Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Temptation

346 ayoyi · 52 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. A’a, cikin dukan waɗannan abubuwa mun ma fi masu nasara ta wurin shi wanda ya ƙaunace mu.

  2. Gama na tabbata cewa ko mutuwa ko rai, ko mala’iku ko aljanu, ko abubuwa na yanzu ko abubuwa masu zuwa nan gaba, ko ikoki,

  3. ko tsayi ko zurfi, ko wani abu dabam cikin dukan halitta da zai iya raba mu da ƙaunar Allah wadda take cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.

  4. Kada ku bar mugunta ta sha kanku, sai dai ku sha kan mugunta ta wurin aikata nagarta.

  5. Saboda haka bari mu daina ba wa juna laifi. A maimakon, sai kowa yă yi niyya ba zai sa dutsen tuntuɓe ko abin sa fāɗuwa a hanyar ɗan’uwansa ba.

  6. In kana ɓata wa ɗan’uwanka zuciya saboda abincin da kake ci, ba halin ƙauna kake nunawa ba ke nan. Kada abincin da kake ci yă zama hanyar lalatar da ɗan’uwanka wanda Kiristi ya mutu dominsa.

  7. Ya fi kyau kada ka ci nama ko ka sha ruwan inabi ko kuma ka yi wani abin da zai sa ɗan’uwanka yă fāɗi.

  8. Kada ku ƙi kwana da juna sai ko kun yarda a junanku kuma na ɗan lokaci, don ku himmantu ga addu’a. Sa’an nan ku sāke haɗuwa don kada Shaiɗan yă jarrabce ku saboda rashin ƙamewarku.

  9. Sai dai ku yi hankali, kada yin amfani da ’yancinku yă zama abin sa tuntuɓe ga marasa ƙarfi.

  10. Gama in wani wanda lamirinsa ba shi da ƙarfi ya gan ka, kai da kake da wannan sani, kana ci a haikalin gumaka, ashe, ba zai sami ƙarfin halin cin abin da aka miƙa wa gumaka ba?

  11. Saboda haka ta wurin sanin nan naka sai ka sa wannan ɗan’uwa marar ƙarfi wanda Kiristi ya mutu dominsa yă hallaka.

  12. Sa’ad da ka rushe lamiri mai bi marar ƙarfi, ka yi wa Kiristi zunubi ke nan.

  13. Saboda haka, in abin da nake ci zai sa ɗan’uwana yă yi zunubi, ba zan ƙara cin nama ba, don kada in sa shi yă yi tuntuɓe.

  14. Ba jarrabar da ta taɓa samunku, wadda ba a saba yi wa mutum ba. Allah mai aminci ne; ba zai bari a jarrabce ku fiye da ƙarfinku ba. Amma in aka jarrabce ku, zai nuna muku mafita, domin ku iya cin nasara.

  15. Sai dai in wani ya ce muku, “Ai, wannan an miƙa ne wa gunki,” to, kada ku ci, saboda duban mutuncin wannan da ya gaya muku, don kuma lamiri yă kasance babu laifi

  16. ina nufin lamirin wancan mutum ne fa, ba naku ba. Don me lamirin wani zai shari’anta ’yancina?

  17. In na ci abinci da godiya, don me za a zarge ni a kan abin da na ci da godiya ga Allah?

  18. Saboda haka, duk abin da kuke yi, ko ci ko sha, ku yi shi duka saboda ɗaukakar Allah.

  19. Kada ku sa wani yă yi tuntuɓe, ko mutumin Yahuda ne, ko mutumin Al’ummai ko kuma ikkilisiyar Allah

  20. Ku zauna a faɗake; ku dāge cikin bangaskiya; ku zauna da ƙarfafawa; ku yi ƙarfi.

  21. don kada Shaiɗan yă rinjaye mu. Da yake muna sane da dabarunsa.

  22. Sai dai ina tsoro kada yă zama, kamar yadda maciji ya yaudari Hawwa’u da makircinsa, ku ma a bauɗar da hankalinku daga sahihiyar biyayya amintacciya ga Kiristi.

  23. Ba abin mamaki ba ne, gama Shaiɗan kansa ma yana ɓad da kamanni kamar shi mala’ikan haske ne.

  24. Don haka, ba abin mamaki ba ne, in bayin Shaiɗan sun ɓad da kamanni kamar su bayin adalci ne. A ƙarshe, za a sāka musu gwargwadon ayyukansu.

  25. Don kada in cika da girman kai saboda waɗannan mafifitan manyan wahayoyi, sai aka sa mini wata ƙaya a jikina wadda ta zama ɗan saƙon Shaiɗan, don ta wahalshe ni.