Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Righteousness of God: Acknowledge, though the wicked prosper
Ayoyi game da Acknowledge, though the wicked prosper
Ga yadda mugaye suke, kullum ba su da damuwa, arzikinsu yana ta ƙaruwa.
Tabbatacce a banza na bar zuciyata da tsabta; a banza na wanke hannuwa don nuna rashin laifi.
Dukan yini na sha annoba; an hukunta ni kowace safiya.
Da na ce, “Zan faɗa haka,” da na bashe ’ya’yanka.
Sa’ad da na yi ƙoƙari in gane wannan, sai ya zama danniya a gare ni
sai da na shiga wuri mai tsarki na Allah; sa’an nan na gane abin da ƙarshensu zai zama.
Kullum kai mai adalci ne, ya Ubangiji, sa’ad da na kawo ƙara a gabanka. Duk da haka zan yi magana da kai game da shari’arka. Me ya sa mugaye suke nasara? Me ya sa dukan maciya amana suke zama ba damuwa?