan zo in furta in kuma yi shelar ayyukanka masu girma, ya Ubangiji Mai Iko Duka; zan yi shelar adalcinka, naka kaɗai.