Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Resurrection of Christ: Foretold by Himself

7 ayoyi · 46 fannoni

Ayoyi game da Foretold by Himself

  1. za su kuma bashe shi ga Al’ummai su yi masa ba’a, su yi masa bulala, su kuma gicciye shi. A rana ta uku kuma a tashe shi!”

  2. Da suna saukowa daga dutsen, Yesu ya umarce su kada su gaya wa kowa abin da suka gani, sai bayan Ɗan Mutum ya tashi daga matattu.

  3. Amma bayan na tashi, zan sha gabanku zuwa Galili.”

  4. Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku rushe wannan haikali, zan kuwa sāke tā da shi cikin kwana uku.”

  5. Yahudawa suka ce, “Sai fa da aka shekara arba’in da shida ana ginin haikalin nan, kai kuwa a cikin kwana uku za ka tā da shi?”

  6. Amma haikalin da ya yi magana jikinsa ne.

  7. Bayan da ya tashi daga matattu, sai almajiransa suka tuna da abin da ya faɗa. Sa’an nan suka gaskata Nassi da kuma kalmomin da Yesu ya yi.