Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Resurrection of Christ: Fraud impossible in

4 ayoyi · 46 fannoni

Ayoyi game da Fraud impossible in

  1. Suka ce, “Ranka yă daɗe, mun tuna, mai ruɗin nan tun yana da rai ya ce, ‘Bayan kwana uku, zan tashi daga matattu.’

  2. Saboda haka, ka ba da umarni, a tsare kabarin sai rana ta uku ɗin. In ba haka ba, almajiransa za su iya zuwa su sace jikin, sa’an nan su faɗa wa mutane cewa, an tashe shi daga matattu. Ruɗin ƙarshen nan fa, sai yă fi na farkon muni.”

  3. Sai Bilatus ya ce, “Shi ke nan, ku ɗebi soja, ku je ku tsare kabarin iya ƙoƙarinku.”

  4. Sai suka je suka tsare kabarin ta wurin buga masa hatimi, suka kuma sa masu gadi.