Tsallake zuwa abun ciki

Mary

14 ayoyi

An kuma san shi da: Mary Magdalene, Magdalene

Ayoyin da suka ambaci Mary

  1. A cikinsu, akwai Maryamu Magdalin, da Maryamu uwar Yaƙub da Yoses, da kuma uwar ’ya’yan Zebedi.

  2. Maryamu Magdalin da ɗayan Maryamun, suna zaune a wurin, ɗaura da kabarin.

  3. Bayan ranar Asabbaci, da sassafe, a ranar farko ta mako, Maryamu Magdalin tare da ɗaya Maryamun, suka je don su ga kabarin.

  4. Waɗansu mata suna kallo daga nesa. A cikinsu kuwa akwai Maryamu Magdalin, Maryamu mahaifiyar Yaƙub ƙarami da Yusuf, da kuma Salome.

  5. Maryamu Magdalin da Maryamu uwar Yusuf sun ga inda aka kwantar da shi.

  6. Da Asabbaci ya wuce, sai Maryamu Magdalin, Maryamu mahaifiyar Yaƙub, da kuma Salome suka sayi kayan ƙanshi domin su je su shafa wa jikin Yesu.

  7. Da Yesu ya tashi daga matattu da safe, a ranar farko ta mako, ya fara bayyana ga Maryamu Magdalin, wadda ya fitar da aljanu bakwai daga cikinta.

  8. da kuma waɗansu mata waɗanda aka warkar da su daga cututtukansu, da kuma mugayen ruhohi. Cikinsu akwai Maryamu (wadda ake kira Magdalin) wadda aljanu bakwai suka fito daga cikinta.

  9. Matan da suka gaya wa manzannin waɗannan abubuwa su ne, Maryamu Magdalin, da Yowanna, da Maryamu uwar Yaƙub, da waɗansu da suke tare da su.

  10. To, tsaye kusa da gicciyen Yesu kuwa akwai mahaifiyarsa, tare da ’yar’uwar mahaifiyarsa, Maryamu matar Kilofas, da kuma Maryamu Magdalin.

  11. Da sassafe a ranar farko ta mako, tun da sauran duhu, Maryamu Magdalin ta tafi kabarin ta kuwa tarar an kawar da dutsen daga bakin kabarin.

  12. Maryamu kuwa ta tsaya a bakin kabarin daga waje tana kuka. Da tana cikin kuka, sai ta sunkuya ta leƙa cikin kabarin,

  13. Yesu ya ce mata, “Maryamu.” Sai ta juya wajensa ta ɗaga murya ta ce da Arameyanci, “Rabboni!” (Wanda yake nufin “Malam”).

  14. Sai Maryamu Magdalin ta wajen almajiran da labari cewa, “Na ga Ubangiji!” Ta kuma gaya musu cewa ya faɗa mata waɗannan abubuwa.