Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Resurrection of Christ

120 ayoyi · 46 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Amma suka matsa masa suka ce, “Sauka wurinmu, don dare ya kusa, rana ta kusa fāɗuwa.” Sai ya sauka wurinsu.

  2. Da ya zauna a tebur tare da su, sai ya ɗauki burodi, ya yi godiya, ya kakkarya ya fara ba su.

  3. Sa’an nan idanunsu suka buɗe, suka gane shi. Sai ya ɓace musu.

  4. suna cewa, “Gaskiya ne! Ubangiji ya tashi, ya kuma bayyana ga Siman”

  5. Sai su biyun nan suka ba da labarin abin da ya faru a hanya, da kuma yadda suka gane Yesu yayinda ya kakkarya burodin.

  6. Suka firgita, suka tsorota, suna tsammani fatalwa ce suka gani.

  7. Sai ya ce musu, “Don me kuke damuwa, kuke kuma shakka a zuciyarku?

  8. Ku duba hannuwana da ƙafafuna. Ai, ni ne da kaina! Ku taɓa ni ku ji, ai, fatalwa ba ta da nama da ƙashi, yadda kuke gani nake da su.”

  9. ya karɓa ya ci a gabansu.

  10. Sai ya wayar da tunaninsu don su fahimci Nassi.

  11. Ya ce musu, “Wannan shi ne abin da aka rubuta, cewa dole Kiristi yă sha wahala, a rana ta uku kuma yă tashi daga matattu.

  12. Yana cikin sa musu albarka, sai ya rabu da su. Aka ɗauke shi zuwa cikin sama.

  13. Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku rushe wannan haikali, zan kuwa sāke tā da shi cikin kwana uku.”

  14. Yahudawa suka ce, “Sai fa da aka shekara arba’in da shida ana ginin haikalin nan, kai kuwa a cikin kwana uku za ka tā da shi?”

  15. Amma haikalin da ya yi magana jikinsa ne.

  16. Bayan da ya tashi daga matattu, sai almajiransa suka tuna da abin da ya faɗa. Sa’an nan suka gaskata Nassi da kuma kalmomin da Yesu ya yi.

  17. Ba mai karɓe mini rai, ina dai ba da shi. Ina da iko in ba da shi, ina da iko in ɗauko shi kuma. Wannan umarni kuwa daga wurin Ubana na karɓo shi.”

  18. (Har yanzu ba su fahimci Nassin nan da ya ce lalle ne Yesu yă tashi daga matattu ba.)

  19. Sai Maryamu Magdalin ta wajen almajiran da labari cewa, “Na ga Ubangiji!” Ta kuma gaya musu cewa ya faɗa mata waɗannan abubuwa.

  20. Da Yamman ranar farko ta mako, sa’ad da almajiran suna tare, ƙofofi kuma suna a kulle saboda tsoron Yahudawa, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsakiyarsu ya ce, “Salama tă kasance tare da ku!”

  21. Bayan ya faɗa haka, sai ya nuna musu hannuwansa da gefensa. Sai almajiran suka yi farin ciki ƙwarai da suka ga Ubangiji.

  22. Toma kuwa (wanda ake kira Didaimus), ɗaya daga cikin Sha Biyun, ba ya tare da almajiran sa’ad da Yesu ya zo.

  23. Bayan mako guda, har wa yau almajiransa suna cikin gidan, Toma kuwa yana tare da su. Ko da yake ƙofofi suna kulle, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsakiyarsu ya ce, “Salama tă kasance tare da ku!”

  24. Sa’an nan ya ce wa Toma, “Sa yatsarka nan; dubi hannuwana. Miƙa hannunka ka sa a gefena. Ka daina shakka ka gaskata.”

  25. Daga baya Yesu ya sāke bayyana kansa ga almajiransa, a bakin Tekun Tibariya. Ga yadda ya faru.