Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Psalms

896 ayoyi · 16 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Mai albarka ne mutumin da korinsa sun cika da su. Ba za a kunyata su ba sa’ad da suke ƙarawa da abokan gābansu a ɗakin shari’a.

  2. Waƙar haurawa. Masu albarka ne dukan masu tsoron Ubangiji, waɗanda suke tafiya a hanyoyinsa.

  3. Za ka ci amfanin aikinka; albarku da wadata za su zama naka.

  4. Matarka za tă zama kamar kuringar inabi mai ’ya’ya a cikin gidanka; ’ya’yanka maza za su zama kamar tohon zaitun kewaye da teburinka.

  5. Ta haka mai albarka yake wanda yake tsoron Ubangiji.

  6. Bari Ubangiji ya albarkace ka daga Sihiyona dukan kwanakin ranka; bari ka ga wadatar Urushalima,

  7. bari kuma ka rayu ka ga ’ya’ya ’ya’yanka. Salama tă kasance tare da Isra’ila.

  8. Waƙar haurawa. Sun yi mini danniya ƙwarai tun ina ƙarami, bari Isra’ila yă ce,

  9. sun yi mini danniya ƙwarai tun ina ƙarami, amma ba su yi nasara a kaina ba.

  10. Manoma sun nome bayana suka yi kunyoyinsu da tsayi.

  11. Amma Ubangiji mai adalci ne; ya ’yantar da ni daga igiyoyin mugaye.

  12. Bari dukan waɗanda suke ƙin Sihiyona a juye da su baya da kunya.

  13. Bari su zama kamar ciyawa a kan rufi, wadda takan bushe kafin tă yi girma;

  14. da ita mai girbi ba ya iya cika hannuwansa, balle wanda yake tarawa yă cika hannuwansa.

  15. Kada masu wuce su ce, “Albarkar Ubangiji ta kasance a kanku; muna sa muku albarka a cikin sunan Ubangiji.”

  16. Waƙar haurawa. Daga cikin zurfafa na yi kuka gare ka, ya Ubangiji;

  17. Ya Ubangiji, ka ji muryata. Bari kunnuwanka su saurara ga kukata ta neman jinƙai.

  18. In kai, ya Ubangiji, za ka lissafta zunubai, Ya Ubangiji, wa zai tsaya?

  19. Amma tare da kai akwai gafartawa, saboda haka ake tsoronka.

  20. Zan jira Ubangiji, raina zai jira, kuma a cikin maganarsa na sa zuciyata.

  21. Raina na jiran Ubangiji fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya, fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya.

  22. Ya Isra’ila, sa zuciya ga Ubangiji, gama tare da Ubangiji akwai ƙauna marar ƙarewa kuma tare da shi akwai cikakkiyar fansa.

  23. Shi kansa zai fanshi Isra’ila daga dukan zunubansu.

  24. Waƙar haurawa. Ta Dawuda. Zuciyata ba mai girman kai ba ce, ya Ubangiji, idanuna ba sa fariya; ban dami kaina da manyan al’amura ba ko abubuwan da suka sha ƙarfina.

  25. Amma na haƙura na kuma kwantar da raina; kamar yaron da aka yaye tare da mahaifiyarsa, kamar yaron da aka yaye haka raina yake a cikina.